​MACE ZA TA IYA DAGA MURYARTA DA KARATUN SALLAH ?​

343 9 0
                                    

​MACE ZA TA IYA DAGA MURYARTA DA KARATUN  SALLAH ?​

​Tambaya :​

Assalamu alaikum Malam barka da yau, tambaya zan yi malam. Shin ya halatta mace ta daga murya a cikin karatun sallah kuwa???

​Amsa :​

Wa alaikum assalam To dan'uwa ya halatta a gare ta ta daga muryarta yayin karatun alqur'ani a sallah, sai in akwai wanda ba muharrami ba a kusa, to sai ta yi kasa da muryarta, don kar ya fitinu.
Wasu malaman sun haramta mata bayyana karatu, in ta ji tsoran fitina, saboda Annabi s.a.w. ya umarci mata da yin tafi a sallah, lokacin da liman ya yi rafkannuwa, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta :1145,  sai suka fahimci cewa: Annabi ya umarce su, su yi tafi ne, don kar wadanda  ba muharramai ba, su ji sautinta.
Mace tana daukar hukuncin namiji a cikin dukkan hukunce-hukuncen shari'a, in har ba'a samu nassin da ya kebance ta ba, wannan ya sa za ta bayyana karatu a wuraren da  yake bayyanawa, in ba'a ji tsoron fitina ba .

Allah ne mafi sani .

​Amsawa​✍🏻

​DR. JAMILU YUSUF ZAREWA​
13\5\2015

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now