AMSOSHIN TAMBAYOYINKU

730 19 0
                                    

TAMBAYA 1,304
Assalama alaikum Malam Allah Ya qara fahimta. Malam idan nashi exam sai  in manta abubuwan Dana karanta kuma inaganin abin nasani amma sai  inkasa tunawa Dan Allah Malam ataimakamin da addu'a kuma abani shawaran abin daya  kamata nayi nagode
AMSA
ka lazimci wannan abubuwan suna taimakawa wajen rashin mantuwa da ƙara ƙarfin hadda
1. Shan zuma
2. Yawan ambaton Allah
3. Cin ƴaƴan inabi/ zabibi
4. Cin halal
5. Cin abinci mai kyau
6. Kaucewa saɓon Allah
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam Daiyib

TAMBAYA 1,305
Salam Malam Dafatan Alkhairi dan Allah malam  Ina So ka Turo min adduar Istikara?
AMSA
Hadisin istikhara hadisi ne tabbatacce daga bakin Annabi (saw) kamar yanda bukhari ya rawaitoshi hadisi na 1166, 6382, 7390 da abu dawud 1538 da tirmizhi 480 da nisa'i 3253 da ibn majah 1383 daga jabir ɗan Abdullahi yace : annabi ya kasance yana koya mana istikhara a al'amuranmu gaba ɗaya kamar yanda yake koya mana sura a cikin ƙur'ani yana cewa idan ɗayanku ya yunƙura domin yin wani al'amari to yayi raka'a biyu wanda ba farilla ba sannan ya ce: Allahumma inni astakiruka bi ilmika wa astaqdiruka bi kudratika wa as'aluka min fadlikal azim fa innaka taqdir wala aqdir wa ta'alam wala a'alam wa anta allamul guyub, Allahumma in kunta ta'alam anna hazal khairun li fi dini wa ma'ashi wa aqibata amri ajilu amri wa aajiluhu faqdirhu li wa yassirhu li summa barik li fihi. Wa in kunta ta'alam anna hazal sharrun li fi dini wa ma'ashi wa aqibata amri ajilu amri wa ajiluhu aajiluhu fasrifhu anni wasrafni anhu waqdir liyal kaira haisu kana summa ardini bihi)) sanna sai mutum ya faɗi buƙatarsa, sannan ya kamata mu sani cewa sakamakon istikara shine Allah ya tabbatar maka abin, ba mafarki ba
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam Daiyib

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now