26

3.5K 226 1
                                    

            💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 27

Appa yatashi zaune yana murmushi, oyoyo babana nida Ammi.
   Shima bobo dariyar yakeyi, yaje dafda Appa yazauna tamkar zai shige jikinsa.
   Appa yamik'a masa hannu su gaisa, amma saiya nok'e ya ce, "ina yini Appa.
  Dariya Appa yasakeyi, mukarram bakaso musamu ladan musabahane?, mirmushi yayi batareda yace komaiba, Appa yakamo hannun bobo yahad'e danasa yana fad'in ya iyalin?.
   Suna nan lfy Appanmu, sunama gaisheku.
    Muna amsawa. yau baka je aiki bane?.
   Naje Appa, amma nataso dawurine saboda d'akko Nawal a school.
   Ok, to ina direbanta?.
   Wai bayajin dad'in jikinsa, shine nacemasa yahuta kawai.
   ALLAH yabashi lafiya to.
  Amin.
Assalamu alaikum.
   Wa'alaikisslam. Appa da bobo suka amsawa ammi sallamarta, bobo yamik'e da sauri yakar6i kayan hannun ammi, kai Amminmu da kanki?, miye amfanin wad'ancan yaran?.
   Dariya tayi tazauna, to mukarram inbanyiba wazaiyi?, hidimar mijinace fa.
   Murmushi bobo yayi, shiyyasa kullum yakeson Amminsa haryau baiga macen datakai amminsu iya tattalin mijiba, gashidai sun tsufa amma har yanzu suna tattalin junansu tamkar yara.......
   Ammi tak'atsema bobo tunani da fad'in mukarram ga abinci.
   Firgigit yadawo da kallonsa Kansu, Ammi mikikace?.
    Tunanin mi kakeyine?.
  Bai 6oye musuba yafad'a musu abinda yake tunani, Dan akwai fahimtar juna da shak'uwa tsakaninsu da iyayensu.
   Daga Ammi har Appa dariya sukayi danjin firicin bobo, ammi ta ce, "toga abinci azuba?.
   A'a ammi nima matana tacikamin ciki da girkinta mai dad'i.
      hhhhhh d'an bantan uba, ashedai gaskiyar Hamza dayace kanason matarka, babanafa akwai iya taku.
   Dariya sosai bobo da Ammi sukeyi danjin zancen Appa, appa ya ce, " naji dad'i sosai wlhy, ALLAH yak'ara Baku zaman lfy da zuri'a tagari.
   Kansa ak'asa ya ce, "amin."
   Hira sukacigaba dayi, Appa yanacin abinci, bayan ya kammala ya ce, "mukarram!.”
    Yanda Appa yakira sunan nasa yasan tabbas maganar muhimmiyace, shima cikeda girmamawa da nutsuwa ya ce, " na'am Appa.
     Appa yagyara zamansa, yanamai tsurama bobo ido, mukarram mike tsakaninka da Alh sunusi Dala?.
    Ajiyar zuciya bobo yasauke, cikin nutsuwa yayma Appa bayanin tun farkon tsintar muheebat dakuma abinda yake faruwa a yanzun.
    Appa ya girgiza kai alamar gamsuwa, ya ce, "ina alfahari daku sosai 'ya'yana, ngd ma ALLAH dayayiku masu hankali dasanin darajar d'an Adam, lallai kaburgeni sosai babana, kuma Nagoya maka baya d'ari bisa d'ari ka kwatoma yarinyar hak'k'inta, “I'm proud of you my dear son”.
     ALLAH yatsare minku aduk inda kuka tsinci kanku.
    Amin Appa mungodema ALLAH dasamunku amatsayin iyaye nagari, bamuda abin biyanku saidai muyita binku da addu'a har k'arshen numfashinmu.
   Ammi dai sai murmushin jin dad'i takeyi.
   Appa yacigaba da fad'in dama abinda yasa kaji namaka maganar yaune Alhaji Sadiq muna hira yake bani labarin furucin Alh sunusi akanka, todaya fad'i sunanka shine yagano d'aya daga cikin 'ya'yanane, shine yasameni yake gayamin nasaka ido kar a cutarmin dakai, Dan Alh sunusi bashida imani ko kad'an.
      _(nasan har yanzu baima San kai d'ana bane shiyyasa yake rangwanta maka, Dan bama shiri sosai nidashi, siyasa tasakashi d'aukar gaba damu nida Abban Ammar)_
    amma kadage da addu'a muma zamu tayaka, ALLAH yana tareda mai gsky kaji my son.
    Murmushi bobo yayi, ya ce, " karka damu Appa wlhy daidai da second 1 banta6ajin tsoro ko Shankar Alh sunusi ba, ni duk sanda yay wani abunma k'aramin k'aimi yakeyi.
    Daga Ammi har Appa dariyar sukayi, sukace to ALLAH yak'ara tsareka auta, fira sosai yasha da iyayensa, saida suka dawo daga sallar magriba sannan yay musu sallama zai tafi.
   Appa ya ce, "gobe idan ALLAH yakaimu yanason ganinsu su duka, yanaso su tattauna akan maganar auren su khursiyya.
   To Appa ALLAH yakaimu lfy.
  Amin bobon Ammi.
  Dariyar bobo yayi yafice sai gida.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
     Bayan isha'i ummi tashiga d'akin safna danganin ko lfy?, akwance take tana chart itada baseera dawasu k'awayensu a group sunata zugata akan bobo, Dan tuni sunsan labarin bobo.
   Jin motsin tahowar mutum yasata tura wayar a k'ark'ashin filo, danbata buk'atar kowa yagane halin datake ciki.
    Azaune ummi tasameta tana duba takardunta na makaranta.
   Ummi ta ce, " o aini nazatama bakida lfy ne?, kimdawo baki nemeniba bare naji labarin autana.
   'Yar dariyar basarwa safna tayi, lah ummi wlhy fitsarine yakoroni shiyyasa banshigoba, daga baya kuma namak'ale ad'aki dankarki lik'amin girki.
    Dariyar ummi tayi, ta ce, "malalaciyar banza, ke koma auren akai miki yanzu aii mijin yabani, babu abinda kika iya sai kwalliya.
   Safna ta ce, " kai ummi, aidai nasan Kodan k'yawuna mijin ya zauna dani.
   Baki ummi ta ta6e ta ce, "keni rabani da shiriritarki Yakika ganomin autata?.
   Tana nan tak'ara k'iba, cewar Safna tana ta6e baki.
   Alhmdllh ummi tafad'a cikeda jin dad'i, ALLAH yak'ara baku zaman lfy autana, har hankalina ya kwanta aii wlhy.
    Itadai safna batace komaiba har ummi tafice.
Raka ummi tayi da harara kamar ba uwartaba.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now