40

4.7K 221 2
                                    

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 41

Wunin ranar gaba d'aya haka bobo da Rahma suka kasheshi asoyayya da tattalin juna, dukda Rahma tanad'anjin kunyar bobo har yanzu.
     Ganin shiru basuzoba Ammi takira bobo tana tambayar ko jikin Rahmar ne har yanzu?.
    Cikin Sosa kai na jin kunya ya ce, "a'a ammi taji sauk'i bamuzoba daine kawai, sai gobe idan ALLAH ya kaimu.
   Murmushi Ammi tayi ta ce, " toshikenan ALLAH yakaimu goben tunda dai lfy Alhmdllh, ka gaishemin da ita
   To Ammi zataji.
  Rahma dake kwance ajikinkinsa ta ce, "ya Abdulmaleek ko kunya bakajiba Dan ALLAH.
    Murmushi yayma tareda fad'in kunyar wa zanji?.
   Ta Ammi mana.
Nanma murmushin yasakeyi batareda yace komaiba.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
       Shirye shiryen biki ya kankama sosai, hidima akeyi babu kama hannun yaro.
    Rahma da bobo kan sai godiyar ALLAH, soyayyarsu suketa zubawa kamar babu gobe, amma dai baisake mata komaiba Dan yana tausayinta sosai, kuma bobo ba irin fitunannun mazan nan baneba, tattalikam tana shansa, azuciyarta har mamakin bobo takeyi Dan bata ta6a tunanin yanada sauk'i hakaba, ada tana masa kallon muskili masifaffe.
   Amma yanzun data k'ara kusanci  dashi saitaga Bahaka bane, dukda yanada fad'a amma sai anta6oshi yakeyi.

Safna kam abin duniya ya isheta, k'iri² Ammi tahanata komawa gidansu Rahma, kayantama ranar gabad'aya bobo yakawomata gidan Ammi, bak'aramin 6aci ranta yayiba dantasan wannan Duk shirin bobone.
    Yau tunda safe take tsumayensa amma yak'i zuwa gidan kamar yanda yasaba, suna zaune itadasu khairiyya dake had'a kayansu saboda daga gobe shagalin biki zai fara.
    Kad'an kad'an saita lek'a window d'akinsu khairiyyar Dan daganan ana hangen Wanda zaishigo gidan, ta kalli agogon hanunta tareda yin tsaki.
    Khursiyya ta ce, "aunty safna lfy kuwa?.
    Murmushin yak'e tayi tareda wayancewa ta ce, " wlhy ya Abdulmaleek nake jira sonake nakar6i sak'o awanjensa.
   Su khairiyya basu kawo komaiba aransuba sukace ayya k'ila yanacan yana shan sharafin soyayarsama, kinsan su ya Abdulmaleek sai addu'a, k'ila kuma bazaizo gidanba saiya tashi daga aiki Dan wataran haka yakeyi.
    Dammmmm safna taji gabanta yafad'i, azuciyarta ta ce, "soyayya kuma?, wani kululun bak'in ciki yatokare mata mak'oshi ta had'iyeshi dak'yar, zamewa tayi takwanta visa gadon su khursiyya tana sauk'e ajiyar zuciya wadda su bama sukulaba hankalinsu nakan rigima akan wani wandon jins dakowa ya ce, " yanaso sukahau kokawa, can ALLAH yabama khursiyya sa'ar kwacewa daga hannun khairiyya ta sambad'a da gudu zuwa waje.
   Itama khairiyya ta take mata baya tana fad'in wlhy baki isaba saidai kowa yahak'ura mu badashi, daidai zasushiga d'akin Ammi bobo yashigo falon da sallama.
     Sanye yake cikin suit blue, komai na jikinsa blue ne amma banda belt da takalmi dasuka kasance jajaye, dressing d'in bak'aramin feeting d'insa yayiba, masha ALLAH.
    hannunsa yatura cikin aljihun wandonsa yajingina da kujera yana kallonsu khairiyya daketa zagaye falon batareda sunkula dashiba.
    Ganinfa bamasu gansaba yasakashi daka musu tsawa, kai!!! Wane irin iskancine wannan?, zaku maida mana gida filin polo?.
   Can suka tsaya suna mazurai, yacire hannunsa daga aljihu ya nunasu Ku nakula kafin kubar gidannan saina ta6a lfyar jikinku?, dannaga wani tashen iskanci kukeji yanzu?, to ubanmiye ya had'aku?!!.
    suduka saida sukad'an razana da tsawar dayayi, sukad'anja baya khairiyya ta CE, "Yaya wandonefa nad'auka shine ta kwace tagudo.
     Tsaki yayi ya ce, " wandon nawaye?.
   Da Sauri khursiyya ta ce, "nawanefa, itama khairiyya ta CE, " Yaya k'arya takeyi nawanefa.
     Kansa yadafe Dan suna Neman samasa ciwonkai ma wlhy...
    Ammi tafito ta ce, "miya faru kuma tom and Jerry?.
    Suduka suka nufi Ammi suna mata bayani.....
    Hannu Ammi tad'aga musu ta ce, " ainagaya muku kubar sayen Abu guda d'aya saboda gudun irin wannan ranar to gashinan kun saya kuma yanzu bawaje d'aya zaku kasanceba sannan kowa yanaso.
   Khairiyya tayi kwalkwal zatayi kuka, Ammi tafasan Nafi son wandon kuma nace ta d'auki rigar nitabani wandon amma tak'i yarda.
   Hannu bobo yamik'a ya ce, "kubani wandon....
     Jikin khirsiyya na Rawa tamik'a masa, yana kar6a ya haura saman Appa batareda yasake maganaba.
     Khairiya tafara hawaye tana hararar khursiyya Ammi ta ce, " wlhy ALLAH yabaku sa'a kunsandai halin mukarram sarai ba bak'oku bane, idan darabon saiya zaneku kuna a amare kukuka sani, idan kunason kanku da arzik'in toku kama kanku danni babu ruwana wlhy, tana gama fad'a itama tahaye saman Appa.
     Jiki asanyaye suka koma d'akinsu, Safna ta kallesu tana fad'in kukuma lfy INA wandon?.
     Baki Khairiyya ta turo ta ce, "bataja ya Abdulmaleek ya kwaceba.
    Zumbur safna tamik'e tana fad'in yazone?.
      Basu tanka mataba Dan duk haushinsa ya ishesu.
    Itama bata saurari amsa daga garesuba tafito falon, jin k'amshin turarensa daya tafi yabari yasakata murmushin jindad'i, tasan yanzu yana wajen iyayensa danhaka tafito  harabar gidan.
     Ganin motarsa yasakata k'ara sakin wani murmushin, bud'e gaban motar tayi tashige Dan bai kulleba.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now