ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKA WA MUTUM RAGE YAWAN FUSHI*

264 1 0
                                    

*066 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKA WA MUTUM RAGE YAWAN FUSHI*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum, ya aiki? dan Allah ina niman alfarmarku, ina so ku ba ni wata addu'a saboda idan mutun ya yi min kuskure ko dan kadan ne wallahi sai na rama nake samun sukuni a zuciyata, ko da mijina ne idan yai min sai na rama ko da za mu samu matsala da shi sai na rama nake jin daɗi. Ni kuma ban san me ya sa nake yin haka ba, wallahi ni kaina ba na son hakan, saboda sai bayan na rama sai daga baya na dawo ina nadamar abin da na yi, na gode.

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu, Baiwar Allah yana da kyau ki sani cewa ba a son rama mummuna da mummuna, daga cikin kamalar mutum ya zama idan aka munana masa ba ya saurin ɗaukar matakin ramawa har sai ya yi uzuri iya uzuri, daga bisani sai ya ɗauki mataki ta hanyar maslaha, idan kuma abin da ake yi masa bai kai ya komo ba, to yin haquri ya fi alheri a zance na gaskiya.

Tabbas matuqar kika yi haquri, duk wani mai cutar da ke sai Allah ya saka maki a kwana a tashi in Allah ya so, saboda haka ki ji tsoron Allah ki riqa haquri da abokan mu'amala, musamman mijinki da kishiyoyinki idan kina da su, da abokan arziqinki a ko'ina suke, wani mutum ya zo wurin Manzon Allah ﷺ ya ce masa ya yi masa wasiyya, sai Manzon Allah ﷺ ya ce masa 'Kada ya yi fushi', ya kuma maimaita masa da yawa cewa 'Kada ya yi fushi', kamar yadda Abu Hurairata ya ruwaito.
Duba Sahihul Bukhariy 6116.

Sannan daga cikin abubuwan da suke taimakawa wajen rage yawan fushi sun haɗa da:

1. Yawaita yin addu'a a kan Allah ya raba mutum da yawan yin fushi, domin zukata suna hannun Allah ne.

2.Yawaita neman tsari daga Shaiɗan, saboda shi ne yake kunna wutar fushi a zukatan mutane, wato yawaita faɗin (A'uzhu Billahi Minas Shaiɗanir Rajeem).

3. Yawaita tuna sakamakon da Allah ya tanadar wa masu kame fushinsu.

4. Qaranta yawan yin magana, da canjawa daga yanayin da mutum yake a lokacin da ya fusata, wato idan yana tsaye ne ya samu wuri ya zauna, idan kuma yana zaune ne sai ya kwanta.

5. Nisantar duk abin da zai iya haifar masa da fushi ɗin, da barin tunanin abin da ke haifar masa da fushin.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
07/6/1440 h.
12/02/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now