*YA HUKUNCIN MAI KARBO KAYAN ABINCIN MARAYU DA ƳAN GUDUN HIJIRA ALHALI BA SHI A

138 1 0
                                    

*187 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YA HUKUNCIN MAI KARBO KAYAN ABINCIN MARAYU DA ƳAN GUDUN HIJIRA ALHALI BA SHI A CIKINSU?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum warahamatullah, malam dan Allah mene ne hukuncin mutumin da yake zuwa gari gari yana amso abinci da kayan sawa a wajen hukuman taimakon marayu da 'yan gudun hijira, kuma in ya amso sai dai ya siyar ya ci kudin, to malam ya ci halak? Na gode Allah ya ba da ikon amsawa.

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu Wa Rahmatullah, duk mutumin da ke zuwa ya karɓo kayan abincin ƴan gudun hijira, da kayan sawan da aka tattala don a tallafa masu, to ya ci haramun matuqar shi ba maraya ɗin ba ne, ba kuma ɗan gudun hijira ba ne, kuma wannan aiki ha'inci ne, sannan cin dukiyar bayin Allah ne ta hanyar ɓarna. Saboda ba shi a cikin ahlin dukiyar, ba shi da haqqi ko na sisin kwabo a ciki.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
20/11/1440 h.
23/07/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now