*.......................*
       Washe gari talata su bobo suka shiga shari'a.
   Tun azaman farko hankalin lauyan Haneef yatashi, dan tabbas yasan Bobo kwarone tunda bayau suka fara karawaba, yasan kuma bobo baya tsayama Mara gsky koyaya suke kuwa, komin k'arfin alak'arsu.
       Zaman nan nafarko kawai bobo yakawo hujjoji da dama wad'anda suka saka mutane dayawa yadda Haneef ya aikata abinda ake zarginsa dashi, amma dayake alk'ali yaci kud'i saiya d'aga shari'ar sai nan da sati biyu masu zuwa.
    Anan lauyan Haneef yanemi Belin haneef amma bobo yace Sam bai yardaba, Alk'ali yasan halin bobo dabin kwakwaf dama kuma bawani shiri sukeba, Dan haka yace k'orafi bai kar6uba, zasucigaba da rik'e Haneef.
    Ran Alh Sunusi ya6aci, sai kallon miye haka?, yakema Alk'ali.
    Alk'ali kuma yanamasa magana da ido akan subi ahankali.
    Duk abinda ke faruwa bobo yana kallonsu, Dan haka yasaki murmushin sa na mugunta, Wanda Ammar kankira da yafi saukar Boom ban tsoro, amma ga Wanda yasan ma'anar murmushin ga bobo kenan.

Suna fitowa daga shari'ar gida bobo yay shirin tafiya, daka gansa Kasan yana cikin farinciki, bud'e  motarsa yayi zai shiga Alh Sunusi da masu tsaronsa suka k'araso wajen, bobo yaja sirin farin gilas d'insa k'asan ido Wanda yadawo k'arshen hancinsa ya tsaya.

_( na ce, "anyi shirin rashin arzik'i kenan��)?._

    Alh Sunusi ya watsama bobo harara, yaro har yanzu kanka yana rawa ko?.
   Murmushi bobo yayi, tareda bud'e  motar yawatsa kayan hannunsa a sit d'in baya, yarufe murfin sannan yajingina da motar yana kallon Alh Sunusi cikeda basarwa.
    Alh wai minayi maka hakane dazafi? kasaka rayuwata agaba.
    Yakamata ka lura dawani Abu, ni lauyane mai zaman kansa, banida banbanci dad'an kasuwa, so saina gadamar saida maka hajata, idan banida ra'ayi saikaje gaba kasiya, Alhaji karik'e girmanka, banaso mufara game tare dakai, Dan akwai matsala.
       da d'anka nake shari'a bada kaiba, so ka kalli gabanka kada katsaya kallon ruwa kwad'o yayi maka k'afa wlhy.
    Yana gama fad'a yashige mota, Alh Sunusi kuma yana zabga ruwan masifa da bala'i, jiyake yak'ara tsanar yaronnan.
   Fuuuuu bobo yaja mota tareda bud'ama Alh Sunusi k'ura, by Alhaji sai zama na biyu, bobo yafad'a yana figar motar yabar harabar get d'in.

Kwafa Alhaji Sunusi yayi, tareda fad'in zakasan koni waye yaro.

.×.×.×.×.×.×.×.×.×.×.
        Da sallamarsa yashigo falon, saidai shiru babu kowa, yakalli agogon hannunsa  12:15pm Nawal bata dawo school ba, aransa yace to ina momynta?.
   K'arar Rahma yajiyo daga d'akinta, da sauri yanufi d'akin, hakan yayi daidai dafitowar Rahma dagudu daga bayi, daga ita sai tawul, jikin bobo tafad'a tana rawar jiki, bashida za6i saina rungumeta, yanda jikinta kerawa kawai ya isa kasan wani abune yabata tsoro.
   "K!, miya farune?."
Dadyn Nawal Dan ALLAH kataimaka ka kashemin shi wlhy inajin tsoronsa, kataimakeni plzzz, tafad'a tana kuma ruk'unk'umesa, tamkar zata fasa jikinsa tashige.
    Bobo ya girgizata "k kinutsu kifad'amin minene mana?.
     d'agowa tayi tana d'an hakki, tuni idanun nan NATA masu kasheshi sun wani sake fitowa, yakula duk yanda yarinyar tashiga rud'ani ko tsoro idonta baya canja kala..... Tunani takatse masa da nuna hanyar bayi.
        Hannunta yakama suka nufi bathroom d'in, kinga Nutsu ki nunamin banason shirme, abayansa ta mak'ale, tashiga waige² Neman abinda yatsotata saidai wayam yabar wajen.
   Yaja tsaki yarinyarnan ALLAH kinyi mugun rainani, yanzu inbanda raini minene a Bathroom d'innan?.
   Wlhy naganshi da idona, saidai idan ya 6oyene, harara ya watsa mata yayo baya zai fita yad'an matseta da bango.
   Sukur² taji abayanta, Dan haka tayi saurin turashi takalli bango, wani k'ara takuma fasawa tatafi luuuu zata fad'i.
   Da sauri yatareta tafad'o jikinsa, Tawul d'in jikinta ya kwance, yakai dubansa ga abinda tagani, wata 'Yar k'aramar k'adan garuwace, (Tsaka), da alama ta'inda zata fita ma take nema, yamaido kallonsa kan Rahma wadda yakeda tabbacin ta suma, runtse idonsa yayi Yakuma bud'ewa a kan k'irjin Rahma, shima jikin nasa rawa yafarayi, da sauri yakauda kansa yaja tawul d'in ya rufe mata jikinta, d'aukarta yayai cak, jikinsa dukya mutu yafito da ita zuwa kan gado.
   Zama yayi yadafe kansa Dan yau surar Rahma ta tsokalishi, babu abinda yake ambata sai _"Hasbinallahu wani'imal wakil"_, tuni idonsa yakad'a yay jajur, zumbur yamik'e yafita kafin yayi aika², kichin yashiga yabud'e firij yakwaso lemon tsami har biyar, jikinsa har rawa yake wajen yankawa, dandanan yamatse ruwan lemon akofi yashanye, ko azababben tsamin baijiba.
   Yadire kofin saman tebird'in tsakkiyar kicind'in, yadafe hannayensa biyu tareda runtse idanu, yakai minti10 ahaka sannan yabud'e ido yaja d'aya daga kujerun kicind'in yazauna yana sauke ajiyar zuciya, tamkar jinjirin daya kwana ya wuni baisha nonon mamansaba.
   Nanma kwantar da kansa yayi atebir d'in, yad'an jima ahaka sannan yatashi jikin a sanyaye yad'auki ruwa mai sanyi ya kwankwad'a, yakusa shanye gora d'aya kafin yacire yana sauke numfashi, goran ruwan yad'ago ya kalla sannan yafice daga kicin d'in.
    d'akin Rahma Yakoma, har yanzu tana nan inda yabarta, yak'arasa gaban gadon ya zauna, yayyafa mata sauran ruwan hannunsa yayi, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, saikuma tamik'e zumbur ta kwakumeshi tana fad'in dadyn Nawal plzzzz kaje kafiddata wlhy banason ganinshi wayyo ALLAH ummi kizo ki ceceni na bani.........
    Ganin yanda take gogamasa jikinta gashi tabi ta k'adandaneshi, idan suka k'ara d'aukar lokaci ahaka bazai iya jurewaba, sai kawai yadaka mata tsawa.
      k!!!!!!!, dallah ki nutsu banason shashanci, miye abin tsoro a tsaka?, duk kinbi kin wani rud'a kanki har kina k'ok'arin illatamin lafiyata Mtsooooow, yaja tsaki.
    Tuni Rahma tashiga  hankalinta, amma har yanzu jikinta rawa yakeyi, harma batasan Tawul d'inta ya k'ara zamewaba.
    Gaba d'aya hankalin bobo yakuma tashi, yatsurama k'irjin Rahma ido tamakar zai cinyeta d'anya.
   Ganin kallon k'urillar dayake mata yasa itama ta kalli jikinta dantaga miyake kallone haka..... Idanu tawaro tareda jan bedsheet d'in ta k'udun dune jikinta.
   Mik'ewa Bobo yayi yayo kanta................

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now