*MAS'ALA A KAN JANABA:*

128 1 0
                                    

*TAMBAYA TA 024*

*MAS’ALA A KAN JANABA:*

_Assalamu Alaikum._

Mlm tambayata ita ce: Idan miji ya yi amfani da matarsa ta cinyoyinta da matse-matsinta amma bai shiga cikin gabanta ba. Shi ya gamsu ta hakan amma ita babu abin da ta ji, kuma ba ta fitar da maniyyi ba, to wanka ya wajaba a kanta?

Allaah ya saka wa malam da alhairi.

*AMSA A024:*

_W alkm slm w rhmtul Laah._

Al-Imaam Muslim ya fitar da Hadisi cewa: Lokacin da aka saukar da wannan ayar:

وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ قُلْ هُوَ أَذًى ، فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ
Kuma suna tambayarka game da haila, ka ce: Shi ƙazanta ne! Sai ku nisanci mata a wurin haila _(Surah Al-Baqarah: 222)._

Sai Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce:

اصْنَعُوا كُلَّ شَىْءٍ إِلاَّ النِّكَاح
Ku aikata dukkan komai, sai dai aure (saduwar jima’i) kawai.

Kuma Al-Bukhaariy da Muslim sun fitar da Hadisi daga Maimunah Bint Al-Haarith _(Radiyal Laahu Anhaa)_ ta ce:

'Duk lokacin da Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ yake buƙatar wani abu daga matarsa a halin tana haila, sai ya umurce ta ta ɗaura gyautonta (kamar sikel ko wandonta), sannan ya aikata duk abin da yake buƙata.’

Malamai sun yarda cewa: Janaba tana samuwa ce ta hanyoyi uku, kamar haka:

1. Fitowar maniyyi ta hanyar saduwa a tsakanin namiji da mace.

2. Fitowar maniyyi a cikin barci ko a farke, kamar ta hanyar yin wasa da al’aura _(istimnaa’i),_ ko amfani da ‘budurwar roba’.

3. Nutsewar kan al’aurar namiji a cikin na-mace a wurin saduwa, ko da kuwa maniyyi bai fita ba.

Don haka, idan miji ya yi amfani da wani sashen jikin matarsa, ba cikin farjinta ko duburarta ba, kuma idan har ya yi maniyyi da hakan, to ya yi janaba kuma sai ya yi wanka saboda haka.

Amma ita matar babu abin da ya same ta, matuƙar dai ba ta fitar da maniyyi ba.

_Wal Laahu A’lam._

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
28-2-2018

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now