21

52 1 0
                                    


Da gudu Deen yayi saurin zubewa a k'asa ta fad'a kan jikin sa ba tareda k'asa ta tab'ata ba, abin tausayi kuka yasaka yana tab'a jikinta yana Yaya Saleema kitashi kiga nine Deen, hannunta yakama yana d'agawa amma ba alamar zata tashi.
Hawaye ne ya wanke masa fuska wannan wacce irin masifa ce?, Yaya Saleema tashi ga only fa yazo, oya wake up plx is me ur choice, jijjiga ta yake amma ina Saleema bata numfashi ma bare ma tasan yana magana.
Abban tane yazo ya fusgeta daga jikin sa yace kai Mara kirki kazo hargida zaka tarwatsa rayuwar yata, Wallahi baka isaba idanma aikoka akai Wallahi 'yata tafi k'arfin ka.
Deen a tsaye yake yakasa komai Illa hawaye dayake fidda wa, ganin Saleema yashe ya k'asa mahaifinnata ma yakasa d'aukan wani action akanta
Sagir ne yace Abba kamata yayi akaita asibiti ko a saka mata ruwa a fuska. Tom da sauri ya tashi ya d'akko goran ruwa a hannu ya d'iba zai shafamata da sauri Deen yasaka k'afa ya tankwab'e hannun sa yace kaiwaye zaka taba mun mata kul d'inka.
Yana gama fad'a ya tsiyayi ruwan ya shafamata ko motsi batayi ba, kanta ya d'ago ya had'a da nasa yace Saleema waimeye haka?, Ki tashi game is over mana, kada kisaka hankalina ya tashi, bai k'arasa ba yaji wani mari a fuskarsa Sagir ne yayi masa shima yana tashi saidayabashi mari uku manya masu zafi kana ya d'aga hannunsa ya nuna shi da yatsa yace ubanka sani bai isa ya maren ba, barekai d'an shayeshayen kawai, abin takaici da wannna bak'in hannun naka daya dafe wajan shan taba dashi wai kake k'ok'arin tab'a mun my choice kayi kuskure
Abba uba nane dakaga ya daken laifi namasa amma kai waye, banza mara hankali masu asirin banza, fau yaji mari a kunnansa dama gashi jini yagama qyankemasa kayansa da fuskar sa, dmmmm yafaraji sannu Kuma daga ganin har jin ya d'auke, layi yafara yana tangad'i zai fad'i daidai nan Sultan ya shigo saboda yaji hayaniya kuma ga motar Deen da Sagir yagani
Ban kad'a labulan yayi Yana shiga Deen yana fad'uwa, qara yasaki yace Abba meye haka, kashe shi kakeson kayi?, wani irin rashin imanine wannan, ancemaka Abba bayajin zafin abinda kakeyi, tabbas yazama dole asamu mafita, Wallahi bazata sab'uba
Aure kam Deen kamar yasamu baijira cewar uban ba, ya sunkuci Deen yasaka a mota yazo d'aukar key daya fad'i lokacin da zai d'auki Deen, nan yaga Saleema akwance, a hankali ya k'araso yace Abba da hankalin ka kuwa?, yarka ta cikinka kakema haka, Lallai Sagir ne yace kai sultan mara kunya ninafi k'arfin kamun tsageranci, ubanka shine yace zaibani Saleema bani nace ba, aure kam kamar an d'aura
Zaikara magana sultan Abba yafara dukansa yanacimasa mutunci a haka yana dukan nasa ya d'auki Saleema a hannun wadda batasan inda kanta yake ba, yatafi sakata a mota
Mama ganin fitowar Sultan da Saleema a hannu itama da gudu ta tawo tace me zanga ni?, jinin data ganine a jikinta yasata kara fasa kuka tace nashiga uku mene yafaru wani abu yasameta?
Sultan kasa magana yai, sai ma tada mota dayafara yi, nan Abba yace kada ka had'amun 'ya da wannan yaron mutuwar sa tafi a awajena, Ka cire mun 'ya kaji, ko kallo bai isheshi ba, illama key da yayiwa motar mama kam gaban motar ta bud'e ta shiga basu saurari maganar sa ba, suka fice sai Greenfield Medical Hospital
Yana hanya yayiwa Abban Deen waya akan yazo yana Asibiti, kafin suje ma shi yaje da Yayun Deen d'in dakuma Yayun Saleema da Abban yahana su zama a gidan
Karb'ar su akayi, taimakon gaggawa akafara basu, iyayen babu mai Iya magana matan su kuka suka saka, mazan kuma kowa sai safa da marwa suke har yanzu basuji takamaiman me yasame suba tunda Sultan yak'i fadar komai
Doctor Feedoh ce tafito da lab court a kafadarta tana share zufa, da sauri suka tashi kowa yafara Doctor yayah?
They ar all fyn fa kada ku damu, namijin babu matsala anmasa treating ko'ina saijiran farka warsa, macen kuma.....
Macen Kuma me?, yayi sanadiyyar kashe mun 'ya ne?, Abba ne dayake shigowa shida Sani yake tambayar menene?
  Kowa kallonsa yayi, azuciye Mama tace Alhaji kaga Wallahi akan 'yata zan iya kaika k'ara Ka takuran 'ya, menene haka idan ka kashe ta kaji dad'i, nagaji nagaji da abinda kake mun, kad'auki Sani kafifita akaina da yaranka
Wallahi kara bani da kanka, kafita idona na rufe, Doctor meyasa meta fad'i anan dukkan mu, masoyan tane
Abba sakin bakin yayi yana kallon ta, kasa magana yayi Alhaji Sani kuwa tsuru tsuru yayi, azuciyar sa yace tabbas sai yakai Alhaji Raheem wajan Malam yashigarmasa hanci da yawa.
Wato gaskiya Saleema da matsala, tana cikin wani hali, dan yanzu haka aman jini ma take zuciyar ta batada kwari, bayan haka tanada matsala a zuciyar tuntana yarinya kunsan haka?
Mama Ido ta bud'e Sultan kam kansa ya dafe yace Innalillahi Abba kajawomana matsala, tabbas Doctor tanadashi don itakadaice ba'ayi sunan taba, muna Egypt wajan gyara zaman zuciyar ta.
   "Tayi wajan 1 year ma batada lafiya, daga nan kuma batak'ara wata rashin lafiya ba, amma munsan da haka saidai mantuwa irinta d'an Adam badan kin fad'a ba Wallahi namanta."
"Good kunsan da haka kuke barinta da tunani da matsala haka, kunsan da haka kuka bari zuciyarta take k'ok'arin juyawa wani b'ari da ba'aso, tabbas addu'a kad'ai itace mafita, saikuma Idan anmata abinda take so."

   Tabbas rashin kwanciyar hankali shine yaja gaba wajan ciwonta, kuma abaya can 9 to 10 months nan ma tashiga damuwa to wannan damuwar itace tayimata yawa hartajamata jirkicewar zuciya
Salati suka fara, ada suna tausayin Deen amma jin abinda yasami Saleema sai cutar ta, ta shafe tasa, nan akafara sallalami, Abba kam ko ajikin sa, illama cewa da yayi Ita tajawowa kanta aure ba fashi nan da kwana 3 ma iyanzu tana d'akin mijin ta
Jakar dake hannun Alhaji Sani Ita ya karb'a yabawa Sultan yace dan ubanka ungo kaje karabawa jama'a ta, kaima ka d'iba karaba, Na'eem Abbas kuma Ku kwasa ku raba.
Yana gama fad'a ya sakai ya wuce
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now