*YA HUKUNCIN MIJI MAI YAWAN RANTSUWAR ZAI YI SAKI*

162 2 0
                                    

*179 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YA HUKUNCIN MIJI MAI YAWAN RANTSUWAR ZAI YI SAKI*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum, barka da warhaka malam, Don Allah ya namijin da duk abin da ya hada shi da iyalinsa, sai ya dunga ikirarin zan iya sakin ki wallahi, kuma ba daya ba, zan iya sakin ki uku? Allah ya kara maka daukaka.

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu, mijin da ke ce wa matarsa zai iya sakin ta ba za a ce ya yi wani laifi ba idan ya kasance wacce ba ta jin nasiha ce har sai ya haɗa mata da tsoratarwar sakin, wata qil hakan ne kaɗai kan sa ta natsu idan ya hana ta yin wani abin ta qi hanuwa. Kuma wannan magana tasa ba saki ba ne.

Sai dai bai dace mutum ya zama duk abin da matarsa ta yi masa babba da qarami ya riqa mata barazanar saki ba, saboda wani abin bai kai girman da za a yi barazanar saki ba. Haka nan bai dace yawan yin rantsuwa a duk lokacin da zai faɗi kalmar ba, sai dai faɗakar da mace da kalmar saki a inda aka buqaci hakan ba laifi ba ne kamar yadda ya gabata.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu zarewa.*
12/11/1440 h.
15/07/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now