3

4.3K 237 6
                                    

              💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

       Bilyn Abdull ce

Pg 4

.......Safna tadanna hon afusace, da sauri maigadinsu yazo yabud'e mata get, ta danna hancin motarta cikin gidan, tana kashe motar tasuri jakarta da wayoyinta zuwa cikin gida.
    Wani wawan tsaki tasaki Dan ganin Rahma k'anwarsu kwance akan cinyar ummi.
   Daga Ummi har Rahma baki suka saki suna kallonta.
  Ummi ta ce, "kekuma lfy daga shigiwa zakiyi mana tsaki?, wai Safna ban hanaki halinnanba ne?.
   Baki ta turo gaba tana Harar Rahma, haba Ummi ALLAH wannan abun kunyane, wannan k'atuwar yarinyar shrkara 17 haryanzu bataida halin yaraba, aiiko jafar d'in ya Shaheed baya wannan ta6arar.
   Rahma ta girgiza kai danjin akanta yayar tata take tada jijiyar wuya, tarasa miyasa basa shan inuwa d'aya da 'Yar uwarta, (ita aganinta abin yafara wuce fad'an sako da sako), afili kuma sai ta ce, " aunty Safna miyayi zafi shiba wutaba, zauna ki huta Dan ALLAH.......
   Duka takaima Rahma ummi ta kare, Safna kishiga hankalinki danifa, uwarmi tamiki daga shigowa?.
    Cikin huci ta ce, "ummi kinajinfa maganar datake fad'amin, ALLAH yarinyarnan ta rainani, zan koya miki hankali kwanannan wlhy.
   Ummi ta tamke fuska tana nunama safna hanya, kinga tashimin anan.
   Ran safna a6ace tabar wajen tanufi d'akinsu tana mita.
   Rahma kam ta sauke ajiyar zuciya tana k'ara gyara kwanciyarta.
  Ummi ma kai ta girgiza ALLAH ya shiryaki Safna tafad'a tana shafa kan Rahma.

Safna tacire kayanta tanata masifa harta shiga wanka, (nikam mamaki take bani, Dan banga abin fad'aba anan).

Rahma tanason shiga d'akinsu tayi wanka tana tsoron masifar Safna, Dan tasan wlhy bata bartaba, k'ilama yau kwana zatayi bala inta da mitar tsiyarta.
   d'akin umminsu tanufa dantayi wankanta kawai, yafi sauk'i.

+++++++++++++++
       Bobo yana kwance ad'akinsa sai juye2 yakeyi, barci yakesonyi amma yak'i d'aukarsa, maganar Ammi ce kemasa yawo akwakwalwa.
    Yasan Ammi sairai babu sauk'ice, indai Abu ya6ata mata rai saita d'auki mataki, shikam yana tsoron zancennan yaje kunnen Appansu, yad'an cije le6e yana sauke numfashi, tund'azu soyake yafita amma yana shakkar had'uwa da Appa.
    Yasan fita tazame masa tilas Dan dole zasu had'u wajen cin abinci.......
   Bai rufe bakiba aka buga k'ofar, batarda ya d'agoba ya ce, "ashigo.
   Khairiyyace k'anwarsa, cikeda da tsoro ta ce, " yaya kazo wai aci abinci.
    Hannu yad'aga mata kawai, bata gane nufinsaba Dan haka ta ce, "ka k'oshi kuma yaa Bobo!?.
   Harara ya watso mata sannan yamik'e, da sauri tayi waje, shikuma yad'auki doguwar riga fara yazura yafito.

Kowa ya hallara shikad'ai ake jira, rissinawa yayi yagaida Appa da Ammi sannan yazauna.
   Khursiyya ta ce, " yaya ina yini, harara ya watsa mata, ya ce, "k d'azu dasafe miya hanaki wankemin bayi?.
   Kanta ak'asa ta ce, " wlhy yaya ina uzirin makarantane, dakuma nadawo na manta.
   Tsaki yaja kawai baisake cewa komaiva.
  Ammi tazubama Appa abinci, tasakama kanta, kairiyya kuma tasakama bobo shima, suma suka zuba.
     Nawal tana kusada Appa.

Suna cikin cin abinci kamar antsikari Nawal ta ce, "aunty khursiyya.
    Na'am Nawal miya faru?, khursiyya ta fad'a.
    Cike da murna ta ce, " Ammi tace nima ankusa kawomin momyna.
     Ayya my dear natayaki murna.
   Ran bobo yak'ara 6aci, fuska ad'aure ya gallama Nawal harara, Appa da Ammi suna kallonsa, amma basuce komaiba.
   Itama Nawal saitayi shiru kafin ya bibbigeta, Dan dukda yana wasa da ita hakan bai hana yaci k'aniyartaba idan ta k'uleshi.

Harsuka kammala cin abinci babu Wanda yakuma cewa komai, bayan sun kammala kowa yakama gabansa.
     Bobo yaji dad'i Affa baimasa maganaba har dare.

Da daddare yana zaune a babban falo daga can gefe, wasu buks yake dubawa, khairiyya da khursiyya da Nawal suna zaune suma kallo sukeyi, Ammi tasakko daga d'akin Appa, takkali Bobo da hankalinsa kekan bincike ta ce, "Mukarram kaje Appanku na kiranka.
   Wani irin fad'uwar gaba da tsinkewar zuciya suka sameshi a lokaci d'aya, bakinsa yana rawa yace Ammi lfy kuwa?.
     Babu komai mikake tunani?.
   " kai ya girgiza mata yana sauke ajiyar zuciya."
   Asanyaye ya haura saman Appa, Appa nazaune yana kallon labarai Bobo yashiga da sallama.
   Fuska asake Appa ya amsa, bayan yazauna ya ce, "Appa gani.
     Appa dattijo mai hikima da iya kama mutum, saiyayi murmushi, dama bawani Abu bane, inasonjin ya shari'arku da B.. Sadiq?.
   Ajiyar zuciya bobo yasauke wadda hartaso bama Appa dariya amma saiya dake.
    Komai yayi Normal Appa, Dan insha ALLAHU zuwa Monday komai zai k'are, alk'ali zai yanke hukunci.
   A to Alhmdllh haka nakesonji, daga nan Appa yacigaba dajansa da hira harya saki jikinsa.
   Cikin hikima Appa ya ce, "Mukarram waini yamaganar aurene?, kodai haryanzu?.

Bobo yad'an Sosa gefen wuyansa Appa Dan ALLAH kudaina yawan damuwa akan aurena insha ALLAH zanyi amma ba yanzuba.
   Tofa, bayanzuba sai yaushe Mukarram?, koso kake saika tsufa agidane?, ai ko bakayi aure Dan kankaba kayi Dan Zuhra, kullum maganar yarinyar nan momy momy to yakamata asamo mata momyn nan.
    Inkuma bazaka iyaba ba awannan karonma zan samo maka matar aure, Dan naga kai tsoron matan kakeji.
   Appa kayi hak'uri, ak'aramin lokaci, insha ALLAHU nanda k'arshen shekara zanyi.
    Appa yad'an zaro ido, Mukarram karshen shekarafa kace?, kai kana ganin zamu iya barinka harnan da watanni Tara babu aure, nifa nagaji da ganinka hakanan gsky.
   Ammi tashigo hannunta d'auke da tire, yaa is'haq yana biye da ita.

Appa ya ce, "yauwa aii gara dakukazo.
   To miya faru Alhaji?.

A'a wai Murarram nakeyima zancen sure, shine yake rik'ona abarsa sai k'arshen shekara.
   K'arshen shekara kuma ya ishaq yafad'a yana kallon Bobo dayake wani 6ata rai. Kai idan anbarka zuwa k'arshen shekarar saika yarda?.
      " emana yaya aii nake ganin zaifi ko?.
     shin wai Abdulmalik kodai bakada lfy ne?.
     Yaya banida lfy kuma kamar ya?.
   Harararsa ya ishaq yayi ya ce, " bansaniba.
    Appa ya k'atsemusu zancen dafad'in Ishaq babu wani abinda ke damunsa iya shegene kawai irin nasa. Amma nima abin yana bani mamaki wlhy, hakamafa lokacin aurensa na farko mukaita fama, kokuwa maganar ishaq gsky ce?.
     Ran Bobo yakuma 6aci, aii dama yasan tunda wannan masifaffen yazo saidai ALLAH, gashinan yak'arama wutar fetir.......
    Appa yakatsema Bobo tunani da fad'in Mukarram baka jinane?.
   Kansa ya girgiza, murya a sark'e ya ce, "wlhy Appa lfy ta k'alau.
   Appa ya kalli ammi, kai ammi ta girgizama Appa kawai.
   Appa yayi murmushi, ya ce, " shikenan Mukarram tashi kaje, ALLAH yakaimu k'arshen shekarar.
   Yakwa mik'e yana washe baki yafice, azuciyarsa ya ce, "su yaa Ishaq ansamu game over.
   (Nikam dariya yabani, Dan k'ila shine mai game over d'in).

Ammi ta ce, " Alhaji nifa ban fahimcekaba?.
    Appa yay murmushi, yanzu zan fahimtar daku, shekaran jiya naje mun gaisa da abokina Alh bilal, anan nakemasa maganar ranshin auren Mukarram abin yana damuna.
   To yanzudai azancen nan danake muku munyanke hukuncin had'a auren mukarram da 'Yar wajensa.
    Ammi tayi murmushi tana fad'in Alhmdllh, kai nayi farinciki wlhy, ALLAH ya tabbatar da alkairi.
   Amin ya ishaq yafad'a shima fuskarsa cike da annuri.
  Ya gaida Appa Dan ko gaisawa basuyiba ma, daganan suka tattauna akan bikin, ya Ishaq yatafi...........

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now