*AZUMI NAWA AKE YI A WATAN MUHARRAM

100 2 1
                                    

*AZUMI NAWA AKE YI A WATAN MUHARRAM?*

*Tambaya:*

Assalamu alaikum Don Allah malam azumi nawa akeyi a wannan watan ?

*Amsa:*

Wa alaikum assalam To 'yar'uwa ana so mutum ya zage dantse wajan yin Azumi a wannan watan, saboda fadin Annabi (SAW) : "Mafificin Azumi bayan Ramadhana shi ne Azumi  a watan Muharram" kamar yadda Muslim ya rawaito

Amma Wanda ya fi muhimmanci shi ne na ranar goma ga wata, sai kuma na ranar tara, Annabi S.A.W yana cewa: "Azumin ranar goma ga wata yana kankakare zunubin shekara daya" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (1162), sannan yana cewa: "Idan na rayu zuwa badi zan azumci ranar ranar tara ga MUHARRAM".

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
31/08/2019.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now