*TA MANCE DA NIYYAR WANKAN HAILA

393 2 0
                                    

*TAMBAYA TA 032*

*TA MANCE DA NIYYAR WANKAN HAILA*

_Assalamu Alaikum._

Mace ce ta gama haila har mijinta ya take ta, sai kuma jinin ya dawo na yini ɗaya. Da ta je wanka kuma sai ta yi niyyar wankan janaba kaɗai, ta mance da abin da ya auku a baya. To malam, ina hukunci?

*AMSA 032:*

_W alkm slm w rhmtul Laah._

[1] Al-Imaam Abu-Daawud ya riwaito Hadisi sahihi daga Sahabiyah Ummu Atiyyah _(Radiyal Laahu Anhaa)_ ta ce:

كُنَّا لَا نَعُدُّ الصُّفْرَةَ وَالْكُدْرَةَ بَعْدَ الطُّهْرِ شَيْئاً
Mun kasance ba mu ɗaukar Sufrah da Kudrah a bayan tsarki da wani matsayi

Don haka, abin da ya kamaci wannan baiwar Allaah ta yi shi ne: Tun farko sai ta dubi irin abin da ya fito mata a bayan tsarkin, idan wani abu ne mai kama da ruwan-ciwo *(Sufrah),* ko kuma wani abu ne mai kama da ruwan-ƙasa ko ruwan-nama *(Kudrah),* to ba za ta ma waiwaye shi ba, saboda wannan Hadisin na Ummu Atiyyah.

A ƙarƙashin wannan, abin da ta yi na manta niyyar wankan haila ba komai ba ne, tun da da ma ba haila ce ta fito mata a bayan ɗaukewar jininta kuma bayan saduwa da mijinta ba.

[2] Amma idan ta tabbatar abin da ya zo mata a bayan hailar launinsa da ƙarninsa da sauran alamominsa duk sun nuna cewa shi haila ne, to a nan sai a ce: Wataƙila kwanakin hailarta sun ƙaru ne, ko kuma da ma can ba ta riga ta yi tsarki ba ne. Don haka, tun da ba ta haɗa niyyar wankan haila tare da na janaba ba a lokacin da ta yi na janaban, kamar yadda sashen Malamai suke gani, ko kuma ba ta yi wankan hailar shi kaɗai da niyyarsa a bayan gama na janaban ba, kamar yadda ɗaya sashen na Malamai ke gani, sannan kuma da yake ɗaura niyya rukuni ne mai zaman kansa a cikin ayyukan ibada, wanda kuma ya haɗa da wankan haila, saboda Hadisin: *Innamal A’maalu Bin Niyyaati,* to sai ta tashi yanzu ta yi shi tare da niyyarsa. Shikenan.

[3] To, ko za ta ramo sallolin da ta yi kafin wannan gyaran? Sahihiyar magana ita ce: Ba za ta ramo ba, _in shaa’al Laah,_ saboda abin da Allaah Maɗaukakin Sarki ya faɗa game da addu'ar muminai:

رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَآ إِن نَّسِينَآ أَوْأَخْطَأْنَا
Ya Ubangijinmu! Kar ka kama mu idan muka manta ko idan muka yi kuskure

Kuma ya tabbata a cikin Sahih Muslim, Ubangiji Ta’aala ya ce:

قَدْ فَعَلْتُ
Na yarda.

_Wal Laahu A’lam._

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
14-3-2018

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now