..................................
       Haka rayuwar tacigaba datafiya, Rahma tanata shan laulayi Dan cikin NATA maisa laulayine, cikin 'yan kwanaki dukta rame, bakomai take iya Ciba, yanzu hakama tadaina girki Dan batason k'amshin gas ko kad'an, kullum daga gidan Ammi ake kawo musu abinci safe da yamma Dan darana tana gidan AMMI, idan zaitafi aiki saiya ajiyeta can, idan kuma yataso yabiya ya d'auketa, daga shi har Ammi tarairaya suke mata ta musamman tamkar zasu maidata ciki, Appa ma ba'a barsa abayaba, duk abinda Rahma tace tanaso saiya siyo mata shi, kamar yanzune za'a haifi jikan farko agidan, ita wani lokacinma har kunyar kanta takeji, amma yazatayi badasonta take sakasu wata wahalarba tsirface kawai irinta ciki.
    Nawal kullum idan tadawo makaranta tana nane da Rahma, maganarta bata wuce yaushe zaki haifomana babyn momy?.
   Rahma takanyi dariya tacemata bayanzuba da sauran lokaci.
    Wata sa in takanyi dariya wataran kuma kuka ta ce, " itafa dawuri take so ahaifamusu sabon baby.
    Idan Ammi ko bobo suna kusa ake diramar sukanyi musu dariya.......

..................................
        Safna na kwance afalo ita kad'aice yau agidan, Abba yana kasuwa, ummi kuma tana gidan aunty yahanasu mamansu Basma, taje saka ranar auren Basma da akeyi yau.
   TV take kallo amma bata fahimtar komai a film d'in dukda sonsa datakeyi tamkar mi.
    Ta gyara kwanciyarta tareda kai dubanta ga hotonta itada Rahma sannan suna yara, sunyi matuk'ar k'yau duk sunyi murmushi, takuma kai dubanta gawani k'aton hoto Wanda yak'awatu da k'yau, kauda idanunta tayi tanamai share hawayen dake ziraro mata akumatu.
   Dubana nakai ga hoton danson ganin suwaye ajiki?, hummm Rahma CE da bobonta sunyi masifar k'yau, hoton and'aukeshine aranar mother's day, tanasanye da bubu shikuma bobon suit, tad'anyi k'asa da kanta yayinda bobo ke kallonta yana murmushi, ya munner agefensu yana bama Rahma wani Abu.
      Masha ALLAH nafad'a azuciyata danba k'aramin k'yau sukayiba, dolene Safna taji 6acinrai, tamayi k'arfin hali databar hoton Agalon, kodayake tana tsoron ummi ne kawai nasani.
      Sallamar da ake kwad'awane yasakata mik'ewa tana tsaki, k'ofar tanufa tabud'e, ganinsu zeenat da baseera yasakata k'are tamke fuska, tayi hakane saboda baseera.
     Basuji komaiba gameda canjawar tata Dan sunsan halin kayansu.
   Cikin falon suka bita, kowa yanemi gurin zama batareda tabasu izinin hakanba.
    Itama tsanar baseerar datayi bai hanata had'o musu abin motsa bakiba kamar yanda tasaba, koba komai aii harda mai k'aunarta Zeenat.
       Zeenat takalleta cikeda tausayawa ta ce, "Safna yak'arin k'arfin jiki?.
   gyara zamanta tayi ta ce, " da sauk'i Zeenat, aina warke.
   Baseerama ta mata ya jiki, adak'ile ta amsa mata.
   Zeenat takuma fad'in wlhy mu bamusan bakida lfy ba, mundai kwana biyu bakije school ba toshime mukace bara muzo muga ko lfy?, munshigo anguwar muka had'u da yaya kamal yake fad'a mana harma asibiti kika kwanta.
   Safna tad'anyi murmushi wlhy kuwa zeenat har asibiti na kwanta yau kwana hud'u da sallamomu.
   ALLAH yasa kaffarane.
   Ameen.
Daga nanan sukayi shiru nad'an lokaci, Zeenat takatse shirun da d'akko zancen bobo.
   Baki Safna ta ta6e saiga hawaye.
   Arud'e zeenat da Baseera suka k'arasa gareta suna lallashi, dagananma har Zeenat ta zayyanemata yanda sukayi da Baseera a kwanankin baya, dakuma Nuna mata tayi nadama, itama suka Shiga mata nasiha da lallashinta da nunamata muhimmancin iyaye da had'arin bijire musu, baseera ta durk'usa har k'asa tana Neman gafarrar safna.
    Ta ce, "tayafe mata, ALLAH ya yafemusu baki d'aya, daganan zeenat tak'ara musu nasiha itama, saikuma suka koma hira tamkar basune sukasha kuka yanzunba.
   Anan suka wuni zubur suna k'ara kwantarma da Safna hankali dakuma k'ara bata shawarwarin yanda zata nemi gafarar iyayenta.
    Saida ummi tadawo suka gaisa sannan suka tafi gida.

%%%
         Da daddare bayan Abba yadawo suna zaune afalo shida ummi saiga ya Shaheed da ya munner.
    Safna dake kwance ad'aki tamik'e tanufo falon Dan ganin ga dama tasamu na Neman gafarar iyayenta da 'yan uwanta.
    Tunda tafito kowa yamaida kallonsa gareta, ganin tanata ra6e-ra6e Abba ya ce " safnata miya farune?."
    Tana tsaye saiga hawaye suna zirara akumatunta, ya munner sarkin tausayi yatashi yaje yakamo hannunta, zaunar da ita yayi kusada k'afafun Abba.
   Abba yadafa kanta yana fad'in haba safna mike damunkine wai a 'yan watanninnan?, kodai har yanzu jikinne mukoma asibiti?.
    Kanta ta girgiza tana share hawaye, cikin shashshekar kuka ta ce, "Abba Dan ALLAH Ku yafemin Kozan samu sassaucin son Abdulmaleek dake son hallakani, wlhy Abba nayi nadamar abinda na aikata, nayi kuskuren bijiremuku akan abinda wayona bazai bani shiba, Abba narantse muku *_NAYI NADAMA_* (sabon buk d'in pertymerh xarah) Dan ALLAH Abba kujanye fushin dakukeyi dani kozan samu ubangijina yabar fushi dani.............nanta shiga basu labarin yanda akai tagane Abdulmaleek shine Wanda take so alokacin data bijire musu, tafad'a musu komai danganeda shawara da muguwar k'awa tabata, saidai ta6oye sunan kowacece kuma batafad'i zuwa gidan malami da bokayeba.......tarushe dakuma mai tsuma zuciyar mai sauraro.
      Tabasu tausayi sosai Dan haka suka shiga lallashinta, Abba ya ce, " munyafe miki Safna domin kuwa ALLAH ya nuna miki kuskurenki tuntuni nadamace dai kika gagara yi saboda sharrin shaid'an, to ayanzunkam ki tabbatar kinyi tuba na gskya Wanda babu kome a aikata wani laifin makamancin haka.
   Kanta tad'aga tana fad'in ngd Abba ALLAH yak'ara tsawon kwana da ikon cigaba da rik'emu, ta rarrafa gaban ummi tana kuka da Neman gafararta, ummi tajata jikinta tarungumeta, nayafemiki safna domin idan nace bazan yafemikiba bansan kuma wane irin gararin rayuwa zaki fad'aba nan gaba, nayafemiki ki kwantar da hankalinki kema ALLAH zai baki miji nagari domin Abdulmaleek yamik'e nisa ayanzu, shid'in mijin k'anwarkine.
   Nanma kanta ta girgiza ta ce, "nahak'ura ummi tuntuni, saidai har yanzu inajin sonsa azuciyata, jinake tamkar kullum ana k'aramin sonsa, ummi ta6a k'irjina kiji, tayi maganar tana kamo hannun ummi tad'ora asaitin zuciyarta.
    Ummi ta jinjina kai danjin bugun zuciyar Safna dake fita da k'arfi, tabata tausayi sosai, dama doctor Kaleel yafad'a musu zuciyarta tana barazanar kamuwa daciwo Ashe dalin son *_Abdulmaleek_* ne.
    Lallashinta ummi taitayi da kwantar mata da hankali, suma su ya Shaheed da ya munner dukata rok'i gafararsu sunkuma gafartamata, tareda alak'awarin tayata da addu'a.
    Nasiha sosai sukai mata mai ratsa jiki da jini.

Tundaga ranar Safna tazama wata shiru shiru amma har yanzu son bobo na nan mak'ayale da zuciyarta saidai Alhmdllh yaragu bakamar daba dayaso zame mata ciwo.
    Yanzukam kulawa ta musamman iyayenta suke bata da k'arajanta ajikinsu, hakan nak'aramata kwanciyar hankali da k'aunarsu, haka rayuwar tacigaba da shurawa har ayau ranar wata juma'a da iyayenta sukazo mata dawata magana ta had'ata aure da yaya kamal, (Brr....kamal Abubakar, yayansu Ameera kuma abokin aikin bobo).................

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now