*LOKACIN LA'ASAR YA YI BAN SAMI DAMAR YI BA HAR HAILA TA ZO MINI

98 0 0
                                    

*014 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*LOKACIN LA'ASAR YA YI BAN SAMI DAMAR YI BA HAR HAILA TA ZO MINI*

TAMBAYA:

السلام عليكم
Mutum ne tafiya ta same shi zuwa wani gari, to sha'anin mota har lokacin sallar La'asar bai sami damar yi ba har magriba ta yi, to a tsakanin wannan lokacin sai ga jinin al'ada ya taho, ya matsayin wannan sallar tasa ta La'asar din kenan?

AMSA:
وعليكم السلام
To 'yar uwa wanda ta sami kanta a irin wannan hali, za ta rama wannan sallar La'asar ɗin da ba ta sami damar yi ba bayan ta yi tsarki, saboda lokacin sallar ya yi kafin hailar tata ta zo mata ne, har ma sai bayan lokacin La'asar ya fita sannan hailar ta zo mata, don haka ne hukuncinta ya zama za ta rama .

Amma ba za ta rama sallar Magriba ba, tun da a daidai lokacinsa ne hailar ta zo mata.
Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
11/4/1440 H.
18/12/2018 M.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now