*HUKUNCIN MAZIYYI DA MANIYYI

186 1 0
                                    

*009 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*HUKUNCIN MAZIYYI DA MANIYYI*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum Allah ya ka rama malam lafiya, dan Allah malam ina da tambaya, dan Allah malam yaya hukuncin Maniyyi da wadiyyi, kuma dan Allah malam a bambance min su biyun, kuma zan iya sallah?

AMSA:

Wa’alaikumus salam, bambancin da ke tsakanin maniyyi da maziyyi shi ne, shi maniyyi ruwa ne mai kauri mai tunkuɗar juna da ke fita a lokacin saduwa (jima'i), ko ta hanyar mafarkin saduwa, ko ta makamantansu, fitar maniyyi a jikin mutum yana wajabta yin wankan janaba.
Shi kuma maziyyi wani ruwa ne ɗan siriri (maras kauri) da ke fita a yayin da sha'awa mai qarfi ta motsa wa mutum, ko ta hanyar tunanin saduwa ko shafa da sauransu.

Shi hukuncin maziyyi ba kamar na maniyyi ba ne, domin shi idan ya fita ba wankan janaba ake yi masa ba, abin da kawai mutum zai yi zai wanke gabansa ne kamar yadda yake yi in ya yi fitsari, daga nan sai a yi alwala idan za a yi sallah ne, idan kuma ba sallah mutum zai yi ba shi kenan, tsarki kawai zai yi ba sai ya yi alwala idan ya ga dama ba.

Allah ne mafi sani.

*JAMILU IBRAHIM SARKI, ZARIA*
5/4/1440 H.
12/12/2018 M.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now