32

3.9K 204 1
                                    

              💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 33

Kafad'a ta d'an nok'e tana girgiza kai dantanajin  kunyar mutanen dake wajen.
   Tayi k'asa da kanta tana kallon k'asa, bata ankaraba taji an rungumeta, ahankali tasauke ajiyar zuciya, shima ajiyar zuciyar ya sauke, cikin kunnenta ya ce, "haba my cute bakiyi missing d'inaba ko?.
    Batace komaiba saidai yanajin alamar murmushin datakeyi.
      Ya sumbaci wuyanta, Ya hamzane dayaga bobo na Neman ruftawa gakuma Appa awajen sai ya k'araso inda suke, ya ce, " baban soyayya kuzo muje gida saikuyi ko?.
  Da sauri Rahma tazare jikinta, bobo yad'an kalleta sannan yadawo da kallonsa ga ya Hamza, Yaya karfa kazama..... Hummm kodayake baradai nayi shiru kawai.
    Dariya ya Hamza yayi ya ce, "a'a fad'i karta kasheka.
    Um um bazan fad'aba narufa maka asiri dai, my cute kona fad'a miki?.
     Girgiza kai Rahma tayi tana murmushi.
   Ya Hamza ya ce, " karki damu Rahma cemasa yafad'a mana, nima saina tona aii yanzunnan.
   'Yar dariya bobo yayi Yakama hannun Rahma suka tafi, ya Hamza yabiyosu abaya suka tafi.
    Yanzun ya Hamza da bobo da Rahma amota d'aya suka tafi, Nawal kam tana wajen Appa, tunda bobo yarungume Rahma Appa yakama hannun Nawal sukabar wajen yana murmushi.

Suna zuwa gida asibiti aka wuce dasu Rahma, Alhamdllh babu wata matsala saidai 'yan raunukan da Rahma taji, ya sulaiman ya dubata tareda basu magunguna sai gida.
     Tunkan su iso gidan yacika da dangi, su Rahma suna shigowa dangi suka rungumesu anata kuka, bayan gama murnar ganin juna Rahma tashige d'akinta tayi wanka tayima Nawal.
    Aka kawo musu abinci sukaci sukasha magani sai barci.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
          Haba ummi yazakice bandamu da 6atan su Rahma ba?, 'Yar uwatace fa, Dan ALLAH kibar fad'a kadama wani yaji zata gskyne.
    Oh da k'yarya nakeyi?.
   A'a ummi nidai bance kina k'aryabafa.
    Banza ummi tayi da ita, tajuya zata fita.
    Safna ta marairaice murya ummi toyanzu mikikeso nayi dazai sakaki farinciki?.
    Kafin ummi tabata amsa sukaji sallamar baseera.
   Tarisina ta gaida ummi, cikin fara'a ta amsa sannan tafice.
    Ummi na fita basira tamatso Kusada safna, k'awata mike faruwane wai naga ummi akanki?.
     Mtsoooww kibari kawai akan 6atan Rahma ne........ Takwashe komai tafad'a mata.
     Baseera tazunguri safna kefa banzace miyasa bazakice zakije kizauna da ita harta samu lfy ba, daganan basaiki gwada sa'arkiba kema.
    Kai hakanefa baseera, wlhy banyi wannan tunaninba ma, duk kaina yakulle baya kawo wuta.
     Aikin 6urrr inji tusa, kinga tashi maza ki shirya.
   Gudu gudu sauri Sauri safna tashirya kayan dazasukai fiye da sati d'aya, tad'auki duk abinda zata buk'ata ta shirya sanan sukanufi d'akin ummi.
    Tana zaune da Alana tana wayane da wata 'Yar uwar tata Dan tana bata labarin 6atan Rahma dakuma dawowarsu yau.
    Tsayawa sukayi harta gama, takalli safna da akwatin kekuma INA zaki da kaya haka?.
     Ummi zanje gidan Rahma na zauna danna ringa taimaka mata har jikinta ya daidaita, naga baikamata ace anbarta da dangin mijiba tamkar batada kowa.
    Baki ummi ta washe ta ce, "kai naji dad'i wlhy safna ALLAH yayimiki albarka, aihaka akeso, kuma tahakane zuminci ke k'ara dank'o.
    Ki gaisheta muma insha ALLAHU gobe zamuzo mu dubasu.
   ALLAH yakaimu ummi, saikunzo safna tafad'a tana murmushi.
    To saimunzo, baseera kigaida mutanen gidan.
  To ummi zasuji.

Safna da baseera suka fito sai gidansu Rahma, sanda suka iso mutane duksun tafi, daga Ammi da inna sai khairiyya da khursiyya suka rage, har k'asa su safna suka durk'usa suka gaida su Ammi.
    Safna ta ce, " Ammi inasu Rahman?.
     Murmushi Ammi tayi ta ce, "aii har yanzu barci sukeyi safna, yawajen su Maman taku?.
    Lfy lau suke Ammi, suma saigobe idan ALLAH yakaimu zasuzo.
    To ALLAH yakaimu lfy.
    Inazaku haka da akwati? Ammi tayi tambayar tana kallon safna.
     Safna tagyara zamanta tana k'ara marairaice fuska tamkar mutuniyar kirki, Ammi dama canayi bara nazo na zauna da ita harta samu k'arfin jikinta, Dan baikamata atakura su khairiyyaba ga bikinsu yana matsowa.
   Murmushi Ammi tayi ta ce, " lallai kinyi tunani Safna, ALLAH yay miki albarka.
      Bobo dake bakin k'ofar Rahma yana niyayyar fitowa yatsaya sauraren tattaunawar Ammi da safna.
       Ransa a 6ace yakalli Ammi suka had'a ido, yaturo baki gaba, murmushi Ammi tamasa tareda yimasa magana da idanu, wai karyace komai.
   Kauda kai yayi yana d'an sassauta turo bakinsa, shifa wlhy yatsani yarinyarnan, amma shine yanzu za'ace tazauna taredasu mtsoooww yaja siririn tsaki.
     Takowa yayi ahankali zuwa cikin falon, jin k'amshinsa da takunsa yasaka safna da baseera juyowa, kan ubancan kai, aii ba safnaba har baseera yau saida tashiga rud'ani.
    Dukda yad'an rame amma k'yawun haibarsa na nan, kuma yak'ara haske sajennan yakwanta luf luf, sai k'amshin turarensa ketashi afalon mai sanyin dad'i, har yazauna Kusada Ammi idon baseera da safna na Kansa, baseera ta ce, "a ranta lallai dolene safna ta haukace,” Ashe haka guy d'in ya had'u masha ALLAHU.
      Bobo yay d'an guntun tsaki Dan baya son kallo, ganin bazasu daina kallonsaba shikuma sun gundureshi, saiya katsesu dafad'in yakuke?.
      Dandanan suka dawo hayyacinsu danjin saukar muryarsa mai ratsa jiki da 6argo.
     Cikin in ina suka gaisheshi, ya amsa da lfy, tamkar yanda yasaba.
    Khursiyya da khairiyya suka fito saga kichin bobo ya kallesu, harkun mammala abincin?.
      Ya Abdulmaleek ai yau abinda kafiso muka dafa zakacidai ko?.
           Murmushi yamusu tareda gyad'a kai kawai.
    Suma dariyar sukayi suna mai farincikin ganin yayansu yau acikin farinciki, khairiyya ta CE, " Yaya tunda aunty Rahma tadawo yanzu saika Dage dacin abinci kayi k'iba.
    Harara bobo yasakar musu yana fad'in Ammi wlhy yarannan sun rainani.
     Ammi da inna suka tuntsure da dariya, inna ta ce, "Abdulmaleek aiko kura da 'ya 'yanta take wasa a daji, ammi ta ce, " wlhy kuwa inna.
    Ammi takalli su khairiyya ta ce, ''kutaso heebba mutafi gida hakannan ko?, tunda kungama aikin, fuska suka shagwa6e, khursiyya ta ce, "Ammi wai kina nufin harda mu?, harararsu ammi tayi hardaku mana, tunda ga safna nan tazo kukuma basaiku koma gidaba, dama ga hidima fall cikinku, dasafe saikuringa zuwa ko?.
     Su saima yanzu suka kuladasu safna dake zaune.
     Ammi takallesu tareda fad'in kuna 6ata mana lokacifa gakuma Deriver yana jiranmu.
    d'akin Rahma suka shiga sunata zum6ura baki, haryanzu su Rahma barci sukeyi abinsu.
   Hibba dake barci suka d'akko suka fito, suna son yarinyar sosai, yanzu haka komai NATA Yakoma d'akinsu, har anmaida mata suna Autar Ammi.
     Har mota safna da bobo suka raka ammi.

Bayan su Ammi sun tafi shima bobo ficewarsa yayi batareda yasake ko kallon indasu safna sukeba.
     Suma cikin gida suka koma suka Shiga d'akin Rahma wadda har yanzu suna barci.
    Suna nan zaune har aka kira magriba baseera tamik'e zata tafi, bayan Safna tarakata k'ofar gida tashiga adaidaita, baseera tana k'ara jaddada mata karfa tayi wasa da damarta, tayi k'ok'i kimai ta aiwatar yanda yadace.
     Safna ta ce, " karkiji komai insha ALLAH zanyi k'ok'ari.
    Okey sainajiki k'awar rai da rai.
   Dariya safna tayi ta ce, "hakane my sweet baseera, suka tafa mai adaidaita yaja suka wuce.

              Safna tana Shiga gidan ta Tatar Rahma ta tashi, tayi farinciki daganin 'Yar uwarta danhaka ta rungumeta, aunty safna yaushe kikazo?. Tun d'azun Nazo kina barci ya jikin?. Da sauk'i saidai jikina yana ciwo tayi maganar tana yatsine fuska, to sannu auta cewar safna, kai kawai Rahma tad'aga mata.
Ta ce, " aunty safna yasu ummi?.
    Suna nan k'alau suncema a gaisheki gobe zasuzo, tom ALLAH yakaimu lfy, Yakuma naji gidan shiru?.
    Kowa yatafi saini kad'ai, Nima zan zauna anan ne harki samu sauk'i.
   Lah da gsk?.
Eh mana safna tafad'a tana murmushi, Rahma tana juya baya safna ta galla mata harara.
    Itakam rahma dabatasan tanayiba ta rungumeta tanamai farincikin faruwar hakan.

Bayan anyi sallar magriba bobo yadawo gidan, kaitsaye d'akin Rahma yanufa, har yanzu suna zaune da safna suna hira, safna tana hirarne kawai amma jitake tamkar ta shak'e Rahma tamutu.
   Sallamarsace tasakasu d'agowa suduka tareda amsawa, suna had'a ido da Rahma yay mata murmushi, ya jikin? Yafad'a cikin sassanyar muryarsa, Rahma tai k'asa da kai sannan ta ce, "da sauk'i.
   To Alhamdllh, kinyi sallah ko?.
   Rahma ta girgiza kai alamar a'a.
   Miyasa?, kobak'yayine?.
    Girgiza kai Rahma tasake yi cikeda kunya, mik'ewa tayi tashiga bayin.
   Harta Shiga bobo yana binta da kallo, saida tashige sannan yajuya yafita.
    Safna tabishi da kallo zuciyarta na suya, jibi Dan ALLAH yama nuna tamkar baisan da ita ad'akinba, tayi k'wafa da fad'in zakazo hannuna ai.

Na CE, " hummm.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
      Yau kwanan su Rahma 2 da dawowa, dangi kam kullum sunata tururuwar zuwa dubasu damusu jaje, A6angaren bobo kuwa kulawa yake basu ta musamman, dai dai da abinci saiyace shine zai bata abaki, itakuma taita zame zame, wata shafta sai anzo shan magani, saida lallashi da mazurai takesha.
     Ran safna na 6aci, Dan aganinta wani abunma bobo yanayi da biyune, Dan haka take k'arajin tsanar Rahma aranta, kullum kuma zuciyarta tana k'ara nunkuwane wajen son Raba Rahma da bobo kota halin k'ak'ane.

++++++++++
     Yau tsawon kwanan safna hud'u agidan amma takasa aiwatar da burinta nasakama bobo magani, Dan ko abinci bayaci taredasu saidai a d'akinsa, kuma su khairiyya suna gamawa zasu d'auki nasa sukai d'akinsa, itakam har yanzu bata ta6a shiga d'akinsaba.
    Bobo kam bak'aramar tsana yayima safna ba, Dan sai yanzun yakejin Kalmar bata sonsa azuciyarsa, kuma dukkan take takenta yanzu yana lura dashi, takan bashi dariya wlhy Dan ganin yanda take nuna masa alamomin so.

    Yaukam bobo yana cikin damuwa Dan yana buk'atar kasancewa da matarsa, tunda yanada lfy, sai juye juye yake agado, jiyake d'akin yayi masa girma, ya kalli agogon dake manne abangon d'akin 1:5pm na dare, yad'anyi tsaki tareda mik'ewa.
   Wani story book yad'auka da filo yafito harabar gidan, wasu kujeru yanufa masu k'yau dake k'ark'ashin wata rumfar bunu, handky d'insa yasaka yashare kujerar da tebirin sannan ya zauna, yad'ora k'afafunsa bisa tebird'in.
    Duk abinda bobo keyi akan idon safna ne, murmushi tasaki sannan ciki sand'a tafito dankar Rahma taji motsinta.
   Kai tsaye wajensa tanufo..........

ABDUL-MALEEK (BOBO)Kde žijí příběhy. Začni objevovat