Shikam yanayanacan gaban Appa suna magana.
     Appa ya ce, "Mukarram tunda Alhaji sunusu dala yabada hak'uri miyasa bazaka hak'ura dakaishi koti ba, bakamar yanda kayi niyya tun farko ba?.
     Appa idan na k'yaleshi to bansan mizaimin agaba ba, badan ALLAH ya tak'aita wahalabafa nasan yaransa zasu iya kashe Rahma da Nawal alokacin nan, Amma shine yanzu zai dawo yana 'Yar murya wai ayi hak'iri, naga da ko magana baya maka amma dayake yanzu yasan miya shirya shine zaizo yay maka dad'in baki akan kahanani kaisa kotu?.
    Hakane mukarram amma ni aganina duk bak'in halin mutum idan yay nadamar kuskure dayayi to yanada k'ayau agafarta MASA tunda ALLAH ma muna MASA laifi kuma idan muka rok'eshi saiya yafe mana, amatsayina na mahaifinka INA rok'ama alhaji sunusi gafara agareka da iyalanka, daga nan idan yasake yunk'urin cutar dawani namu saika d'auki matakin daduk yadace bazan hanakaba saidai na taimaka maka akan hakan.
    Shikenan Appa zan yafe MASA to amma Alhaji Abdurrazak fa?, na tabbata tare sukayi k'ulle k'ullen sacemin mata da 'ya.
     Eh nasani Dan yafad'ami. Shinema yazugashi akan suyi hakan, to amma wani nacin arzik'in wani aii, to shima Alhaji Abdurrazak yaci arzik'in Alhaji sunusi.
    Shikenan Appa zanfad'ama Ammar karsu tura maganar kotu dama sonake agama bikinnan sannan mushiga kotu, tunda hakane zan fad'a MASA najanye amma akwai shari'ar damukeyi da Alhaji Abdurrazak akan kisan Barrister Lawan Usman D/tofa, da ake zargin su suka saka akasheshi akan wata shari'a daya tsaya da lauyansu kuma yasamu nasara.
   Ranar dayaje office d'ina danyimin gargad'i kuma yaso tabbatar min dahakan saidai bodyguard d'insa yak'atseshi.
    Ajiyar zuciya APPA yasauke ya ce, "a'a wannan bazan hanakaba kam Dan waccan shari'ar daban wannan daban Dan haka saidai nace ALLAH yabaka Nasara, Yakuma k'ara kareka daga Sharrin mak'iya da azzalumai, ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka.
    Ammeen Appa, bobo da Ammi suka amsa.
   Daganan wani zancan suka d'akko.
   Bobo yakalli agogo tareda mik'ewa, Ammi Appa bara nashiga Office time na wuceawa kuma inada shari'a yau k'arfe 11:30.
     To ALLAH yabada nasara jarumin babammu.
    'Yar dariya yayi yana k'ok'arin fita, to kugaidamin inna da Baba Dan bazan samu shiga wajensuba nayi latti.
    To zasuji idan sun fito.
   Ficewa yayi da hanzari, abakin k'ofa yaci karo da Idris tareda ya sulaiman zasu shigo.
        Tofa kukuma daga ina haka?, bobo yay maganar yana mik'amusu hannu, gaisawa sukayi cikin musabaha.
   Ya sulaiman ya ce, "yanzu nashigo muka had'u da idris zashi gaida su Ammi.
   Bobo ya maida kallonsa ga idris, ya karatu idris?.
   Alhmdllh yaya komai normal munata fama.
  To ALLAH ya taimaka, ni bara nawuce nayi latti.
   To ALLAH ya tsare yabada sa'a.
   Ameen ngd.
Ya sulaiman ya ce, " yauwa idan katashi kuma Kannada lokaci plss kad'an biyo ta asibiti dama inason ganinka.
   Okey babu damuwa saina shigo.
  Okey saina ganka shima ya sulaiman yafad'a suna nufar ciki shida idris, shikuma bobo yafito.

Motarsa yanufa hankali kwance yabud'e yashiga yana fad'in masha ALLAH yanzu kuma sai office.
    Idan ka gama dani ko?........
    Da sauri bobo yakalli gefensa dan son ganin waye?.
     d'aure fuska yayi tareda fad'in miyasa kina shigarmin  mota?, wama yabaki izinin shiga?.
        Wani murmushi Safna tasaki tareda k'ara lafewa cikin kujerar tana shak'ar k'amshin mortar da turaren bobo, tayi far da idanunta tana kallon k'yak'yk'yawar fuskarsa, aibasai anbani izinin shiga motar mijina ba, tayi maganar tana d'an d'aga gira.
   Kauda kansa yayi daga kanta tareda k'ara had'e fuska, ke banason k'aramin iskanci fitarmin amiota.
    Safna ta marairaice fuska harda hawaye, cikin muryar kuka ta ce, "Dan ALLAH ka saurareni wlhy magana nazo muyi kuma mai muhimmancice.
     d'agowa yayi yakalleta haryanzu fuskarsa ad'aure take, ganin tana kuka saikuma tabashi tausayi, bayason mutum yashiga damuwa akansa, yad'an huro iska daga bakinsa tareda kallon jan agogon fatar dake hannunsa 8:45, batareda ya kalletaba ya ce, " nabaki minti5 Dan inada abinyi.
     Hawayen fuskarta ta share ta ce, "wlhy minti5 yamin kad'an pls ka k'aramin.
    d'agowa yayi yad'an kalleta saikuma ya kauda kai, saidai ki hak'ura kuma saina taso daga aiki Dan yanzu haka nayi latti, so idan nadawo zanzo nan saiki sameni amma ki tabbata magarki tanada muhimmanci, kuma ki tabbata itace magana tak'arshe dazata shiga tsakaninmu daga ita kifita arayuwata, ina d'aga miki k'afane saboda banaso nazama silar rushewar zumincin iyayenmu, sannan bazan iya wulak'anta jinin Rahma ba, dan itama bata wulak'anta jininaba.
   Batareda yasake kallontaba yatada motarsa, ya ce, " sai anjima.
   Jiki a sanyaye Safna ta bud'e motar ta fito, hakan yayi daidai da fitowar ya sulaiman da idris.
   Suduka cikin mamaki suke kallon Safna da kuma motar bobon.
  Bobo dake kallonsu ya sulaiman ta madubi yad'anja tsaki, dama abinda yake gudu kenan, ganin ya sulaiman kamar yanufoshi yaja motar da sauri yabar gidan Dan bayason tambaya, musammanma akan safnar.
     Cak ya sulaiman ya tsaya yabi motar da kallo har bobo yafice daga gidan, kallonsa yadawo dashi akan Safna dake ida share hawayenta.
    Rissinawa tayi tana gaisheshi sannan tara6a ta gefensa zata wuce.
   Jimana ya sulaiman yafad'i yana kallonta.
   Safna tatsaya harya k'araso gabanta suna fuskantar juna, lfy kuwa mike faruwa?.
    Babu komai safna tayi magana muryarta nad'an rawa, shiru ya sulaiman yay yana kallonta da nazarin yanayinta, yad'an gyara tsayuwarsa yana sauke numgashi, ya ce, "keba yayar Rahma bace?.
     Yayartace, cewar Safna.
   To amma miya had'aki da Abdulmaleek? har kike kuka?.
   d'ago ido tayi ta kalleshi, bazata iya kallon idonsaba Dan yana mata kamada na bobo, tayi shiru batareda ta iya cewa komaiba.
   Ganin bazatayi maganaba ya ce, " to shiga cikin....
    Da sauri tawuce batareda ko juyowaba.
   Shima binta yayi da kallo cikin mamakin miye tsakaninta da bobo?, bai zargi komaiba Dan yasan bobo dodon matane, bazai ta6a zarginsa da fasik'anciba, amma tabbas akwai wata ak'asa tunda har bobo yafice daga gidan Dan bayaso suyi magana.
    Yabud'e motarsa yashiga zuciyarsa cike da waswasi, shima ficewa yayi da zummar zai tambayi bobo inhar sun had'u.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now