*BAYANI A KAN SALATUT TASBIHI

496 0 0
                                    

*201 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*BAYANI A KAN SALATUT TASBIHI*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Malam Ina son in san yadda ake salatut tasbihi.

AMSA:

Wa'alaikumus salam, ƴar uwa kafin a kai ga miki bayani a kan Salatut Tasbihi, yana da kyau ki sani cewa hadisin da aka ruwaito wannan sallah ta Tasbihi a cikinsa malamai sun rabu gida biyu dangane da ingancin hadisin, daga cikin malamai na da da na yanzu akwai waɗanda suka raunana hadisin, har ma wasu suna ganinsa a matsayin hadisi ne qirqirarre. Amma wasu malam kuma sun inganta shi, suna ganin ba shi da wata illa, duka dai al'amari ne na ijtihadi, babu buqatar tsawaita kawo maganganunsu a nan saboda taqaita rubutu.

Yadda ake yin Salatut Tasbihi kamar yadda ruwayar Abu Dáwud ta bayyana shi ne kamar haka:

Sallah ce mai raka'o'i huɗu, za a karanta Fatiha da Sura a kowace raka'a, idan aka gama karatun a raka'a ta farko sai a cigaba da tsayuwa a karanta wannan: "Subhaánallah, Walhamdulillah, Walá'ilaha Illallah, Wallahu Akbar" sau goma sha biyar (15), sannan sai a yi ruku'u, sannan a sake karanta ta sau goma (10) a ruku'u, sai a ɗago daga ruku'u a sake karanta ta sau goma (10), daga nan sai a sunkuya zuwa sujjada a sake karanta ta sau goma (10), sannan a ɗago daga sujjada a karanta ta sau goma (10), sai a sake kumawa zuwa sujjada a sake karanta ta sau goma (10), sannan ya ɗago daga sujjada a sake karanta ta sau goma (10) kafin a tafi raka'a ta gaba. idan aka haɗa lissafi ya zama guda saba'in da biyar (75) kenan, haka ake yi a kowace raka'a.
Duba Abu Dáwud hadisi mai lamba ta: 1297.

Wannan ita ce kaifiyyar Salatut Tasbihi, sai dai kada a manta tun a farko an bayyana cewa malamai sun rabu gida biyu dangane da hukuncin hadisin, akwai masu ganin hadisin ya inganta, da kuma waɗanda suke da fahimtar bai inganta ba, sai dai ni a qaramin fahimtata na fi natsuwa da fahimtar malaman da suke da fahimtar rashin ingancin hadisin.

Don neman qarin bayani sai a duba AMUGNIY (2/98), da MAJMÚ'UL FATAÁWÁ (11/579), da kuma ALMAJMÚ'U (3/54).

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
5/12/1440 h.
06/08/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now