18

73 2 1
                                    


   Yana gama magana ya fita, Deen cikin d'akin kuku yake yana Abba me kayiwa Abban Saleema daya zab'i ya tarwatsa rayuwar mu, Abba bani nakeji ba Saleema nakeji wallahi bazata karb'i abinda Abban ta yazo da shi ba.
Kansa ya kwantar akafad'ar Abban nasa, yace Abba da gaske zaka auran Saleema?, amma kuma ai shiya keda iko da ita, duk maganar da yake uban kanzil baice ba illa ma runtse idonsa da yayi
A can kuma Sultan yana kan Saleema wadda ke cikin halin na kuka amma, magana ko kuka mai sauti takasa
Kanta yana kan cinyar mahaifiyar ya, idonta na kulle, sai ajiyar zuciya take, Maman ta itama hawaye take sharewa, wayarta ta janyo, yaranta ta bugawa tace lallai Yau adaren nan su biyo flight suzo hankali ba'a kwance yake ba.
Rud'ewa sukai akan menene, Abban Deen ya kirasu ko wani abu akayi?, ba komai kuzo dai, tom mama gamu nan.
Kanta take shafawa tanamata addu'a, amma ba magana jin alamar saukar numfashi yasa ta duba Alhamdulillah bacci tai, a hankali ta zame kanta ta d'ora kan pillow, shima sultan tsabar takaici a inda yake bacci ya d'auke sa.
Ko da Abban ya dawo bai nemi kowa ba, d'akin sa yayi, yana jin kamar ya sauke nauyi akansa, amma Kuma Idan ya zauna yanason tuno wani abu saiya kasa duk Iya tunanin sa ga Ibadarsa datai rauni abin da tausayi
Yayun Deen sun matsa sai Abba yafad'a musu meke faruwa, amma babu Wanda yasamu arzik'i n kallo acikin su
Ganin yak'i yace musu komai, yasaka kowa tashi sukai masa sallama, daga nan wajan Mom nasu sukai itama sallama sukai mata kowa yakama gabansa.
Tana ganin sin tafi itama ta shirya, taje wajan mijinta, turus tai ganin Deen a kwance ajikin uban, shikuma yana lallashi da sanyin jiki ta k'arasa, agefen su ta zauna tace Alhaji lafiya wani abun akayi?
Babu komai, bangane ba komai ba, meyasami Imam d'in?, kallon ta yai, hawaye taga yana sharewa abin tausayi wato wata musiba ce ta kunno kai tsakanina da Alhaji Abdulazeez wanda a yanzu ya kamun kud'in zancen yaron nan yace bazai bashi Saleema ba, nan ya zayyanomata komai da ake ciki.
Salati tafara tace shidai Sani wanda yazo kwanaki har ka kamun complain akansa? Shifa lallai Allah ya kyauta wannan abin duba wane kwarai. Matarsa tasani? Eh bata bashi goyan baya ba, shine yake cewa matarsa da yaransa narabashi da su
Alhaji addu'a itace mafita tun duniya batasan mai ake ciki ba, ayiwa tufkar hanci amma raba yaran nan Wallahi abune mai wuya, sun wahala ada ayanzuma haka tabbas kasan abinyi
Deen shi baccinsa yakema, haka Abban ya gyaramasa kwanciya a gadon, itakuma Maman taje kamasa kunun data damamasa.
Lokacin daya dawo gida, shiru yaji kamar ba kowa, hakan yasa ya zauna a parlour kozaiga motsin su, amma shiru baidai tashiba ya cigaba da zama yana k'issima abubuwa a ransa akan Alhaji Raheem.
Baiwar Allah Maman su Saleema Ita k'ok'ari takema na gyara wa Sultan kwanciya wanda ya kwanta a k'asa Allah yasa akan rug ne, shiyasa ta janyo pillow tasamasa ta kawo blanket ta rufamasa ana d'an sanyi AC ta kashe ta kunna heater Tana zaman jiran yaran ta
11pm daidai Motarsu ta danno kai cikin gidan, baiji shigowar mota ba, sai sallamar su dayaji. Amsawa yai yana bin kowanne da kallo "lafiya da tsohon daren nan ?
Kallon kallo suka fara, ba suce komai ba, saiga Maman ta sakko tace lafiya akan abinda kake ne na kirasu Idan da yuyuwar aje Asibiti ayi checking naka to Idan kuma Malamai za'abaza naji
Ya Na'eem ne yace Mama lafiya bamu gane ba, Abban Deen ma yamana waya akan muzo, akwai matsala da sai gobe zamuzo ko jibi amma jin kince yanzu dole muka tawo.
Zama tai ta zayyanomasa komai, da yadda yakarb'i komai nasa yabawa Alhaji Sani da komai da komai. Harzuk'a sukai suna waye shi?, Wallahi saisun k'ulle shu, yazo zai had'a rigima kome?
Wallahi duk wanda yayiwa masa wani abu babuni babu shi, Kuma yaje nayafewa duniya shi, wanda baigoyan baya na aurawa Saleema wanda nakeso ba Allah ya isa ban yafemasa ba. Ke Kuma Idan kikasa 'yata ta bijiremun kije abakin auren ki tunda hauka nake gara nafara ta kanku.
Kuma yanzu basai anjima ko gobe ba, ku koma inda kuka fito, kubarmun gida na.
Dama badaku na rayu ba, nikad'ai aka haifan Kuma ni kad'ai nasan zafin neman kud'in, ni kad'ai zan mutu, ni kad'ai nayi rayuwata bada kuba dan na barku so what badaku nazo ba.
Yana gama magana ya sakai ya fice. Kuka Maman tasaka tace wacce irin masifa ce wannan?, kuje Allah yasan nufin ku yana tare daku a ko'ina, Saleema Idan haka shine mafi alkhairi agareta Allah yabata ikon cin jarabawar Allah yayi muku albarka.
Ameen su kace, suma idonsu taf da kwalla, suna tausaya Mahaifiyar su da tilon qanwar su, sallama sukai mata kan zasuje gidan su Deen su kwana tunda Abba ya kashe magana ba su da bakin cewa komai
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now