25

3.4K 198 2
                                    

              💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 26

Rahma tarungume Safna cikeda farinciki, itama rungumeta tayi Dan tayi kewar 'Yar k'anwarta abokiyar fad'anta, I miss you my lovely aunty.
    Miss u too my lili na.
     Safna tad'agota daga jikinta tana fad'in 'Yar lukutar ummi kinfa k'ara lukucewa, mi angon naki yake baki haka?.
    Rahma tarufe fuskarta saboda jin kunya, kai aunty Dan ALLAH ki bari.
   To na bari Safna tafad'a tana kama hannunta sukai cikin falon.
    Rahma ta kalli mazaunin Bobo wayam, Nawal ta kalla data maida hankalin akan game, baby ina papa?.
    Nawal tad'ago tana dariya, yashiga d'akinsa momy..... Tsayawa tayi tana kallon Safna, saikuma ta kalli Rahma, momy wacece wannan?.
    Aunty ce babyna.
Nawal ta taso ta rungume Safna, oyoyo aunty na.
   Itama safna rungumeta tayi tana fad'in oyoyo babyn mom.
   Bayan  sun zauna Safna sai bin Nawal da kallo takeyi, gani take kamar tasan yarinyar.
   Rahma tadire tiren kayan motsa baki agaban safna, tana fad'in wlhy aunty banyi zaton ganinkibafa.
   'Yar dariya safna tayi ta ce, ''saikuma gani kin ganni.
  Zama tayi sukafara hira, kamar basu bane sukeshan fad'a ada.
    Sun shagala sosai akan firar idon Safna ya sauka akan hoton Bobo, wani k'ululu cikinta yabada, batagama dawowa daidaiba Bobo yafito daga d'akinsa.
   Ah bak'uwa mukayi agidan??.
  
Afirgice safna tad'ago tana kallonsa, fad'uwar gaba, bugun zuciya, murd'awar ciki, duk suka k'ara samunta alokaci guda, yanda take raba ido akan Bobo sai kawai ya d'aure fuska.
   Itama Rahma kallonta takeyi ita atunaninta Safna taji kunyane akan abinda ta aikata abaya.
      Safna taduk'e k'anta bisa cinyarta danjin falon yana juya mata, jikinta sai rawa yakeyi, lallai ta tabbata kuka rahamane tunda gashi ita yau takasayinsa.
   Bobo yana zaune saman kujera yad'ora k'afa d'aya kan d'aya, dagashi har Rahma idanunsu nakan Safna, Nawal ma tana mak'ale abayan Rahma tana lek'en Safna, bobo yakalli Rahma, dama tanada wani ciwone?.
   Kai Rahma ta girgiza masa ta CE, ''amma dai ban saniba ko bayan nabar gidan.
   Lumshe idanunsa yayi ya ce, "bata ruwa tasha, Rahma ta tsiyayama Safna ruwa a Kofi tabata, jikin Safna na Rawa takar6a ta shanye duka tamik'ama Rahma kofin, k'ara mata bobo yasake fad'a.
  K'ara mata takumayi, aii ko ta shanyeshi tas.
   Rahma takalli Safna kamar zatayi kuka, aunty ki kwanta kihuta, kiringa fad'in _innalillahi wa'inna ilaihirraji'un_ zaki samu nutsuwa insha ALLAHU.
    BABU musu Safna tabi shawarar Rahma ta kwanta, dukda ayanzu jitake babu Wanda tatsana aduniya sama da Rahma d'in, jitake tamkar tatashi ta shak'eta ta mutu, talumshe idanu tana ambatar innalillahi..... Danjin zuciyarta tana shirin fashewa.

Bobo dai tuni yad'auke kai daga kallon Safna, ya maida hankalinsa ga TV.
    Bayan kamar minti15 Safna tad'anji Nutsuwa tazo mata, tabud'e ido tareda tashi.
   Rahma tai saurin fad'in aunty Yaya jikin?.
    Murmushi Safna tayi Wanda yafi kuka ciwo, da sauk'i kuyi hak'uri na rud'aku, juwace nakeji dama tun ina hanya.
    Sannu Rahma tashiga jero mata, Dan ita tayarda da zancen na Safna 100%.
        Bobo kam azuciyarsa ya ce, " juwar kuma bata tashiba saida kika ganni?, shifa Sam bai yarda da maganartaba, Dan haka yacigaba da kallonsa batareda yak'ara kallon ko inda sukeba.
    Safna kam tafad'i hakane saboda tunowa da maganar malaminta, dayace kota had'uda bobo karta nuna masa komai harsaitaje wajensa yabata wani sirri, da wannan tunanin tad'anji sanyi aranta, shiyyasa ta tashi ta zabga wannan k'aryar.
   Takai kallonta ga bobo daya maida hankali kan latsa wayarsa, muryarta na rawa ta ce, "ina yini.
   Lfy, kawai ya ce, " yamaida Kansa ga waya.

Falon yay shiru nawasu 'yan mintuna, safna dai satar kallon Bobo takeyi, sai yanzu yak'ara tabbatarwa da k'yak'yk'yawane ajin farko, Ashe ranar kallon tsoro sukayi masa, lallai ALLAH yayi halitta awajennan masha ALLAH, sai sambatun k'yawun bobo takeyi ita kad'ai zuciyarta.
        Rahma kam tayi shiru tana tunanin halin da safna tashiga yanzun nan, kome ke damun 'Yar uwar tata?.
         Bobo yamik'e Dan ganin kallon k'urillar da safna take masa, yakalli Rahma bara nad'an kwanta kafin sallar la'asar, kitadani idan lokaci yayi.
   To. Rahman tafad'a kanta ak'asa.
   Shikuma yanufi d'akinsa, harya shige safna tanabinsa da kallo.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum