43

3.5K 193 0
                                    

              💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 44

Ina mai baki shawara amatsayina na mijin k'anwarki, ki nutsu kinemi miji kiyi aure kidaina wahalar da kanki akaina.
   Amatsayinki na wadda tayi kuskure abaya yakamata kiyi zaman gyarashi yanzu, sannan ki d'auki sona dakike ik'irarin kinayi ki jefar dashi gefe ki tsarkake zuciyarki, ki daina biyema k'awayen banza suna sakaki a hanyar hallaka na bin bokaye.....
     Cikin matuk'ar mamaki Safna take kallonsa, azuciyarta ta ce, "a ina yasan wannan?.
    Kamar yasan tunanin datake yayd'an murmushi tareda jinjina kai, yacigaba da fad'in kina mamakin ina nasani ko? Humm hakan babu inda zai kaiki wlhy saidai kiyita komawa baya arayuwarki, Safna babu abinda ke cutar da rayuwarki sai son zuciya, to son zuciya kuma facin zuciyane.
     Na tabbata ALLAH ya jarabceki da sonane saboda hakan yazamarma masu hali irinnaki ishara.
   Da'ace su Abba basuda Rahma dasunji kunya awaccan ranar dakika nuna musu basu isaba, saboda k'ok'arin kunyatasu dakikayi akan dalilinki mara tushe.
   Shin alokacin kinada tabbacin sake ganina?, kokuwa idan kin ganni kinada tabbacin zan kar6i soyayyarkine?, amma saboda son zuciya kika bijirema iyayenki akaina, wannan itace jarabawa tafarko dakika fara fad'uwa arayuwarki.
    Safna iyayenmu sunfi kowa sonmu Dan haka bazasu cutar damuba, idan baki saniba zan fad'a miki ayau, tunda nake banta6a za6ar matar aureba da kaina.
   Matata ta farko ma iyayenane suka za6amin, dukda banasonta amma nayima iyayena biyayya nakar6i k'yautarsu da hannu bibbiyu, biyayyar danamusu ban bijireba sainaci riba, daga ni'ima har Rahma sunzamemin alkairi arayuwata, wadda na tabbata da auren soyayya nayi bazanci riba hakaba, kema na tabbata dakinma iyayenki biyayya dakinyi gamon katar da abinda kikeso, amma kinga sakamakon da bijirewar taja miki yanzu, saidai sharri shaid'an dana zuciya sun danneki kin kasa ganewa bare kiyi nadama harki nemi afuwar iyayenki.
   To inamai tabbatar miki idan baki gyaraba haka zakiyita fad'uwa ak'asa, ki k'are rayuwarki a bibiyar tamu rayuwar, gashi mukuma kullum farincikine ke k'ara baibaye rayuwarmu saboda albarkar iyaye dake bibiyarmu.
    _amatsayinmu na 'Ya'ya wad'anda iyayenmu sukasha wahala wajen haihuwarmu, rainanmu, karatunmu, tarbiyyarmu, basa son kukanmu, kulada lafiyarmu daduk wani motsinmu, amma ayayin damuka girma muka mallaki hankalinkanmu lokacin daya kamata mu share hawayensu, amma sai suka nemi wata alfarma agaremu  muka bijire musu, saboda mu muna ganin mun waye su mutanen Dane, mukuma 'ya'yan zamani wad'anda boko tagina, shin kuwa muna ganin ALLAH zai k'yalemu kuwa?, aganina babu abinda 'ya'ya zasuyi aduniya su biya iyayensu akan hidima da d'awauniyar dasukayi dasu suna k'anana._
       Akwai inda zaka iya bijirema iyaye kaci riba, shine idan sunce kasa6ama ALLAH, wannankam ba'a yarda kamusu biyayyaba.
     Idanfa ta gsky da tsarin addini za'abi, iyaye akace suza6ama 'Ya'ya mijin farko, idan kuma k'addara ta gifta hartayi zawarci to wannan tanada 'yancin za6ama kanta akaro na biyu tunda ta mallaki hankalin kanta.
    Safna kije ki tsugguna ga iyayenki kinemi gafararsu na tabbata insha ALLAHU ko yayane saikinji sona yaragu azuciyarki.
     Inhar iyaye na fushi dakai tom dolene kaita tsintar kanka cikin asara, bafa zaka sami sassauciba harsai sun janye fushinsu akanka, tokema ki gwada ki gani insha ALLAHU zaki dace.......
   
Shashshekar kukan Safna ne yakatsemasa dogon bayanin daya d'akko, d'ago k'yawawan idanunsa yayi yana kallonta, ya ce, "ba kuka zakiyiba inhar nasihata tashigeki, nadama zakiyi, kuma ki d'auki hanyar gyarawa.
     Cikin shashshekar kuka safna ta ce, " duk abinda kafad'a gsky ne, amma wlhy akowane dak'ika na rayuwata k'ara sonka nakeyi, narasa yanda zanyi nacireka araina, ina sonka so bana wasaba.
    Tabashi tausayi kwari da gsk, Dan haka cikin taushin murya ya ce, "kiyi hak'uri Safna, kimik'a lamarinki ga ALLAH shine zai taimakeki, na tabbata shaid'an nak'ara hura wutar sonane azuciyarki Dan kawai yaraba zumincin dake tsakaninki da 'Yar uwarki, Yakuma cigaba da 6atar dake acikin duhuwa kikasa rok'ar gafarar iyayenki bare harkici riba a rayuwarki.
   Zan tayaki da addu'a ALLAH yacire miki sona azuciyarki kema yabaki miji nagari maisonki fiye da komai amadadina, nabaki kwana uku kije kiyi tunani kuma kiduk'ufa da addu'a Nina zan tayaki.
    Jinjina kai Safna tayi cikin sanyin jiki, ga hawaye sha6e sha6e afuskarta, yazaro farin handky d'insa daga aljihu sai tashin k'amshi yake yabata.
   Hannu biyu tasaka takar6a tareda fad'in ngd ya Abdulmaleek, ALLAH yabiyaka da mafificiyar nasara, yasakama rayuwarka da mafificin alkairi.
   Jinjina mata kai yayi tareda lumshe idanunsa fuskarsa d'aukeda murmushi Wanda bata ta6a ganin irinsaba daga gareshi.
   Itama mayar masa da murmushin tayi, tashare hawayenta da handky d'in.
     Gaba tayi yana binta abaya gabad'aya saiyaji tabashi tausayi Dan baiyi tunanin zatayi sanyi dawuri hakaba.
   Cak safna tatsaya tanabin mutanen Dake tsaye da kallo a harabar gidan d'aya bayan d'aya.
   Da Rahma suka fara had'a ido, tunda take bata ta6a ganin 'Yar uwarta Rahma hakaba, ta tamke mata fuska tamau kamar batasan miye dariyaba arayuwarta, juyawa tayi da kallonta ga sauran saitaga ya ishaq da matarsa ya Sulaiman da mayarsa ya Hamza da matarsa, wannan ya tabbatar mata sunfitone dazummar tafiya k'ila anata Neman bobo, gaba d'ayansu takula kallon tuhuma da tsana suke mata, k'asa tayi dakanta idonta cikeda hawaye, batason su maidata ruwa, tanason kowa ya fahimceta kuma ya k'aunaceta, juyawa tayi ta kalli bobo, shikam hankalinsa kwance yake, Dan fuskarsa da murmushi ya ce, "oh kunata jirana ko?, bara nama su Ammi Sallama mu wuce.......
     Baijira amsar kowa acikinsuba yayshige warsa falon.
    Sum sum safna itama tayi yunk'un tafiya Dan tsorata da kallon tsana dasuke mata kuma harda 'Yar uwarta a ciki, da Sauri aunty Sameera tayi yunk'urin Tarar safna amma sai Yaya ishaq yad'aga mata hannu alamar tabarta.
    Ganin haka yasaka safna saurin shigewa falon sukaci karo da bobo dake fitowa, kallonta yayi d'an murmushi ya ce, " karfa komai yadameki nida kaina zan warware musu k'ullin kinji.
   Kanta ta d'aga Dan koba komai taji sanyi tunda bobo yafara nuna mata kulawa, saida safe tafad'a a sanyaye.
    ALLAH yakaimu yay maganar yana fita, Itakuma tahaye sama zuciyarta na k'ara k'arfafata akan karta bari dalilin wasu tubanta ya ruguje.
       Koda bobo yafito saiya Tatar ya ishaq nagaya musu karkowa yatada maganar sai bayan biki, suna ganinsa kowa yagyara tsayuwarsa kamar basa maganar komai.
    Shima bai nuna musu yaji komaiba yabasu hannu sukayi musaBaha kowa yashiga motarsa, hannun Rahma Yakama saita fisge..   
     Cikin d'an mamaki yakalleta ta kauda kanta gefe, k'ara damk'ar hannunta yayi yatura amota, Duk abinda ke faruwa 'yan uwansa suna kallonsu amma babu Wanda yay yunk'urin yin magana.
    Yana turata amotar yamaida yarufe, shima yazagaya yashiga suka fice kowa Yakama hanyar gidansa.
          Tunda suka fice agidan Rahma tafara shashshekar kuka, baice da ita komaiba dukda kukan NATA na ta6a zuciyarsa, tsayawa yayi wajen wani gashin kaza yasaya sannan yadawo motar, gefen Rahma yakalla saiyaga tayi barci, girgiza kai kawai yayi yatada mortar yay gaba.
   Bayan sun gaisa da maigadi yashiga cikin gidan yay fakin Inda yadace, baitadasuba sai kawai ya d'auki Nawal yakai cikin gidan, yadawo Yakuma d'aukar Rahma, yana tafiya yana kallon fuskarta daduk yayi jurwayen hawaye, lallausan murmushi yasaki ahankali ya ce, "my Nusfulhayat sarakan kishi, Ashe kema rigimammace?,...da wannan tunanin yakaita d'aki itama, yadawo yakwashi tarkacensa yay ciki.
    Bai tadasuba amma cikin dabara yasauya musu kayansu zuwa na barci, yamik'e yanufi d'akinsa, shima wankan yayi sannan yazauna yaci naman ya k'oshi yad'ora da ruwa mai sanyi, yay hamdala ga ubangiji ya mik'e Yakoma d'akin Rahma.
      Shima gadon yahaye yakwanta a bayanta tareda rungumeta, hannu yakai danufi shafa fuskarta amma amamakisa sai yaji hawaye sha6e² wasu na korar wasu.
     Tashi yayi zaune ya kunna fitilar d'akin yana mai kallon fuskarta, yakai tsawon minti 6 ahaka, amma har sannan kukan takeyi kuma idonta arufe ruf.
   gyarama Nawal kwanciya yayi, itakuma Rahma yad'auketa cak yay waje, duk abinda yakeyi tana jinsa amma tak'iyin koda motshin kwarai.
   Koda ya direta asaman gado saiya kuma dawowa yakashema Nawal fitila yasake yimata addu'a, Yakoma Inda yabarta anan yatarar da ita, yagirgiza kai kawai yakashe fitilar tareda hayewa gadon.
      Jawota yayi jikinsa yarungume, cikin taushin murya ya ce, "my Nusfulhayat!.
    Shiru Rahma tayi kamarma batasan da wata halittaba awajen, yakira sunanta yakai so hud'u amma ko motsi batayiba, ajiyar zuciya ya sauke tareda k'ara k'ank'ameta ajikinsa yana aika mata da wasu sakwanni cikin nutsuwa da kwarewa.
    K'arfin kukan Rahma ne yak'aru, tad'an fara mutsu mutsu ganin haka sai kawai ya manne bakinsa da NATA........

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now