*SHIN RIBÁ YANA DA IYAKA SANANNE A KASUWANCI?*

79 1 0
                                    

*046 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*SHIN RIBÁ YANA DA IYAKA SANANNE A KASUWANCI?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Gafatta malam ni ne na siya kaya naira dari (N100), sai na siyar naira dari biyu (N200), shin na ci haram ne?

AMSA:

Wa'alaikumus Salam. Lallai ɗan uwa ba haramun ka ci ba, saboda babu wani dalili a littafin Allah ko a sunnar Manzon Allah s.a.w. ko a ijmá'in malamai da ya iyakance iya riba a kasuwanci. Sai dai fa hakan bai zama hujja na gallazawa bayin Allah farashin kayayyaki ba, saboda Allah na sa wa kasuwanci albarka matuqar an sauqaqa, kuma an yi gaskiya.

Kawai dai a tabbatar mai sayen kaya ya san qimar kayan da zai saya, bai jahilci kayan ba, saboda wani akan buga masa tsada ne ta hanyar la'akari da bai da ilimin wannan abu da zai siya, Allah ya shiryar da mu.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
25/5/1440 h.
31/01/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now