*TA YAYA ZAN TATTALI MIJINA?*

195 5 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*TA YAYA ZAN TATTALI MIJINA?*

*TAMBAYA:*
Assalamu Alaikum, tambayata a nan ita ce malam a yi min karin bayani a kan yadda ake tattalin miji?

*AMSA:*
Wa'alaikumus Salamu, ƴar uwa mace za ta iya tattalin mijinta cikin sauqi idan ta cire girman kai da ganin isa, sannan kuma ta sa haquri tare da yawaita addu'a. Sai dai kamar yadda maza suke da haqqi a kan matansu, to haka su ma matan suna da haqqi a kan mazajensu, kamar yadda aya ta 227 ta cikin suratul Baqara ta bayyana.
Sai dai a nan za a dubi yadda mace za ta yi tattalin mijinta ne kamar yadda mai tambaya ta nema. Daga cikin dabarun da mace za ta bi don ta tattali mijinta sun haɗa da:

1. Nuna masa soyayya a zahiri da ɓoye, da bin umurnin da duk ya yi mata wanda bai saɓa wa shari'a ba, da yin haquri da talaucinsa idan ya kasance talaka ne, da riqe masa sirrinsa musamman akan wani aibi da yake da shi, da yin shiru a lokacin da ya fusata har sai ya sauko, da yi masa magana cikin tausasawa da rarrashi.

2. Yi wa miji kwalliya, da yawan yin tsafta ba tare da zama da qazanta ba, da yi wa miji murmushi da sakin fuska, da yin tarayya da shi a lokacin da yake cikin farin ciki ko baqin ciki, da amsa masa kira a duk lokacin da ya kiraki, da rashin aikata abin da zai fusata shi.

3. Ki guje wa rashin godiya a kan abun da yake maki na kyautatawa komai qanqantarsa, da gujewa yawan kai masa qara ko na wane ne, da gujewa kai shi qara a wajen iyayenki har sai in abin ya zama dole sai an yi hakan, kada ki riqa yi masa alfahari da tinqaho da kyawonki.

4. Ki riqa ganin girman mijinki, saboda miji yana da haqqi mai girma a kan matarsa, saboda girman haqqin miji a kan matarsa, Annabi ﷺ ya ce: "Matar mutum ba ta taɓa cutar da shi a nan duniya, face sai matarsa daga cikin matan Aljannah ta ce: "Ki daina cutar da shi, Allah ya tsine maki, shi fa baqo ne a wurinki, ya kusa ya rabu da ke zuwa wurinmu"". Ibn Majah 1857.

5. Ki riqa neman yardar mijinki, ki taimaka masa wajen neman halal, kada ki zama marowaciya ga ƴan uwan miji, da sauran mutan gida, ki zamo mai taimaka masa wajen yi wa Allah ɗa'a a duk abin da ya umurce shi da abin da Allah ya hane shi, kada ki riqa tuna masa kirkin mijinki na farko idan ke bazawara ce a wurinsa, kada ki fita gida sai da izininsa, kada ki tambaye shi zuwa unguwa ki haɗa da zuwa inda ba ki tambaye shi ba, kuma ki daina yawan fita unguwa in bai zama dole ba.

6. Kada wani ya shigo gidan mijinki sai da izininsa, ki yi qoqari wajen neman ilimi da aiki da shi, ki riqa damuwa da kula da mijinki da ƴaƴansa har wanda ba ke kika haifa ba, kada ki riqa bijiro da saɓani a gaban yara. Ina kashedinki da yawan tsaftace gidanki.

7. Ki riqa girmama iyayen mijinki, musamman mahaifiyarsa ko da tana cutar da ke, da sauran ƴan uwnsa da abokanninsa, da sauran duk masu alaqa da shi. Da kuma kawar da kai ga saɓanin da bai taka kara ya karya ba. Ki guje wa duk qawar da take ba ki shawarar ɗaukar fansa akan saɓa maki da aka yi.

8. Ki riqa amsa kiransa a duk lokacin da ya buqace  ki zuwa shimfiɗa, ki guji yaɗa labarin yadda kuke jima'i ga qawayenki. Ki guji kaɗaita da namijin da ba muharraminki ba.

Waɗannan kaɗan ne daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata mace ta kiyaye su don ta tattali mijinta, in Allah ya so duk matar da ta kiyaye waɗannan abubuwa za ta zauna lafiya da mijinta.

Domin neman qarin bayani sai a duba littafin Muhammad Siddeeq Alminsháwiy mai suna: FANNUT TA'ÁMULI BAINAZ ZAUJANI shafi na 59 zuwa na 125.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
26/6/1440 h.
03/03/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now