*HUKUNCIN RAGEWA MUTUM MINTINA A GIDAN RADIO📻 BAYAN YA BIYA KUDI

256 1 0
                                    

*HUKUNCIN RAGEWA MUTUM MINTINA A GIDAN RADIO📻 BAYAN YA BIYA KUDI💵*

Assalamu'alaikum,
Malam Dan Allah menene hukuncin 5minutes da gidan radio📻 suke ragewa a kowanne program... Mutum ya biya kudin 1hr amma sai su yanke masa 5minutes wani ma yafi haka suke yankewa. Allah ya saka da Alkhairi. Ameen

*Amsa*

Wannan baza'ace haramunba muddin sun shardantawa masu shi haka ko kuma sanannene a tsarinsu,  Tunda
المسلمون على شروطهم
Kamar yadda idan misali kahau mota a tashar Kano zuwa wani gari, garin kuma tasharsu tana nisa da cikin garin kamar kilomita daya ko biyu ai bazakace sai an kaika cikin garinba saidai in ka shardantawa dreban haka,
   Amma in babu wannan sharadin ko wannan tsarin na minti 55 Madadin minti 60 to zaluncine,
ALLAHU A'ALAM

*Via Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu*
14/Al-muharram/1441
14/September/2019

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now