AMSOSHIN TAMBAYOYINKU

770 13 0
                                    

*_INA FAMA DA CIWON KODA, ZAN IYA CIYARWA A MAIMAKON AZUMI?_*

                       *Tambaya*
Asalamu Alaikum malamai na inada tambaya macece bata da lafiya na ciwon koda yafara zama kuronik sai satinnan likitoci suka bata shawara duk bayan minti Talatin taci wani Abu daga Abinci kartakoshi to malam yaya za'a billowa maganar Azumi ciyarwa za'a cigaba da yi ko jira za'a yi sai ta warke ta rama ?

                           *Amsa*
Wa'alaikum assalam, in har tana tunanin samun sauki kafin wani azumin ya zo, ba za ta ciyar ba, za ta bari ta rama bayan ta samu dama, saboda aya ta: 184 a suratul Bakara ta nuna cewa: wajibin mara lafiya shi ne rama azumin da bai yi ba na Ramadhana bayan ya samu dama a wasu kwanakin.
Mutukar likitoci sun tabbatar ba za ta samu saukin da za ta rama azumi daga baya ba, ya halatta ta ciyar a maimakon kowacce rana.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

_*سبحانك اللهم وبحمدك اشهد ان لااله الا انت استغفرك واتوب اليك*_

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now