Malm yanxu idan mutum yana karatun alqur ani acikin xuciyarsa xaisamu ladan kawo

251 0 0
                                    

السلام عليكم يامعلم

*TAMBAYA*

Malm yanxu idan mutum yana karatun alqur ani acikin xuciyarsa xaisamu ladan kawo ne harafine? Kokuma sai yayi a bayyane ne?

*AMMSA*

Hakika Ambaton Allah yana daga cikin mafi girman aikin  musulmi, kuma baya takaituwa dayi da harshe kawai, bal za'a iya yinsa da zuciya ko gabobi.

idan aka saki Kalmar zikiri to ta kunshi duk wani abu da bawa zai nemi kusanci zuwa ga Allah dashi na Akida, tunani, aiyukan zuciya, aikin gabobi, yabon Allah, koyon ilimi da koyar dashi, da sauran su.

Amma asalin zikiri hakan fara daga zuciya Kamar yanda Manzon Allah sallalahu alaihi wasallam yake cewa: " ku saurara, Hakika cikin jiki akwai wata tsoka idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, kuma idan ta baci dukkan jiki ya baci, Ku saurara itace zuciya"

رواه البخاري ومسلم

Don haka zikiri yana kaikomo ne gaba daya bisa zuciya, sabida fadin Allah Jalla wa ALÁ :

وَلَا تُطِعْ مَنْ أَغْفَلْنَا قَلْبَهُ عَن ذِكْرِنَا وَاتَّبَعَ هَوَاهُ

Kuma kada ka bi wanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga ambatonMu, kuma ya bi son zuciyarsa..

Don haka idan mutum ya ambaci Allah da harshensa ko gabobinsa ba tare da ambatonsa a zuciya ba, wannan ambatone tauyayye Kamar gangar jikine da bashi da rai.

Siffar ambaton Allah da zuciya ya kunshi : yin tunani cikin ayoyin Allah, son Allah, girmama shi, mayar da al'amari gareshi, jin tsoronsa, dogaro gareshi, da sauran su.

Ambaton Allah da gabobi ya kunshi : yin sallah, ruku'u, sujjada, jihadi, zakka, da sauransu.
Matukar anyisu da nufin yiwa Allah biyayya Allah Taala yana cewa :

إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَىٰ عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنكَرِ وَلَذِكْرُ اللَّهِ أَكْبَرُ

kuma ka tsayar da sallah.
Lalle salla tanã hanãwa daga alfãsha da abin ƙyama, kuma lalle ambaton Allah ya fi girma.
Wasu cikin malamai sukace : domin abinda sallah ta kunsa na ambaton Allah mai girma.

Ambaton Allah da harshe ya hada da karatun kur'ani da sauran zikirai Kamar : tasbihi, tahmidi, hailala, ziran safe da yamma, dana kwanciya bacci da shiga bandaki.
Irin wannan nau'in na zikiri babu makawa sai an motsa harshe gurin yinsa, kuma koda mutum yayisu idan bai motsa harshensa ba ba za'a lissafamasa yinsu ba har sai ya motsa harshensa.

Ibn Rushdin ya nakalto daga Imamu Malik an tambaye shi matsayin mutumin da yake karatu a cikin sallah ba'a jin muryarsa kuma baya jiyar da kansa, kuma baya motsa harshensa gurin karatun. Sai yace: " wannan ba karatu yake ba, sanu dai kadai karatu shine Wanda aka motsa harshe gurin yinsa".

البيان والتحصيل 1/490

Malam Kásániy yace : " karatu baya kasancewa sai da motsa harshe da haruffa, bakaga mai sallah Wanda yake da ikon yin karatu idan bai motsa harshensa ba sallarsa bata yiba. Hakama idan yayi rantsuwa bazai karanta koda sura guda ba cikin kur'ani sai ya kalli cikin kur'ani kuma ya fahimci abinda ya kalla rantsuwar bata hau kansa ba".
بدائع الصانع 4/118

An tambayi sheikh Usaimin kan wajabcin furta karatu cikin sallah?

Sai yace : babu makawa sai anyi karatu ta hanyar furtashi, idan mutum yayi karatu da zuciyarsa a cikin sallah karatun bai wadatar dashi ba, hakama sauran zikirai, yinsu a zuciya baya wadatarwa, babu makawa sai an furtasu da harshe da lebuna, domin su zance ne, shi kuma baya tabbatuwa sai da motsa harshe da lebe".

مجموع الفتوى ابن عثيمين 13/156

Don haka yin karatu ta hanyar kallo ba tare da motsa harshe ba ba'a daukarsa matsayin karatu, kuma ba'a bada sakamakon da ake bawa masu yin karatu akansa, wannan kawai yana tsaya wa matsayin tuntun tuni ne cikin kur'ani, kuma za'a bashi lada kan haka.

Sheikhul Islam Ibn taimiyya rahimahullah yace : " mutane sunada mataki gudu hudu gurin ambaton Allah :
Na farko : mai yin ambaton Allah da zuciya hade da harshe wannan shine Wanda akayi umarni dashi.
Na biyu : ambaton Allah da zuciya kadai, idan ba za'a iyayi da harshe ba to yayi, amma idan za'a iya barin yi da zuciya ita kadai shi yafi.
Na uku : ambaton Allah da harshe kawai, shine harshe ya zamo danye shakaf wajen ambaton Allah.
Na hudu : rashin yin kowanne daga ciki wannan shine halin tababbu.

مجموع الفتوى 10/566

Don haka abin da akeyi abune mai kyau, amma abinda yafi shine a dinga hadawa da furucin, da tun tun tunin zuciya, ba dole sai an daga murya sosai ba, kawai motsa bakin da murya kadan yayi, sabida haka a dage wajen yin hakan Don a sami lada mai girma.

Wallahu Aalamu

Allah ne mafi sani.

*✍📚Shashen fatawa a bisa Qur'ani, Sunnah da maganganun magabata na ƙwarai (sawtul hikmah)*

18/1/1400.
17/09/2019.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now