9

3.1K 190 1
                                    

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 10

  Kafin la'asar zazza6i yarufe Rahma, tana d'akin Abba kwance ak'udundune, ya Muneer yashogo da Dr kaleed har cikin falon Abba.
   Abba da kansa yashiga d'akinsa yatasoda Rahma daketa rawar sanyi, saman kujera ya zaunar da'ita Doctor yashiga aikinsa, babu wata matsala Alhaji 'Yar damuwace kawai Dr Kaleed yafad'a.
   Abba ya ce, "to Dr babu wani taimako da za'ad'an bata kenan?.
  A'a zan mata allura  da magani tad'an samu barci, insha ALLAHU daga nan zuwa yamma zata koma Normal, yanzudai idan namata allurar tad'an samu koda tee ne tasha saitasha magani tayi wanka da ruwa maid'an sanyi ta kwanta, insha ALLAHU normal zata tashi nanda anjima.
   To madallah Dr mungode sosai.
  Babu damuwa Alhaji aii aikinane.
   Babu 6ata lokaci Dr yayma Rahma duk abinda yadace, ummi tabata shayi tad'ansha kad'an tabata magani Wanda tashashi da k'yar Dan Rahma akwai tsoron allura da magani, bataso ko kad'an allurarma saida lallashi akayi.
  Bayan tasha maganin ummi ta taimaka mata tayi wanna a bayin Abba, kaya aka d'akko mata tasaka takuma kwanciyarta a gadon Abba sai barci.

Hummmm wai ina Safna?.
   Tana nan acikingidan kuma labari yakai mata, ancanjeta da Rahma, Dan haka tadage tarink'a tsallen murna ita taci nasara, shikenan zata mallaki bobonta nanda lokaci kad'an, har ruwa tazuba k'asa tasha Dan dad'i.
   Cikeda farinciki takira Baseera ta guntsa mata, murna sosai ta tayata harda jinjina da yaba k'ok'arinta na dagiya.
  Bayan sungama da baseera takira zeenat itama, zeenat ta ce, " wlhy Safana kin tafka babban kuskure a rayuwarki, na tabata nangaba saikinyi Dana sani Mara iyaka, son zuciya yasa kin bijirema iyayenki akan Wanda baima San da zamankiba, ke kanki bakisan Inda yakeba yanzu, bakida tabbacin zai kar6eki kobazai kar6i soyayyarkiba, wlhy kidaina biyema hud'ubar baseera zatayita kaiki tana baroki a tashar wahala ne......
    Safna ta k'atseta atsawace, kee!!! Dallah malama yimin shiru, nakiraki nafad'a mikine danki tayani murna ba surutun banzaba, aiikin banza kawai mtsowww taja tsaki tana yanke wayar.
  
"Daga can Zeenat ta girgiza kai tana fad'in ALLAH ya shiryeki Safna, amma zakiyi nadama wlhy na tabbatar."

Babu Wanda yakumabi takan Safna shagalin biki akacigaba da gudanarwa, itama tafita harkar kowa agidan lamuran gabanta kawai takeyi harda yima Rahma dariyar mugunta.
  Na ce, "hummmm.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*
       Bobo ya lalubo wayarsa dake wringing daga aljihun jins d'insa, ido yad'an zaro tareda kallon Ya Sulaiman dake duba yarinyar da akaima fad'e.
   Lfy kuwa bobo?.
Tab ya Is'haq ne kasanfa sunacan suna jiranmu..... K'ara kiran da akayine yasa Yakuma kallon wayar, ya is'haq d'innedai, d'agawa yayi tareda yin sallama.
  Abdulmalik wai kuna inane kaida sulaiman?, ya Is'haq yafad'a daga can.
   Wlhy muna asibiti wajen yarinyarnan amma gamunan zuwa Ku k'ara hak'uri.
  Tom yakamatafa kuyi sauri Dan akwai abubuwa agabanmu masu yawa.
   Gamunan yanzunan insha ALLAHU.
   yanke wayar yayi tareda dawo da kallonsa kan ya sulaiman, ya Sulaiman yakamatafa muje kasandai masifar babban yaya, muk'arasa kafin ya k'ulu.
    Gsky ne muje kawai aii nagama harma takoma bacci.
   Bobo yad'an lek'a fuskarta, ya ce, " baiwar ALLAH, wlhy rashin maganar yarinyarnan yana damuna, yakamatafa ace iyayenta sunsan halin datake ciki.
   Hakane gsky to amma yazamuyi? tunda bamusan idan takeba, saidai mucigaba da addu'a. Idan kuma tak'ara samun lfy mubi shawarar Ammi mumaidata wajenta kawai.
  To shikenan bobo yafad'a yana fitowa.
   Waje yanufa shikuma ya sulaiman yashiga office Dan ajiye kayan hannunsa.
   Babu dad'ewa yafito, mota yashiga Inda bobo ke zaune a mazaunin direba, bobo yatada motar suka fice daga asibitin.

.+.
     Gidansu Safna kuwa anyi shirin kamu Wanda aka had'a a babban harabar gidan nasu, saidai matsalar amarya babu lfya tana d'akin Abba kwance tana barci.
    Hafsat matar ya Shaheed ta kalli ummi, ummi to yanzu yaza'ayine harfa dangin angon sun iso ga babu amarya, dama Safna zata mana alfarmar yanzu kawai saita zauna amadadin Rahma d'in.
   A'a barta kawai hafsat, nibanamaso muna saka Safna acinkin sha'anin bikinnan, takalli agogon dake hannunta, hafsat inaga bari kawai atada Rahma d'in dukda dai bata dad'e da kwanciyaba.
   A'a ummi abarta kawai likitafa ya ce, tana buk'atar Hutu, gashi dangin ango since k'arfe tara akwai mother Night, yakamata tasamu ishashshen barci kafin sannan, yanzu bari nayima Basman aunty Yahanasu magana saita shirya tazauna amadadin amarya tunda kusan kansu d'aya.
   Yauwa hakama yafi, dama gasu suna kama ba laifi.
  
Haka suka saka Basma aunty yahanasu k'anwar ummi tashirya tsaf tamkar amaryar, idanma baka saniba saika d'auka Rahma d'ince Dan suna matuk'ar kama, idanuwa kawai Rahma zatafi Basma.
   Dahaka aka gudanar da kamu Wanda yak'ayatar da dangin ango, su khairiyya da khursiyya dasu aunty Rasheeda sai zuba lik'i suke wa amarya, Dan basusan ba amaryarsu bace.
  Dahakadai taro yatashi gab da magriba Alhmdllh.
 
Duk shagalinnan da akeyi Safna tana d'aki kwance abinta, da barcima takeyi kid'an da'aka sakane yasa tatashi tana mita da tsaki anhanata barci wai, wayarta ta d'auka takira *boy danneman k'arin bayani akan aikin data bashi.
  Ya ce, "mata yana nan yana k'ok'ari.
  Tana yanke wayar takira Baseera sukaita labarinsu Rabi duk akan bobone.
  Na CE hummmm.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now