TA SAMI SABANI TSAKANINTA DA MAHAIFIYARTA! MENE NE MAFITA?*

126 2 0
                                    

*173 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*TA SAMI SABANI TSAKANINTA DA MAHAIFIYARTA! MENE NE MAFITA?*

TAMBAYA:

Assalamu alaykum. Allah ya kara wa malam lafiya da nisan kwana. Malam !tambayata malam ita ce: Mahaifiya ce da 'yarta aka samu akasi aka samu matsala sai ita 'yar take cewa za ta je ta samu mahaifin maman nata ta fada masa abin da ya faru tsakaninta da mahaifiyar tata, sai mahaifiyar ta ce in kin fasa zuwa Allah ya tsine miki malam menene hukuncin tsinuwar? Malam kuma fa ba ta je wajen baban mamar tata ba malam, mene ne mafita?

AMSA:

Wa'alaikumus Salam, amin na gode da wannan addu'a. ƴar uwa abin da wannan ɗiya ta yi kuskure ne babba, bai dace mutum ya kai qarar mahaifansa ba ko da a wurin iyayen mahaifan ne, saboda yin haquri da abin da iyaye suke wa mutum ya fi masa alheri duk yadda ya kai ga rashin jin daɗin wannan abu, inda za a iya ɗaga qafa a kai qarar mahaifa wurin iyayensu shi ne inda iyayen suke take wa ƴaƴansu wani haqqi na Shari'a da ba zai yiwu a bar abin a haka ba, ko suke saɓa wa Allah kuma aka tsoraci kada hakan ya kai su shiga wuta, misali iyaye Musulman da ba sa kiyaye Sallar Farillah, ko wasu haqqoqin Allah makamantan haka, su ma ɗin ba kai qarar su za a fara yi ba, za a yi ta nuna masu haɗarin haka ɗin ne ta hikima da girmamawa, idan ya gagara ne sai a kai wurin waɗanda ake ganin ya dace.

Yanzu wannan tsinuwa da ta yi wa ɗiyar  ba a sani ba ko manufar tsinuwar har zuci ne ba, ko kuma a fatar baki ne kawai don ta hana ta zuwa wurin mahaifan nata ba, to mafita a nan ita ce  ta je ta qasqantar da kanta a wurin mahaifiyar ta ba ta haqurin wannan ɓata mata rai da ta yi, idan kuma ba za ta iya zuwa ita kaɗai ba, to ta nemi waɗanda mahaifiyar take  ganin girmansu su je tare a ba ta haquri, wannan shi ne mafita, kuma in Allah ya so za ta janye wannan kalma a kan ɗiyar.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
7/11/1440 h.
10/07/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now