17

3.3K 215 0
                                    

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 18

Hankali tashe Alh sunusi ya iso gidansa, ko fakin bai bari direbansa yagamaba yafice.
   Matarsa na zaune afalo itada k'annen Haneef d'in yafad'o ko sallama babu.
   Arazane suka mik'e suna binsa da kallon mamaki, dukda ba yaune rana tafarko daya fara shigowa gida ahakaba.
   Ina my son?, yafad'a aburkice.
  Cikin mamaki haj Falmata ta ce, "Haneef?.
   "Eh," ya bata amasa afusace.
   Yanzu babu dad'ewa yafita aii, wani abune yafaru?.
   Wata uwar harara yasakar mata, waike wace irin shashashar uwace?, wai kina nufin bakisan 'yan sanda sunzo har gidannan sun kamamin yaroba?.
    Afirgice ta ce, "naga takaina ni Falmi, yaushe hakan tafaru?, yanzufa Haneef d'in yashigo gidannan ya sauya kaya yafita.
   Bai sauraresuba yafice yabarsu cike da tashin hankali.
   Abin kamar wasa Alh sunusi har dare yana Neman Station  d'in da akakai Haneef amma babu ko Alamarsa, ransa yak'ara 6aci da harzuk'a, aiiko wlhy saiya d'auki mataki akan 'yan iskan police d'in dasukai k'arfin halin shigar masa gida harda kama masa tilon d'ansa namiji.
   Gida Yakoma danufin zaije ga Qumissioner of police gobe idan ALLAH ya kaimu, saidai zuciyarsa namasa rad'ad'i idan yatuna Haneef zai kwana a Station yau.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
   *_9:30pm_* ya isa gidansa duk agajiye, jinsa yake yau fes tunda ankama masa d'an iskan nan, bayan sun gaisa da mai gadi yashige cikin gidan.
    Babu kowa afalon, har TV akashe yake ga gidan tsit kamar babu kowa, da alama masu gidan har sunyi barci.
   K'ofar yamaida yarufe sannan yanufi d'akinsa, yazube kayan hannunsa cike da gajiya, babu 6ata lokaci yacire kayansa ya fad'a bayi domin yin wanka.
    Bayan yafito yagabatar da shafa'i da wutiri, 'yan dube dube yafayi da alama akwai abinda yakeson gani, amma babu, d'an k'aramin tsaki yayi tareda mik'ewa yafice.
 
Cikin barci Rahma taji ana bubbugata, afirgice ta tashi, Dan dama  tsorace takwanta, saboda rashin dawowar mai gidan.
    Ganin shine atsaye yasa ta sauke ajiyar zuciya, ahankali ta ce, "sannu da zuwa.
       Bai amsaba ya ce, " ina shayina?.
   Tad'an dafe kanta, wlhy na manta ne.
   Aii yanzu na tuna miki, yafad'a yana ficewa.

Asanyaye Rahma tasakko daga gadon, Dan barcin data fara yasa jikinta yin lakwas, haka ta k'arasa kicin tana jan k'aramin tsaki, idonta cike da barci tadafa masa shayin, tajuye akofi tareda yanka lemon tsami ta matsa aciki, tad'ora akan k'aramin tire tafice.
    Ganin baya falo gabanta yafad'i, kenanfa d'akinsa zata kai masa?, tai shiru kamar mai nazari, zuciyarta ta ce, "kije kikai karya huce Rahma ki k'ara jama kanji wani laifin", tunda tazo gidan yauce rana tafarko dazata Shiga d'akinsa, Dan haka k'irjinta keta dukan uku uku, haka tadaure ta kwankwasa, saida tayi kusan Monti biyu sannan ya ce, " tashigo.
    Ahankali ta tura k'ofar tashiga, wani k'amshi yadaki hancinta tashak'a talumshe idanunta, saikuma ta bud'e ta sauke akan Bobo dake zaune abakin gado yana latsa laptop, k'afarsa d'aya ak'asa d'ayar kuma ya tank'washeta a gadon, sanye yake da kayan barci ruwan ganye mai turuwa, tana mamakin yanda yakeson latsa laptop da karatun jarida.
   Jin shiru bata ajiyeba, bakuma tayi maganaba yasashi d'agowa ya kalleta, shima baiyi maganaba saidai tura mata k'aramin tebir na gilas dayayi.
   Ganin haka yasa itama tad'ora batareda ta ce, "k'alaba.
   Bayan ta ajiye saikuma tayi tsaye takasa tafiya.
   Yana danna laptop d'insa yana shan shayi, tsawon minti 7 ita batayi maganaba shikuma ya shareta yanata aikinsa, yakula bazatace komaiba, kuma akwai magana abakinta, Dan haka shi ya daure ya ajiye NASA shan k'amshin ya ce, " kinada matsalane?.
    Kad'an ta kalleshi taga har yanzu idonsa nakan laptop d'in.
    gyara tsayuwarta tayi, muryartan nan mai kasheshi ta daki kunnensa, dama sonake naji yau ko lfy Baka dawo da wuriba?.
    Cak ya tsaya da abinda yakeyi, yad'ago fararen idanunsa ya sauke akanta, sanye take cikin dogon hijjabinta har k'asa, sa6anin d'azu daya Tatar da ita da kayan barci.
   Ahankali yasauke ajiyar zuciya, koba komai yaji dad'in kulawarta agareshi, cikin miryarnan tasa ya ce, "babu wata Marsala aikine yamin yawa a office.
    " okey saida safe."
                    Harta kai k'ofa yana binta da kallo, yadaure ya ce, "incedai babu wata damuwa daga babyn taki?.
    Bata juyoba amma ta tsaya, Dan furucinsa na k'arshe yaymata dad'i, muryarta araunane ta ce, " a'a babu Marsala, saidai tata jiran dawowarka, harta gaji tayi barci..... Bata jira amsarsaba tafice.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now