*NA FARA YIN SAHUR SAI NA JI ANA TADA SALLAH, SHIN YA HUKUNCIN AZUMINA?*

206 0 0
                                    

*NA FARA YIN SAHUR SAI NA JI ANA TADA SALLAH, SHIN YA HUKUNCIN AZUMINA?*

*Tambaya:*

Assalamu Alaikum Warahmatullah

Afwan don Allah tambaya gareni👏🏽

Watace tayi niyyan azumin nafila Sai ta makara qarfe 5:00 daidai ta farka Sai tasha tea Amman a lokacin bataji qiran sallah ba tana cikin Sha Sai taji qiran tada sallah shin zata iya yin azumin ko zata ajiye?

Wassalamu Alaikum.

Maman Abdurrahman Gombe.

*Amsa:*
Wa Alaykumus Salam wa Rahmatullah wa Barakaatuh.

Idan ya tabbata cewa ta farka barci karfe biyar na safe kuma ta san haka, ni ina fahimtar ta sha tea ne da gangar saboda wadanda ke rayuwa a Gombe sun san cewa alfijir na fitowa daga 4:47-4:50 sabanin nan Zaria. Kenan wadda ta farka daga barci 5:00, ta san an kira sallar Asuba, jiran liman kawai ake yi don tayar da sallah.

Idan kuwa tana rayuwa ne a kauye inda ba a cika kiran sallah da wuri ba, har sai ta nuna, kuma ita ba ta da masaniya game da yadda lokutan sallah ke canzawa, kuma ba ganganci cikin lamarin,  ina fahimtar za ta iya cigaba da azumi bisa ka"idar:

*"القدرة مناط التكليف".*

Maganar cewa ba ta ji kiran salla ba, ba zai zama hujja ba, matukar ta tabbatar da alfijir ya fito a lokacin da ta farka barci.

Wallahu A'alam

*Amsawar: ✍*
*Sheikh Prof. Ahmad Bello Dogarawa Hafizahullah*
7th Dhul Hijjah, 1440H.
{08/08/2019}

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now