*SHIN ZA A IYA YAYE YARO KAFIN YA CIKA SHEKARU BIYU

308 4 0
                                    

*069 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*SHIN ZA A IYA YAYE YARO KAFIN YA CIKA SHEKARU BIYU?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum malam ina da yaro yana da shekara daya da wata hudu da rabi, kuma na kasance ina da shigar ciki, kuma ciki na sani laulayi sosai mallam, zan iya yaye yaran?

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu, za ki iya yaye shi a wannan yanayi da yake ciki matuqar yaye shi a wannan lokacin ba zai cutar da shi ba. Saboda ayar da ke Suratul Baqara da ta ce iyaye su shayar da ƴaƴansu na tsawon shekaru biyu, ba ta qare ba har sai da Allah ya ce "ga wanda suka yi nufin cika shayarwar". Wannan sai ya nuna ba dole ne sai yaro ya cika shekaru biyu ana shayar da shi ba. Amma cikawar shi ne aka fi so, saboda yaro ya fi samun ingantacciyar lafiya.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
09/6/1440 h.
14/02/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now