ZARAHADDEEN

بواسطة hijjartAbdoul

1.6K 71 8

read and find out المزيد

1
2
3
4
5
7
8
9
10
11
12
13
14
16
15
18
19
20
21
22
23
24
25
26.
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42.
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60

6

31 1 0
بواسطة hijjartAbdoul

*****"Lafiya naga kina ɗingisa ƙafa?

Cewar Sadiq yana amsar kayan hannun ta.

"Wallahi wani ne ya taka min ƙafa...

"Ya taka miki ƙafa?

Ameer yayi saurin tarar numfashin ta.

Tace, "Ehh".

Mota ya buɗe yana zaunar da ita tare da ƙafar ganin yarda ta yatsan da aka taka wurin ya ɗan kumbura.

"Shi kuwa wannan wanne ɗan kut***ba ne da baya gani, baya lura tsabar renin hankali".

"Kuma kamar yana sane".

"Ke kuma baki mare shi ba?

Sadiq tsayawa kawai yayi yana kallan sa. Ehh lalle Ameer daman haka yake?

"Muje ki nuna min shi na ci kut***sa ko shi waye dan uban sa. Dan uwar sa baya shi da hankali ne? Kalli fa ƙafar ki fa".

"Ameer dan Allah mu tafi".

"Sai de uwar mu tafi".

Ya faɗa yana kama hannun ta, dan ta kai shi ciki. Ita kuma taki tashi.

Sadiq yace, "Dan Allah kayi haƙuri wuce muje mu tafi, ai ba wani serious issue ne ba".

"Uhm".

Ya yasa ƙafar ta a cikin motar ya buga murfin da ƙarfi sannan ya shiga gaba ya zauna yana cigaba da zazzaga masifa yayin da Sadiq da Zarah ido ne kawai na su.

"To wai ke uban me ya hana ki kau ɗa masa mari?

"Mari kuma?

Ta faɗa tana ɗan zare ido.

"Eh mari uban waye ce ya taki ki".

Har suke je yana banbami yana ƙuncin rai daƙyar ya sa yayi shiru ya dena mita. Inda suka bar shi anan duka dawo suka same shi sai de yanzu kuma yayi shirin tafiya masallaci ne jira kawai yake ayi kiran magrib ya wuce still de aikin yake yi. Buɗe gate ɗin da aka yi ne kamar a fusge da ƙarfi yasa shi kallan gate ɗin Ameer ne.

"Me ya faru?

Ya tambayi zuciyarsa amsar da bashi da ita, har ya rufe gate ɗin ya dawo kusa da shi be dena kallan sa ba. Ganin su Zarah sun fito tana rakin ƙafar da yanzu ta sake tashi dan ba ƙaramin take mata ƙafa yayi ba da takalmin. Shi kuma Sadiq yana riƙe da ita suka ƙara so suka zauna a kujerar kusa da Deeni. Shi kuma Sadiq yaje ya ɗauko wata kujerar suka shi a tsakiya.

"Me ya faru?

"Wani ɗan renin hankali ne ya taka ni".

Ta faɗa idan ta na zubar da hawaye.

Ameer yace, "Dalla Malama rufe wa mutane baki, da baki waskawa shege mari ba kina wani ɗan renin hankali".

Deeni yace, "Me ya faru?

Ameer yace, "Wani ya taka ta, kuma ta zo mu je na ci uwar sa taƙi yarda shima Ya Sadiq ya biye mata".

"Shine duk wannan ɗacin ran?

"Yaaaa".

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli ƙafar ya kalli Sadiq ya maida kallan sa ga Zarah ya ƙura mata kallo kamar wanda yake san ganin wani abu a jikin ta. Ya juya ya kalli Ameer sannan yayi murmushi.

Yace, "Ameer".

"Na'am".

"To ai har haƙuri ta bashi".

"Yaya ya za'a yi ta bashi haƙuri? Mutum ya maka laifi kuma sannan ka bashi haƙuri?

"Anyi haka ko ba'a yi ba Zarah?

Tana sunkuyar da kan ta tana wann turo baki gaba ga kwalla da ta ka cika mata ido.

Tace,"Anyi".

"Allah shikuwa shiyasa Anty take burgeni ta wani lokacin, yanzu ne zaka ji ɗau ta ɗauke mutun da bari bata san reni ita a rayuwar ta".

Sadiq yace, "Ai naga alamar halin ku ɗaya da ita, komai faɗa komai faɗa haba dan Allah ku sauya rayuwar ku Wallahi. Ku ke yin haƙuri bakomai ake yin magana akai ba".

Deeni yana tattare kayan sa, yana tunanin su kam ba su da faɗa sam, mutum sai musu laifi amma za su bashi haƙuri, Sadiq ne kawai yayi fada sanda yana yaro amma yanzu shina be da faɗa, ko cacar baki ake zaka same shi shine mai sulhu saɓanin shi da ko kashe kan ku zakuyi ba zai kalle ka ba, ita kuma Zarah hayaniya amma akwai cika baki a baya wanda ya mata laifin. Sun kasance tamkar mahaifin su haka suke. Yayin da su kuma suka biyo halin Kakar su da sam ba sa barin ta kwana musamman Hafsat da har yau be taɓa ganin masifaffiya irin ta ba.

"To sai de ku kuke haƙurin amma nide ba zan yi ba".

Ya faɗa yana tashi ya wuce dan dagaske zuciyarsa tafasa take yi akan me zai taka ta? Duk laifin Zarahn ma yake gani. 

*****Hashim kuwa matuƙar mamaki ta bashi mamaki, to mene dalilin ta na bashi haƙuri bayan shine ya mata laifin? Haka de ya ture komai ya sai abinda zai siya ya wuce. Koda yaje kwanciya yana rufe ido fuskar Zarah ta zo masa, tare da 'ouch' ɗin da ta ce. Tashi zaune yayi yana shafa kan sa, kawai ya taka ta ne dan yaga wacce iri ce ita? Ita masifaffiya ce ko aka sin haka? Sai ya tarar da ita mai haƙuri ce dan har yanzu marin da Hafsat ta masa idan ya tuna haushin kan sa yake ji. Har yau be san wanne irin mataki zai ɗauka ba. Daga ƙarshe ficewa ma yayi daga hotel ɗin yaje ya sarara kan sa ya sake sannan ya dawo da ya tabbatar da baccin ya ci idan sa tukunna. Washegari babu aiki amma hakan be hana shi gudanar da abubuwan da suka zo yi ba.

*****Yau kam dukan su suke zaune a parlour har Hafsat da ta kasance mai zaman ɗaki. Ummu na matsawa Hajja ƙafar ta, ita tana aiki Sabir da Taufiq na karatu yana ƙara masa Hadithn da be iya ba, Ameerah kuma na kallo, Hafiz shima aikin yake yi.

"Allah idan baka mai da hankali ba zan ki fa maka mari abin ya ishe ni tun ɗazu ake faman yin abun ɗaya".

Taufiq ya faɗa a zafafe. Sabir yana jerin mutanen da baya saurin ɗaukan karatu amma idan ya ɗauka baya mantawa gashi kuma yana san karatun hakan yasa yake da san karatu. Irin su kuwa kowa yasan daman sai ankai zuciya nesa ake musu karanta.

"Kayi haƙuri".

Sabir ɗin ya faɗa abin tausayi, shi kan sa abin yana damun sa amma idan ya iya zo kaga yadda ake murna.

"Munafuki kamar na Allah".

Taufiq ɗin ya faɗa ƙasa-ƙasa yarda shi kaɗai ne zai ji shi, haka suka ci gaba amma kuma be iya ɗin ba, agogo ya kalla yaga goma saura tun wajen takwas da rabi suke faman yin abu ɗaya Hadith ƙwara ɗaya ya gagara ya riƙe shikam ya gaji. Karanta masa yayi be iya ba, ya buge masa baki be sauke nasa hannun ba yaji an kife shi da mari, marin da ya janyo hankalin kowa ya zuba musu ido, ko be ɗago ba yasan Antyn su ce.

"Tashi kasan inda dare yayi maka".

Ta faɗa tana rufe laptop ɗin ta. Tare da janyo Sabir ta daura shi akan cinyar ta ta kwantar da kan sa a jikin ta tana janyo Hadithn, tasan ba zai taɓa yin bacci ba matuƙar be iya wannan karatun ba, hakan yasa ta ajje duk wani aikin nata domin koya masa.

Hajja da ta fara gyangyadi kin mari yasa ta buɗe ido tana zabura.

"To nide a gidan ana yawan ɗaukan hakki na".

Banza tayi mata ta fara koya masa a hankali a hankali.

Hafiz yace, "Me kayi aka mare ka?

Shiru yayi yana muzurai yana ɗan kallan ta, duk ya tashi ya yi nesa da su.

Yace, "Ba abinda nayi".

"Haka ne".

Ya faɗa yana cigaba da aikin sa.

Hajja tace, "Ke dena danna min ƙafar nan nagaji kuma".

"Gaskiya Hajja kin tsufa da yawa".

"Uban ki ma zai tsufa".

Ummu tace, "Ahh Allah ya baki haƙuri".

Tace, "Wato Ameer ya tafi ko neman mutane baya yi ko? Ko ya kira ku?

Ameerah tace, "Nide be kira ni ko a chat ma be neme ni ba".

"Yo ke da kuka zo duniyar tare ma kenan bare kuma mu da daman ya tsane ni".

Ummu tace, "Yaya kira mana shi Bude Call kaji ko?

Ta faɗa tana komawa kusa da shi, kiran nasa yayi be ɗaga ba sai kawai ya kira Deeni yace zai kira Video call ƴan gida za su ga Ameer. Hakan yasa Deeni fita ya sanar da su sai be tafi ba  yayi musu connecting da Tvn, suna can connecting Hafiz yayi musu.

"Laaaa ƴan gidan mu".

Cewar Ameer yana ganin kowa da kowa kamar Yadda suma suke ganin su ga murya raɗau babu matsalar network.

Hajjah tace, "To me zaka faɗa mana? Bacin sai da muka nema ka tukunna?

"Kefa Hajja matsalar ki kenan, ai kya tsaya a gaisa ko? Anty ina yini".

Ɗagowa tayi ta kalle shi, shima lokacin Deeni ya kalli Tvn sai suka haɗa ido ta wani haɗe rai ta tamke fuska irin bana san kallan nan naka.

"Anty ki saki fuskar mana".

Banza tayi masa, Sabir ya tashi yaje ya tsaya a gaban Tvn ya fara zuba.

"Kai Sabir matsa daga nan naga ƴan uwa na".

"Wai ina Taufiq?

Ummu ta nuna inda yake da hannu.

Yace, "Me aka masa?

Ameerah tayi masa alama da hannu alamar marin sa aka yi ta nuna Hafsa.

"Allah sarki Balaraben gidan mu sannu fa,kai ma waye ka ce  taɓa ɗan lelen Anty".

Deeni girgiza kan sa yayi yana kallan ta, ita kuma lokacin ta tashi ta ɗauki littafin Sabir tare da kiran Sabir ɗin ta goya abin ta. Tana gunguni ita kaɗai bakin ta kawai ya kalla yasan me tace kafin ya ƙare mata kallo tana tafiya har ya dena ganin ta. Su kuma suka ci gaba da hiran su yarda bikin Ameerah zai kasance, har Sadiq ake tsara bikin yayin da Zarah da Ummu sune bakin maganar Ameerah ita kawai shiru tayi tana jin su bata ce komai ba, sun jima suna wayar daga ƙarshe suka kashe kowa yaje ya kwanta cike da annashwa.



******Yana zaune a office ɗin sa yana aiki aka kira shi a waya, aka sanar da shi Meeting ɗin da za suyi ƙarfe goma, ganin lokaci yaja ya sa shi tashi domin ganowa ko ta zo, dan sun yi waya da Hafiz yace masa za su zo. Yana fitowa suka gware da ita, ita kuma an nuna mata office ɗin sa domin zuwa su yi magana.

"Baka gani ne?

Ta faɗa tana ɓata fuska, tare da kallan kayan da ta zubar, yasa kai zai fice.

Tace, "Kayan waye zai kwashe min?

Bece da ita komai ba ya durƙusa ya kwashe mata jakar ta da takardun da suka zube ya bata. Tasa hannu ta karɓa. Ta kuma sa kai zai wuce.

Tace, "Baka iya bada haƙuri ba?

"Allah ya baki haƙuri".

Ya faɗa yana ratsa ta zai kuma wuce wa.

"Baka ji ba".

Sai ya tsaya be tafi ba.

"Baka ga office ɗin ka na zo ba?

Maimakon yayi magana sai ya koma baya ya buɗe mata office ɗin shi kuma yayi waje, tunda tace masa office ɗin sa ta zo sai taje ta zauna a office ɗin.

"Kai kuma ina zaka je?

Ta faɗa a masifance dan wannan shirun nasa ta gaji da shi ace mutum ba zai yi magana ba sai shiru. Sai ya dawo ya zauna a kujerar sa, ita de bata ce komai ba tana tsaye shima be ce da ita komai ba.

"Zaman ma ba zaka ce nayi ba?

"Zauna".

Ya faɗa yana cigaba da aikin sa kafin su shiga meeting ɗin. Duka wannan weekend ɗin be yi wani aiki sosai ba, dan research kawai yake yi. Haka suka ƙaranci shirun su babu wanda yace da kowa komai kuma ko ɗagowa be yi ba daga abinda yake yi har ya kalli lokaci, sannan ya tashi ya fice, iya haushi da shaƙa ta shaƙa kam babu ƙarya, itama lokacin ta kalla sannan ta tashi da sauri ta bi bayan shi dan bata san inda Za'a yi meeting ɗin ba yanzun ma sai da ta tambaya aka nuna mata.

"Ka tsaya mana".

Sai ya tsaya be juyo ba.

"To mu tafi".

Ta faɗa bayan ta kamo shi, sai ya kalle ta, suka tafi. Tare suka shiga meeting Kamar de na farko shine ya gabatar da komai aka jinjina musu aka kuma karrama su kafin ana ɗauki share ɗin su da ta zo karɓa aka basu daga nan aka yi hotunan samun nasara sannan aka yi ƴar ƙwarya kwarya ɗin walima a wurin  duka be ɗauke su wani lokaci ba aka tashi. Cin abincin ne kawai ya ɗan ja musu lokaci ɗaya da rabi suka fito daga wajen office ɗin sa ta dawo tayi alwala tana cikin toilet ɗin shima ya shigo sam be lura da mutum ba sai da ya buɗe toilet ɗin, tana gaban madubin tana alwala ya cire hijabin ta a gefe kai ba ɗan kwali. Saurin fita yayi yana furta sorry.

"Da meyasa ba zaka yi knocking ba. Kawai kayi ta kalle wa mutum jiki".

Yana jin ta be tanka mata ba, ji rashin gaskiya irin nata fa, wai shi da office ɗin sa amma ta zo take masa iko. Matar nan ko. Kafin ta fito ya shimfiɗa mata abun Sallah, shi kuma ya wuce yayi alwala ya zo ya fita. Tana zaune shiru be dawo ba, kuma Hafiz yace tayi masa magana ya kai ta airport.

Har ya dawo tana nan a zaune inda tayi sallah, be yi mata magana ba yaje ya zauna a kujerar sa yana cigaba da aikin sa, tashi tayi ta fara naɗe abin sallahr lokacin Ameer ya shigo bakin sa ɗauke da sallama bayan sa Sadiq ne, be ƙara sa sallamar ba yayi kan to da gudu yana ambatar sunan ta.

"Kai dalla can meye haka?

Ta faɗa tana matsawa ganin yarda ya yo kan ta zai rungume ta. Tsayawa yayi yana ɓata fuska.

"Gaskiya Anty baki haɗu ko ɗan irin missing ɗin nan nawa baki yi ba".

Ya faɗa yana zama a kujerun dake office ɗin, itama zaman tayi tana cewa.

"Ka san sarai bana san hauka ai".

"Ina yini".

"Lafiya, ya aikin?

"Ke de bari aiki yana nan muna yi, ni fa zan haɗawa Ameerah kayan ɗakin ta, ke ma idan auren ki ya tashi nine nan zan haɗa maki ko ƴar Anty na?

"Kai fa baka rabo da hauka".

"Daman ai haka zaki ce".

"Shi wannan gemun fa da ka fara tsaidawa".

"Anty bakya gani na, gemu na tun a gida ya fara ɗan fitowa".

Ya faɗa yana shafa abin sa, ko dan ƙare masa kallan da tayi ne yasa ta sai yanzu ta gani oho ko dan ba kula bace bata sani ba sai de yanzu taga ya fito.

"To de be maka kyau ba".

"Kai Anty Allah zai min kyau bari su fito dayawa".

"Kai ma gemun zaka tsaidar? To de ba kyau yake maku ba".

"Ahhh kiji fa aiki, Annabi haka yace ku sake gashin baki ku bar gemu".

Banza tayi masa bata ce komai ba, sai da suka yi shiru Sadiq yace, "Anty ina yini? Ya gida? Ya Hajja? Ya kowa da kowa?

Kallan sa tayi kallan irin duk ni ɗaya? Kafin tace, "Lafiya".

Ameer yace, "Kai Anty haka zaki ce Lafiya Alhamdulillah duk suna nan lafiya, suna gaida ku".

"To Usman".

"Laaa Anty sunan Baban to ba ruwana".

"Wai ba za'a kai ni airport ɗin ba?

Ta faɗa tana kallan shi, be kalle ta kamar yarda bata ambaci suna ba, shima be san tana yi ba. Ameer ne yayi masa magana sannan ya ɗago.

"Sadiq je ka kai ta airport".

Daga be kuma cewa komai ba ya cigaba da aikin sa. Da Ameer aka tafi shine ya ringa zuba shi kaɗai tana ɗan bashi amsa haka haka de.

*******Yau ne ake sa ran dawowar su Baba kowa yana ta murnar dawowar su, dan ba ƙaramin kewar iyayennasu  suka yi ba. Anyi musu girki kala kala shi da Umma kowa an dafa masa abinda ya fi so. Ana yi azahar Hafiz yaje ya ɗauko su, batare da ya sanar da kowa ba, suna zaune sai ganin su suka yi Sabir da gudu yaje ya rungume Baba, ɗaga shi sama Baba yayi yana farin cikin ganin sa, haka Ummu da Ameerah duka rungume Umma dan sosai suke cikin farin ciki da ganin su.

"Baba sannu da zuwa".

Ta faɗa tana mai cike da farin cikin ganin Baban na su. Taufiq kuwa rungume Baba yayi duk da ya dauki Sabir.

"Hajiye ta".

Ya faɗa yana kamo ta, haɗa su yayi da Sabir da Taufiq ɗin ya rungume su.

"To ai kwa bar su haka ko? Kunje kun rungume su ko?

Taufiq yace, "Kawai ki ce mu barki ki ga ɗan ki shine magana".

Suna ƙara sowa za su zauna.

Yace, "Taufiq wato Hajjan tawa kike yiwa haka?

"Ai bari kawai, Malam( haka take fada masa saboda ɗan ta ne na fari) haka yake min kar ka so kaga yarda yaran nan suke min".

"Hajja ".

Suka haɗa dukan su suka faɗa.

"To karya zan yi muku?

Hafiz yace, "Haka ne yi haƙuri ga Baba nan ya zo zai yi maganin su".

Baba kawai murmushi yayi bece komai ba, Umma ta gaida ta ta amsa sannan suka wuce wajen Umma zuwa sama. A tare suka ci abinci dukan su kowa na murnar ganin su cike da farin ciki. Har zuwa dare suna tare. Kafin Hajja tayi magana da Baba. Suna zaune a ɗakin ta, tana saman gado shi kuma yana ƙasa.

"Malam".

Tunda yaji haka yasan magana ce mai muhimmanci, hakan yasa shi gyara zaman sa yana jin ta.

"Magana ce ta Alhaji da ya zo min da ita".

Shiru yayi yana kallan ta.

Yace, "Hajja wacce magana?

"Maganar bikin nan yana so a ƙara matso da ita nan da wata ɗaya".

Shiru be yi magana ba.

"Na kuma ce masa babu matsala dan haka yace zai dawo idan ka dawo".

"To Hajja duk abinda kika yanke ai dai-dai ne".

"Kana ganin ya shiryu kuwa?

Sai da yayi murmushin sa dake ƙara fuskar sa ta dattijai kyau.

Yace, "Ai Hajja in sha Allah babu matsala tunda komai ya wuce. Kuma sune da kan su suka zo suka ce suna so. Sannan shima yaron naga da hankalinsa kawai mu bi ta da addu'a". 

"To shikenan Allah yasa Alkhairi kake ƙoƙarin haɗawa, Allah kuma ya maka albarka. Da ka manta duk wani abu da suka yi maka a baya".

"Ameen Hajja Nagode".

Daga suka ɗan taɓa hiran su na ɗa da uwa, take sanar da shi kafar ta ta matsa mata kwana biyun nan daƙyar take iya takawa.

"Hajja ko asibitin nan zamu koma ayi gashin nan".

"Kayya jikin tsufa ne fa, daman sai a hankali ai. Ai mun jima a duniyar munga abinda zamu gani".

Baya san take wannan zancen, dan kuwa uwa uwa ce duk tsufan da zatay shi yana san ta a haka ko da kowa zai gujeta. Sai da ya gama shafa mata man zafi a ƙafar ya rufe mata ita da abin rufa sai da yaga tayi bacci sannan ya fito ya same su a parlour Umma na ɗaki ta kwanta, Hafsa ma bata nan.

"Ina Ameer?

Dan tun ɗazu yake son tambayar su amma sai wani abun ya zo ya manta. Shiru suka yi aka fara kallan-kallo.

Hafiz ne yace, "Baba yana Kano wajen Deeni, Deenin ne ya ce masa su tafi ganin yarda ya nace sai ya bishi".

"Kai kuma ka barshi ya tafi?

"Yi haƙuri Baba".

Ya faɗa yana sunkuyar da kan sa, cike da ladabi, Hafiz yana da wani abu indai yayi laifi zaka masa faɗa ya bada haƙuri sai sunkuyar da kan da ƙasa yayi kalar tausayi zaka nemi wannan faɗan ka rasa, wannan kuma baya rasa nasaba da irin shaƙuwar da suka yi da Deeni dan shima haka yake, har gwara Hafiz zaka ɗan iya masa faɗan amma ba duka amma shi Deeni sai de ka bishi da nasiha.

Kamar de yarda ya faru a yanzun, kasa ma masa magana yayi kawai ya wuce ya tafi ya barshi a tsaye, ajiyar zuciya Hafiz ya sauke yana mai cike da farin ciki.

******"Assalamualaikum Baba ina yini".

"Yi hakuri na ga kiran ka ban samu na kira ba sai yanzu. Ya gida ya su Zarah da Sadiq?

"Duka alhamdulillah Baba. An dawo lafiya?

"Alhamdulillah".

"Na kuma ji wani abu Deeni, kai yanzu..."

"Baba dan Allah kayi haƙuri".

Yayi saurin tare shi.

"Baba tunda yana so a barshi yayi ɗin, kuma kaga daga zuwan sa Alhamdulillah dagaske yake san yi aiki dan sosai yana samun ƙaruwa. Kuma sannan Baba a wajen aiki babu wani ɗan gida a wajen abinda suka ga daman kawai suke yi. Shi Sadiq ba kullum yake tsayawa ba, ni kuma aiki da weekends ɗin ma bana san mun dama".

"Baba kayi haƙuri yana so, shi ne yace zai yi. Kada a durƙusar da wannan ƙwarin gwuiwar nasa".

A hankali ya cigaba da bawa Baba hujja masu ƙwarin, wanda ko waye ana masa wannan maganar dolen ka kayi haƙuri. Ya rasa Deeni wanne irin mutum ne.

"

واصل القراءة

ستعجبك أيضاً

272K 17.4K 48
The feeling of being abandoned by one's own family was not unknown to Aadhira. She hates her family for abandoning her when she was only a newborn, l...
32.9K 3.7K 25
Love is a strong feeling of affection, idolization, adulation, endearment and adoration. Love is happiness and love is delight. As a young Muslimah...
18.8K 2.2K 17
I went through my heartbreak messages. I have kept record of them ever since I started dating. My friends got tired of keepin track of my love storie...
5K 874 17
Every girl's dream is to find that perfect man, that perfect person who loves you, cares for you and sticks by you no matter what. Aleeya is tricked...