*MUN CI BASHIN KUDIN BIKI NI DA MIJINA, WA YA DACE YA BIYA

115 5 0
                                    

*177 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*MUN CI BASHIN KUDIN BIKI NI DA MIJINA, WA YA DACE YA BIYA?*

TAMBAYA:

Assalamu Alaikum, Malam ina da tambaya; wani ne ya nemi budurwa aka sa masu ranar aure, da auren ya zo sai ya kasance sun yi rigima da wani a kan kasuwancinsa, har aka rufe shi a gidan yari, iyayensa ba su bari an daga bikin ba, suka ce a fara za a yi belin din sa kafin ranar daurin aure, to sai ya yi wa amaryarsa waya a kan cewar tun da ya kama za a yi biki ba shi nan to ta ranci kudi ko ma a ina ne dubu N150,000 ta yi duk abin da suke bukata na walima kunshi da sauransu, da niyyar zai biya bayan bikin, to malam har ya fito aka yi biki, sai Allah yasa kafin ya biya mutanen sai suka rabu da matar, kuma ba a biya kudin nan ba, malam menene hukuncin wannan bashin, shin ita ce za ta biya ko mijin nata? Saboda bayan mutuwar auren mijin nata ya ce shi wallahi ba zai biya ba, ita za ta nema ta biya tun da sun rabu.

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu, ƴar uwa a zahirin abin da ya bayyana a gare mu in dai wannna maganar haka suka yi ta, to mijin nata shi ne ya kamata ya ɗauki nauyin biyan wannan kuɗi, saboda shi ne ya ba da umurnin a ciwo wannan bashi, kuma ya ɗauki nauyin cewa zai biya idan ya fito gidan kurkuku, sai dai mu a nan ba mu isa mu ce lallai-lallai hakan za a yi ba, wannan matsalar magabatansu ne ya kamata su zauna don a warware matsalar, idan kuma duk ya gagara sai a garzaya kotu, shi Alqali zai bayyana wanda ya wajaba a kansa ya biya wannan kuɗi a tsakanin su biyun, wannan ita ce magana ta gaskiya.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu zarewa.*
11/11/1440 h.
14/07/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now