*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

607 7 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YA HUKUNCIN JININ DA KE ZUBO WA MACEN DA TAKE TSARIN IYALI (PLANNING)?*

TAMBAYA:

Assalamu Alaikum, malam don Allah tambayata ita ce; macen da take tsarin iyali (planing)sai jini yana zuwa mata ko wani lokaci, ko kuma yana mata wasa, ya matsayin sallan ta? Kuma za ta iya hada shimfida dame gida? Allah ya taimaka ya kara mana basira baki daya. Nagode.

AMSA:

Wa'alaikumus Salam, An tambayi Majalisar malamai masu ba da fatawa na qasar Sa'udiyya game da macen da jini ke zuwa mata a kowane lokaci saboda tsarin iyali (planning) da take yi, ko kuma yake mata wasa lokaci bayan lokaci sai suka ba da amsa da cewa:

"Idan ya kasance jinin da yake zuwa mata bayan ta yi amfani da abin da ake palanning ɗin da shi jinin al'ada ce sananne ga mace, to za a ɗauke shi ne a matsayin jinin haila, za ta daina yin azumi da sallah, amma idan ya kasance ba jinin haila ba ne, to ba za a hukunta shi a matsayin jinin haila wanda ke hana yin azumi da sallah da jima'i ba, saboda shi wannan jini yana sauka ne saboda wannan abin hana haihuwa da aka yi amfani da shi". 
Duba Fatáwál Lajnatid Dá'ima 5/443.

Wato wannan na nufin duk macen da ke amfani da magungunan hana ɗaukar ciki sai hakan ya sa jini ke zuwa mata ba a lokacin al'adarta ba, to duk lokacin da jinin ya zo mata sai ta duba launinsa da duk yanayinsa, da zarar ta ga ya yi daidai da irin jinin hailarta, to za ta hukunta shi ne a matsayin jini ne na haila, idan kuma ta ga bai yi kama da jinin al'adarta ba, to ba za ta hukunta shi a matsayin jinin haila ba, za ta ci gaba da yin ibadarta kamar yadda ta saba, har ma mijinta na iya kusantarta.

Amma wasu malaman kuma suna ganin kawai idan jinin ya zo mata, to ta qidaya iya adadin kwanakin da take haila, da zarar sun cika shi kenan hailarta ta qare ko da jinin bai tsaya ba, sai ta yi tsarki ta ci gaba da ibada. Wasu kuma suna ganin za ta bari ne ta gani har jinin ya cika kwana goma sha biyar, daga nan shi kenan sai ta yi tsarki ta ci gaba da ibada, idan kuma ya dakata da zuwa kafin kwana sha biyar su cika shi kenan sai ta yi tsarki ta ci gaba da ibadarta.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
17/7/1440 h.
24/03/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now