*HUKUNCIN ƁOYE KAYAN KASUWANCI HAR ZUWA LOKACIN TSADARSA

79 1 0
                                    

*045 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*HUKUNCIN ƁOYE KAYAN KASUWANCI HAR ZUWA LOKACIN TSADARSA*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Shin ya halatta mutum ya sari kaya lokacin da take araha idan ya yi tsada ya fitar ya saida dan ya samu riba?

AMSA:

Wa'alaikumus Salam. Mutum ya Saye kaya ya ɓoye shi sai bayan wani lokaci ya yi tsada ya fito da shi don ya gallazawa al'umma, wannan shi ne malamai suke kira IHTIKAR, KO BAI'UL MUHTAKIR, wannan aiki haramun ne babu ko shakka, Sahabin Annabi s.a.w mai suna Ma'amar ya ruwaito hadisi cewa:
Annabi s.a.w ya ce: "Duk wanda ya yi ihtikari (ɓoye kaya har sai ya yi tsada) mai saɓo ne". A wani lafazin kuma ya ce: "Babu mai yin ihtikari sai mai saɓo".
Duba Muslim 1605.

Lallai bai halasta mutum ya saye kayan abinci da makamantansu da nufin ɓoye shi har zuwa lokacin da mutane suke tsananin buqatarsa, sannan ya fito da shi ya gallaza ma jama'a ba.

Amma wanda ya sayi kaya ko ya yi noma sai a lokacin kayan ya yawaita a kasuwa ta yadda ko ya fitar da kayan ba zai sami riba ba, sai ya bari har zuwa lokacin da farashi zai ɗan matsa gaba, to wannan babu laifi matuqar ba zai cutar da kowa ba.
Duba Alminhaaj: Sharhun Nawawiy Ala Muslim 6/42.
Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
25/5/1440 h.
31/01/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now