Ajiyar zuciya ya sauke tareda lumshe idanunsa, zuwa wani lokaci ya bud'e idon, d'an murmushi naga yayi Wanda bansan da liliba, saikuma yacigaba da aikinsa yana shan shayi.

Itakam Rahma tana komawa d'aki tahaye gado ta kwanta abinta sai barci.

::::::::::••••••••••••:::::::::
       Washe gari Rahma ta tashi kamar yanda tasaba ta had'a break fast da gyaran gida, taima Nawal wanka itama tayi, kwalliya sosai taima yarinyar tai tsaf da ita, Dama ga ruwan k'yau d'an Asali, kan baby Nawal yasha gyara Dan jiya da yamma Rahma tayi mata kalba, kasancewar yau juma'a.
   Tana cikin saka mata janbaki yaturo k'ofar yashigo da sallama ciki ciki kamar Wanda akaima dole
  Da sauri Nawal ta hantsilo daga kujerar madubi danta hango daddynta ta madubi, oyoyo papa na tafad'a cike da farinciki tana rungumesa, shima d'aukarta yayi yad'aga sama yana dad'in "I luv u my child," yasumbaci kumatunta.
   Ta shagwa6e fuska, papa shine jiya kak'i ka dawo ko?, lah nadawo mana, saidai kinyi barci sannan kitanbayi momy kiji?.
   Nawal takalli Rahma dake kallonsu cike da sha'awa, wai haka momy papa yadawo jiya?, kai Rahma tad'aga mata tana murmushin daya kusan narkar da Bobo atsaye, hakane babyna yadawo kina barci.
   Nawal tasunbaci kumatun babanta da k'asunba ta kwanta luf tanata shek'in gara.
   Shikam hankalinsa nakan Rahma yana mata wannan munafikin kallon NASA k'asa k'asa.
   Talura dashi tsaf dan haka tatsargu, rissinawa tayi ta ce, "INA kwana?."
    Lfy, yafad'a cike da basarwa shi adole ba ita yake kalloba.
   Rahma ta d'an ta 6e baki, dukda ta fahimci salon amsa gaisuwarsa kenan...... Muryarsa ta katse mata tunani, kushirya idan mungama break gida zamu wuce, Dan duk juma'a a can kowa yake yini.
   Ahankali ta jinjina kai kamar wata k'adan garuwa.
   Shikam yajuya yafice da Nawal ahannu.
   Itama fitowa tayi tahad'ama kowa abinci agabansa, hankalinsa kwance yakecin abinci shida d'iyarsa, amma Rahma duk atakure take, haka kullum take cin abin ci atakure, bakuma danwai bata saba da ahakan bane, saidai kawai nauyinsa datakeji, tunda agidansu gaba d'aya suke had'uwa suci abinci tuntana yarinya.
   Tananan tana juya cokali haryagama shida Nawal, yad'auketa suka koma falo suna jiranta.
   Ganin yatashi yasata sakin jiki taci abincinta sannan takwashe kayan taje ta d'auraye.
   d'aki takoma tacanja shigarta cikin wani had'ad'd'en doguwar rigar shadda pink colour, kayan sunmata k'yau sosai, tasaka k'aton farin hijjabinta sannan tafito, babu kowa afalon, danhaka takashe komai na kayan wuta, gamawata keda wahala yafito shida Nawal daga d'akinsa, hannunsa rik'eda jakar aikinsa.
   Kallo d'aya yaymata yad'aukekai, saidai har azuciyarsa yaji dad'in hijjabin data saka, yanason kamilar mace arayuwarsa, gaba yay suka bishi abaya.
   Tashaya kulle k'ofar falon shikuma sukai gaba cikin mota shida Nawal.
   Ganin Nawal abaya itama tabud'e bayan zata shiga, ahankali yay maganar tamkar mai ciwon baki.
   "Halan ni direban kine?."
    Cak tatsaya tafasa bud'ewa, kuma tak'i dawowa gaban.
  Yakuma cewa kina 6atamin lokacifa, kuma wajen aiki zanje,  jiki a sanyaye tabud'e gaban tashiga, shima baisake cewa komaiba yatada motar suka fice bayan sun gaisa da baba mai gadi.

Karatun Alkur'ani yasaka musu, cikin k'ira'ar shiek Abdurraham sudes, ahankali Rahma kebin karatun, yana kallonta ta gefen idonsa, jiyay tak'ara girma a idonsa.
   Har sukaje gidan Appa babu Wanda yay magana, garama Nawal takanyi jefi2.
   Saida yatsaya suka gaisa da baba mai gadi, yaymasa alkairi kamar yanda ya saba sannan yashige ciki.
           Yana faka motar Nawal tafice da gudu zuwa cikin gidan, sukuma suka fito cikin nutsuwa, da gudu khairiyya da khursiyya suka fito, rungume Rahma sukayi suna farin cikin ganinta.
  Ta ce, "aini nayi fushi, daga zuwa d'aya baku sakeba.
   Kiyi hak'uri auntyn mu, Ammi ce ta ce, " mubari sai nan gaba.
    Bobo yak'araso yana harararsu to maganannu ai kwabari kushiga gida dai ko?, yay gaba abinsa.
   Khursiyya ta ta6e Baki, aifa yau munga banu jarabatu yazo, ALLAH yasa aiki zai wuce cewar Khairiyya.
   Rahma najinsu dai tayi murmushi kawai.
   Cikin gidan suka shiga, hakan tayi daidai da sakkowar Ammi daga saman Appa, Dan Nawal nazuwa canta haura.
   Ta rungume Rahma tanamai jin dad'in ganinta, cike da kunya Rahma ta rissina ta gaida Ammi, ta amsa cikeda fara'a, da tambayarta ya zaman babudai wata Marsala ko?.
   Kan Rahma ak'asa ta ce, "Ammi babu matsalar komai, to Alhmdllh d'iyata haka nakeson ji.

A'a mukarram d'ina lfy dai ko?, Ammi tafad'a tana kallon bobo dayay tsaye yana kallonsu tun d'azun.
      yaturo baki gaba kamar wani yaro, yo Ammi sai yanzu kika san dani?.
   Ammi taje takama hannunsa, o ni na isa namanta da babana, kawai ina murnar ganin d'iyatane.
   Yakuma turo Baki, Toni bari nakoma tunda bak'ya murnar ganina, yanda yay maganar ashagwa6e yasa su khairiyya kwashewa da dariya.
  Harara ya watsa musu suka bar wajen, itadai Rahma murmushi takeyi da mamakin Bobo, irin wannan shagwa6a haka kamar wani d'an shekara 5, anace mata tanada shagwa6a toga Wanda yatakata iyawa.

Ammi ta lallashesa suka haye sama domin gaida Appa.
    Appa yaji dad'in ganinsu sosai, Dan haka yaymusu nasiha sosai sannan bobo yamik'e yaymusu sallama Dan wucewa aiki, saikuma antaso.
   Yakalli Rahma k'asa k'asa ya ce, "saina dawo.
    Kanta ak'asa ta ce, " ALLAH yatsare yabada sa'a.
  Yaji dad'in addu'arta Dan dama ita yake son ji.
   Ammi taji dad'in addu'ar da Rahma taima bobo, hakama Appa, suma sukai masa yatafi.

Zuwa 10:30 gidan yagama cika, aunty Rasheeda da 'yayanta, aunty Sameera ma da NATA, aunty ummy ma haka, mazan kuma suna ajiyesu suka wuce wajen aikinsu.
   Dan danan gidan ya haukace da hayaniya, yaran duk suna falon sama wajen Appa, sukuma iyayen suna falon k'asa sunashan hira kamar wasu k'awaye, babu wannan shegiyar ak'idar ta kishin Sauri, hirarsu suke sosai, Dan danan Rahma tasaki jikinta dansu, su aunty Rasheeda akwai saurin shiga rai, gasu khursiyya iyayen shafta............

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now