*TA YAYA ZAN RAGE YAWAN YIN MANTUWA?*

615 4 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*TA YAYA ZAN RAGE YAWAN YIN MANTUWA?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum, malam ina so a ba ni addu'ar maganin mantuwa idan da akwai, ya kasance ina yawan manta abubuwa gaskiya kwakwalwata ya dena daukan abu, ina dauka sai ba da jimawa ba sai na manta.

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu, A gaskiya ni ban san wata addu'a keɓantacciya da ta gangaro daga Manzon Allah ﷺ wadda take taimakawa wajen hana mantuwa ba, sai dai kawai shawarar da zan ba ki shi ne, ki riqa yin addu'a da kanki a kan Allah ya raba ki da yawan yin mantuwa na rashin kiyaye abu, kuma ki qara qoqari wajen nesantar saɓa wa Allah Ta'ala, sannan kuma ki yi qoqari wajen qara kiyaye waɗannan abubuwa:

1. Rage yawan surutai da ba a buqatar su.

2. Samun isasshen barci a kullum.

3. Naci wajen haddace abin da ake da nufin haddacewa ta hanyar yawan maimaita shi.

4. Rage wa kai yawan hidindimu, da kaucewa yawan zullumi.

5. Lizimtar karatun Alqur'ani.

6. Sa ikhlasi a cikin al'amura, wato duk abin da za ki yi, ki yi shi don Allah.

In Allah ya so Allah zai yaye maki yawan mantuwa idan kika kiyaye waɗannan abubuwa.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
28/6/1440 h.
05/03/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now