*YAYA MATSAYIN KARBAR MAGANI A WURIN MAI AIKI DA JINNU

131 3 0
                                    

*196 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YAYA MATSAYIN KARBAR MAGANI A WURIN MAI AIKI DA JINNU?*

TAMBAYA:

Assalamu Alaikum, malam da fatan an tashi lafiya, Allah ya sa muna da rabo mai amfani, Don Allah malam, Ina so a kara min haske ne, wata mata ce ta ji wani mutum yana talla gidan radio, yana ba da maganin sihiri da masu aljanu, sai ta cire number shi ta je, to ashe da aljani yake aiki, a nan ne yake fada mata damuwan ta, wai aljani a ka tura mata shi ke saka ta cikin matsalan da take ciki, shin ya halasta ta karbi magani a wajen shi, ko bai halasta ba?  Allah ya kara basira.

AMSA:

Wa'alaikumus salam, ƴar uwa bai halasta ta karɓi magani a wurin irin wannan mutumi da ke aiki da aljanu don a yi mata maganin aljani ko sihiri ba, saboda wannan hanya ce ta kaiwa zuwa ga shirka, akwai hanyoyi ingantattu da Shari'a ta tanadar don a yi maganun aljanu ko sihiri, idan an tuntuɓi malamai za su ba da bayani.

Kuma an yi wa malaman Lajnah makamanciyar wannan tambaya sai suka ba da amsa da cewe:

"Neman taimakon aljanu ba ya halasta wajen sanin nau'in ciwon da aka kamu da shi, ko wajen yin maganinsa, saboda neman taimakon aljanu shirka ce, Allah Ta'ala ya ce: "Wasu mazaje daga cikin mutane sun kasance suna neman tsari da wasu mazaje daga cikun aljanu, sai suka qara masu zunubi"...
Dubi Fataáwál Lajnatid Dá'ima 1/92. (Almajmu'a ta biyu).

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
3/12/1440 h.
04/08/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now