32

126 5 1
                                    


   Allah sarki a haka Saleema ta shafe wajan awa uku tana kuka ba bu irin lallashin da Maigidan bai mata ba amma takasa anan bacci ma ya d'auketa akan kujerar gidan.
   Alhajin gidan ne yace wato yarinyar nan tausayi taban, Kuma anawa ganin abinda uban ya fad'a kamar ba haka abin yake ba, saidai bansan gaibu ba amma dan Allah ki kula da ita. Saleem ya ringa d'ebeta kewa duk da uban yace kada ta fita.
   Kinga Idan kika fita aiki sai 6, so zaman ba dad'i haka. Insha Allah zan kula da ita Yauwa.
    Sultan kam da Deen kwana sukai suna tattaunawa akan yadda zasu b'ullowa wannan abin, duk hasashen su babu basuga hanya ba, kuma sun rasa ina Abba yakai Saleema dan sunyi tambaya babu wanda yace yes yasan inda take.
    Saleem ne ya shigo gidan, cak ya tsaya ganin Saleema na bacci, leka fuskarta yai tabbas Saleeman Deen ce wannan, to ya akayi tazo gidan?.
   Jin motsin Maman sa yasa yai saurin yin sallama da qarfi yana Mama nadawo, A'a Saleem ka dawo sannu da zuwa dama fita zanyi, kuma ga bakuwa kaga bazan barta Ita d'aya ba, tunda gaka ma saika zauna.
   Ok Mama ba damuwa, d'aki tashiga bata jima ba ta fito, taimasa sallama ta tafi.
   Tana tafiya waya ya janyo
'Hello Deen Ango ina amarya?
  "Kai saleem kasan komai fa ko nace kaji shine zakace ina amarya.
   Bangane ba mene?, nan ya bawa Sultan waya sukai magana tunda shi bai iyawa, hankalin sa baya jikin sa.

   Ai kafin sultan yagama jin zancen ya datse wayar sun mik'e sai gidan su Saleem.
   Waya sukai masa sunzo fa yana sunga kamar ba kowa a parlour'n?, eh ina part din Abba kuzo nan.
  Haka suka mik'a Deen yakasa gasgata cewa Saleeman sa na gidan.
    Da sallama suka shiga, amsawa Saleem yai, kana yace ku zauna muyi magana kada naje wani abinne yasa aka kawota gida, namayi saurin gaya maka, fad'an ya akayi ta dawo gidan mu?
   Deen shine yamasa bayani tun farko har kawo yanzu, hawaye Saleem ya share tace tabbas nasan Alhaji Sani amma wannan mutum bai mori hali ba, Allah yasaka muku. Ameen sukace
    Ina Yaya Saleema?, nuna masa d'aki yai tana ciki bacci ma take. Sultan ne ya mike sai Deen baiwar Allah tanakan kujera a takure ga hawaye duk ya bushe a fuskar ta, Sultan ne ya shafa kanta yace Deen Ku godewa Allah jarrabawace wannan Allah yasa kun cinye yana gama fad'a yasakai ya fita dama Saleem bai biyo su ba.
   A hankali ya taka zuwa inda take, idonta yafara kallo yaga ya d'aga alamar taci kuka ta k'oshi dan har ajiyar zuciya takeyi, baisan lokacin da hawaye ya zubar masa ba na tausayin ta.
    Hannun datayi matashi da shi ya d'auke, sannan ya daga kanta ya aza kan cinysa duk abinda yake mata bata motsa ba, illama shigewa jikin sa datayi.
    Wata irin ni'ima yaji a jikin sa, da nutsuwa jin jikin su ya had'u waje guda. A haka bacci shima ya d'auke shi ya d'an rankwafa jikin ta.
    Saleem ne yace Sultan ya dai naga mutumin shiru?, huum abinda zance kenan, wataqil ana kashe wa juna zuciya ko kuma dai amma bara nagani.
   Tare suka shiga ganinsu sukai a haka bacci ya d'au shauqi, Murmushi Sultan yai yace kwayi bacci yara, ai kun wahala, fita sukai suka barsu.
    A hankali Saleema ta tashi k'amshin Deen ne yafaramata sallama kafin ta bud'e ido ta ganshi hancin su nakan na juna hannunta Yana cikin nasa, bata gasgataba saidata tab'ashi taji gaske ne da sauri ta mik'e shima lokacin ya bud'e idon.
     Kallon juna sukai kafin takaimasa masa wata wawar runguma tana dariya. Deen kaine?, bakinta kawai yake kallo yadda take furta maganar cikin sanyin murya kaikace sarewa ake kad'a wa.
      Da hannu yamata alama datayi masa kiss batayi musu haka suka d'auki lokaci suna abu d'aya. Harsaida suka cika dan Kansu.
      Saleem ne ya shigo anan suka yanke shawarar Deen yaringa zuwa kafin komai ya daidaita Kuma saiyayi a hankali kada agano su.
***********
   Lokaci na tafiya kwanaki na shud'ewa satittika na zuwa, amma babu abinda ya sauya tsakanin Deem da Saleema soyayya suke sha a gidan kamar gidan auren su.
   Deen nan yini nan kwana saleem yana musu CID. Dan akwai lokacin da Abba yazo gashi bakatatan yazo Deen da Sultan duk suna gidan, ana parlour anata hira kwatsam saiga Abba Saleema hanjjn cikinta saidaya Kada Deen kam kwakwalwarsa ce tadena aiki tunda ido hud'u sukai da Abba.
  Amme me ko qarasa shiga baiba akamasa waya, d'aukan da yayi ya juya waje shine ya cececesu Kuma da yake kusan ba'a hayyacinsa yake ba, bai gane Deen ba. Shiyasa akasaka Maigadin gidan CID da Saleem.

    Deen da Saleema kam a yanzu babu wanda yakaisu farinciki baran da sanyin nan, hooo ana shan d'umin juna, dama kwangila ce aikin Deen kuma yana iyakar iyawar sa wajan ganin komai ya tafi daidai.
    'Abban sa ganin kamar Deen ya canja Kuma baya kwana a gida, yasaka takanas rannan ya bishi yaga inda zashi, kwatsam ya ga ya shiga gida hankalin sa ya tashi Deen me yazama rashin Saleema zaisaka Deen a hanya bata gari ba."
    "Kamar ya shiga yaga gane?, amma yakasa dan baisan abinda idonta zai gane masa ba, amma yai takaicin rayuwar da Deen ya zab'awa kansa, yai takaicin d'ansa kamili Yau gashi zaije wajan wata ko yasha abinda zai gusar masa da hankali."
    Haka ya dawo gida, Mom d'in Deen itama tafara fuskantar wani abu shiru kawai tai, mijin tama a yau taganshi wani iri, tasan halinsa baya fadar damuwar sa, saidai kabi mutum da addu'a.
    10:30am Deen ya shigo gidan, yana wani karsashi har tunbi da wata k'iba yai, ga sajensa wanda Saleema ke so yai masa d'as a fuska, a haka ya shiga wajan Abban sa.
     Zama yai Abba ina kwana?, lafiya lou Deen ya kake?, Abba lafiya ras nake yana magana yana d'an murmushi.
     Hira suka fara jefi jefi, daga can Abba yace Deen ina kaje baka kwana a gida ba?
    D'agowa yai yace Abba a gida na kwana mana da Asubah na fita.
    Haba Deen nifa uban kane ba aboki ba, nasanka sarai, wato ka canja hali zakazama d'an iska kana yawon dare ka zama matured daidai dani da Yayun ka, abin kunya zaka janyo mun koh?.
    Shikenan Imam Deen tunda haka ka tsarawa kanka, rayuwa ce.
     Baibari ya k'arasa maganar ba, da kuzari ya gurfana agaban Abba muryarsa na rawa yace Abba wayace maka ina bin mata wallahi abinda bantab'a yi ba kenan a rayuwa ta.
    Bansan mace ba sai akan Saleema bantaba had'a jiki ko hannu da wata ba, Illa Saleema Abba kasan halina fa wallahi qarya ake mun.
    Kaga bafa kuka nace kamun ba, ko ka taran jama'a magana ce nake maka, ina kaje jiya a court road?.
     Wajan Saleema naje amma bantaba zuwa wajan wata ba, nan ya kwashe ya gayawa Abba abinda ake ciki komai da komai, kabbara Abban yai to amma meyasa baka gayan tun wuri ba?.
    Ina tsoro kada kace nadena zuwa ne, Huum Deen mai Saleema dariya yai yace anyi ba'ayi ba kenan bonono rufe k'ofa da b'arawo Allah ya kyauta nima kaga wajan wani Malami Sharifi zamu akan a taimaka mana da addu'a akan Allah ya yayewa Abban Saleema abinda ke damin sa.
      *******
   Abban Deen takanasa yaje gidan Aminan nasa baya nan lokacin, zama yai ya tara yaran gidan Allah yasa weekend ne, yamusi bayani akan komai da komai.
    Ya Na'eem shida Sultan kaf sunsan maganar so basuyi wani d'oki akan haka ba, Maman kam kukan dad'i tasaka Ashe yarta na kusa Kuma wajan mijin tama.
   Rigima tasaka sai a kaita ta ganta wallahi tai missing Saleema over tanaji kamar sun shekara basuga juna ba, da qyar ta yadda sai da Safe sannan zasu kaita.

    Sagir yasamu abinda yake so dukiya, kullum cikin facaka da ita yake, gidaje wajan Uku na Abban Saleema suka siyar wanda su takardunsu a hannun sa suke Kuma ya basu su.
    A yanzu yazama raqumi da akala komai sai Alhaji Sani, hatta abincin da zaici a gidan sa shine mai aikowa da komai,
   Motocin Abba kaf suna gidan sa, abin tausayi Abba baya iya hasala komai, shikam shida Matar sa duniya sabuwa basa ma garin yanzu suntafi Singapore siyayyar bikin Sagir da d'iyar chairman na marad'i, sun saki kud'i sun yi ta'adinsa shiyasa aka basu 'ya.
     Yau kam Saleema ta tashi da kasala tarasa meke mata dad'i, gashi alkubus take sha'awa a yadda takeji kamar Idan bataci yanzu ba mutuwa zatayi,

    Ga Deen yaje Akhra (Ghana), Hajiyan gidan bata nan. Waya ta d'auka Maman Deen taiwa waya.
   "Hello Mom saida suka gaisa sannan tace mata tana son Alkubus ya za'ayi yanzu Kuma take son ci?, da sob'o amma kada asaka sukari.
    Tana zaune amma tsam ta mik'e me kikace Saleema?, jikin ki ke ciwo ko haka kawai kike so?, Allah Mom haka kawai Natashi ina sha'awar sa, kunu jiya ma nadama da kaina wajan sati biyu bancin shinkafa dama shiyake siyomun Tomas kuma ni nagaji dashi yanzu.
    Baki bud'e takejin bayanin data ke, indai hakane Saleema nada shigar ciki, to tayah?,
    Shiru tai saida ga can tace ba komai bara nai masa sainasaka a oven dan yai saurin tashi ko?
    Yauwa Mom da d'ata Idan ansamu mai kawowa Sultan shida Saleem sunje Bichi wajan STYLICH, kinsan sun tubure sai 'yan Bichi, saleem shi Zainab yake so.
   Masha Allah yaran gidan Alhaji Abdullahi koh?, eh. Ah namusu murna da samun yara nagari masu dattako, ahaka sukai sallama kana tabi lafiyar gado kafin a kawo.
   Awa d'aya biyu akayi, saiga waya d'an aiken yazo, da sauri ta mik'e taje ta amsa, hannu baka hannu kwarya haka ta zauna tax ta cinye wajan 8 Leda, lemon kam tunda tad'aga mug d'in empty ta ajiye sa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 07, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now