*HUKUNCIN WANDA YA RISKI ZAMAN TAHIYA A SALLAR JUMA'AH

322 5 3
                                    

*HUKUNCIN WANDA YA RISKI ZAMAN TAHIYA A SALLAR JUMA'AH ?*

*Tambaya*

Assalamu Alaikum Malam, nine nazo juma'a a makare sai natararda zaman tahiyya, shin in imam ya sallame raka'o'i 2 zanyi ko 4❓

*Amsa:*

Akwai fahimta guda 2 akan haka,
   Nafarko= Mazhabin IMAM ABU HANIFA da IBNU HAZMIZ ZAHIR- suna ganin in har yasami imam kafin yayi sallama koda a tahiyyane to raka'o'i 2 na juma'a zai kawo, HUJJARSU akan haka shine Hadisin ABU HURAIRA R/A👉🏼
٤٨- [عن أبي هريرة:] إِذا أُقِيمَتِ الصَّلاةُ، فلا تَأْتُوها تَسْعَوْنَ، وأْتُوها تَمْشُونَ، عَلَيْكُمُ السَّكِينَةُ، فَما أدْرَكْتُمْ فَصَلُّوا، وما فاتَكُمْ فأتِمُّوا.
البخاري (٢٥٦ هـ)، صحيح البخاري ٩٠٨  •  [صحيح]  •  أخرجه البخاري (٩٠٨)، ومسلم (٦٠٢)  •
Wato= "abinda kuka tarar kusallata abinda yasubuce muku kuma kuma kuciko" sukace ai abinda yakubce raka'o'i 2 ne don haka su za'a kawo,
   NABIYU= JAMHURIN MALAMAI kuma sun tafi akan tunda bai samu ruku'i sai tahiya to bai sami raka'a ko dayaba, don haka bai sami juma'aba, don haka raka'o'i 4 na azahar zai kawo, HUJJARSU shine Hadisin ABU HURAIRA👉🏼
٧- [عن أبي هريرة:] أنَّ رَسولَ اللَّهِ ﷺ قالَ: مَن أَدْرَكَ رَكْعَةً مِنَ الصَّلاةِ، فقَدْ أَدْرَكَ الصَّلاةَ.
البخاري (٢٥٦ هـ)، صحيح البخاري ٥٨٠  •  [صحيح]  • 
Lafazin MUSLIM kuma👉🏼
[عن أبي هريرة:] مَن أدْرَكَ رَكْعَةً مِنَ الصَّلاةِ مع الإمامِ، فقَدْ أدْرَكَ الصَّلاةَ.
مسلم (٢٦١ هـ)، صحيح مسلم ٦٠٧  •  [صحيح]  •  أخرجه البخاري (٥٨٠)، ومسلم (٦٠٧)  • 
Wato= "wanda yatararda raka'a daya tareda imam to yatararda sallan"
KISHIYAR FAHIMTAR  (مفهوم المخالفة) na hadisinnan shine👉🏼
ومن لم يدرك ركعة من الصلاة لم يدرك الصلاة
Wato= Wanda bai tararda raka'a ko dayaba to bai sami sallanba, tunda bai samu juma'arba to azahar zaiyi wato raka'o'i 4,
   Yayinda shi kuma ABU HANIFAH bai yarda da MAFHUMUL MUKHALAFAH ba,
   SHEIKH MUHD IBN ABDIL-MAQSUD ya rinjayarda maganar jamhuran Malamai nabiyan raka'o'i 4 na azahar tunda bai sami juma'a ba,
ALLAHU A'ALAM.

*via : Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽*
20/Al-muharram/1441
  20/September/2019

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 21, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now