*SHIN YA HALASTA MUTUM YA SHA NONON MATARSA

662 9 0
                                    

*184 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*SHIN YA HALASTA MUTUM YA SHA NONON MATARSA?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum malam, tambayata a nan ita ce shin wai mutum yana iya Shan ruwan nonon matarsa ya halasta a addinin Musulunci kuwa?

AMSA:

Wa'alaikumus Salam, Shari'a ta halasta wa mutum ya ji daɗi da matarsa gwargwadon yadda ya so, amma ba tare da saduwa ta dubura, da kuma lokacin haila da nifasi, da lokacin harama da aikin Umra da Hajji ba, abin da ba wannan ba ya halasta miji ya ji daɗi da shi a jikin matarsa gwargwadon buqata, kamar sumbanta, da kallo da shafa da makamantansu.

Hatta mutum ya sha nonon matarsa duk yana daga cikin jin daɗi halastacce, ba a hukunta shi da irin hukuncin shayar da qaramin yaron da bai cika shekaru biyu ba, domin shayar da babba nono ba ya tasiri wurin haramta abin da shayarwa kan haramta, nau'in shayarwar da ke tasiri shi ne shayarwar da aka yi wa yaron da bai cika shekara biyu ba.

An tambayi malaman Lajnatud Dá'ima cewa: Mene ne hukuncin addini game da mutumin da kan ji daɗi da nonon matarsa har ya sha, shin abin da ya yi haramun ne ko halas, shin idan ruwan nonon matar nan ya isa zuwa hanjin mijin nan ta haramta a gare shi sai an raba auren?

Sai suka ba da amsa da cewa:
"Ya halasta ga miji ya sha nonon matarsa, haramci ba ya aukuwa saboda isar ruwan nono zuwa hanjinsa".
Duba Fataáwaál Lajnatid Dá'ima 19/351.

Sannan an tambayi Sheikh Ibn Jibreen game da wannan matsalar sai ya ba da amsa da cewa:
"Shayar da babba ba ya tasiri, domin shayarwar da ke tasiri shi ne wanda ya kasance an yi sau biyar ko fiye a cikin shekaru biyu kafin yaye, amma shayar da babba ba ya tasiri, saboda haka, in da wani zai sha daga nonon matarsa, to shi fa bai zama ɗanta ba".
Duba Fataáwá Islamiyya 3/338.

Imamuna MALIK ya ruwaito a cikin Muwaɗɗa daga hadisin Abdullahi ɗan Umar ya kasance yana cewa: "Babu hukuncin shayarwa sai ga wanda aka shayar yana qarami, kuma ba hukuncin  shayarwa ga babba". 
Duba Muwaɗɗa 2/603 na Imamu Malik.

Bisa dogaro da waɗannan dalilai babu laifi don mutum ya sha nonon matarsa, sai dai da za a tsotsa ba tare da shan ruwan ba hakan ya fi, amma shan ba laifi ba ne kamar yadda malamai suka bayyana.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Zarewa.*
16/11/1440 h.
19/07/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now