20

67 1 0
                                    


    Deen shi baisan abinda ake ba, shiryawa yake cikin dakakkiyar shaddarsa getzna maroon colour ga kansa yasha gyara, turare anfesa yayi 10 colour, saboda za'a wajan Saleema.
   Su Shehu dasu Mom harsu Aunty Ummi da suka zo, dariya suke masa, wani barin kuma suna tausaya masa akan yadda ya d'auki son duniya ya azawa Saleema, Abba kansa hawaye ya goge, ganin yana d'okin zuwa, yaman ta kashe din Abban ta da yayi masa, haka yayi shiri yace bara ya zauna sai 5 tayi zaije.
    Saleema kukanta tagama babu mai rarrashi tunda itama mama tanacan takaici da rashin bacci yasata kanta ciwo, so batasan budurin da ake ba.
Sultan ne yashigo yaga tanayin kayan snacks, yace a'a Hajiya Saleema hala Deen ne zaizo ake masa beta haka?, bata juyowa bare ta saurareshi, illama kara gyara zama da tayi, kan kujera dake gaban sink d'in tana wanke plates data b'ata.
    K'arasa wa yayi kusa da ita, yace marowaciya dan kada naci shine kike wani b'ata fuska?, hawaye yaga tanayi batace dai komai ba, hannunta yakama yace Yaya Saleema mene haka?, kada kisaka damuwa komai yasamu bawa da sanin ubangiji, Allah yafimu sanin abinda ya b'oye akan wannan al'amari.
   Addu'a Ita kad'aice mafita, wa kikewa wannan?, Sagir wanda Abba zai ban, shine zaizo Abba yace namasa abin motsa baki, gashi Deen yace zaizo ya zanyi?.
Iska ya furzar yace to kigayawa Deen kada yazo mana, kinsan akwai matsala Idan yazo yaganki da shi, shima da matsala yaganki da Deen zai Iya gayawa Abba, ya kenan?
Harara ta wulla masa, tace bakada lafiya, haka kawai saina cewa Sugar kada yazo, ai mafita zamu nemawa kanmu, amma maganar kada yazo bata tashi ba.
Yaya Saleema bawai banson yazo ba, kada yazo Kuma abu yazama da matsala, kinji abinda wai yaje yayi agidan su?, nan ya gayamata komai harda abinda Abba yace akan bazai bawa b'arawo d'an B'arawo yarsa ba, kinga kuwa da matsala Idan ya ganshi tunda yace ko wajena kada yazo yamasa geji da gidan sa.
Salati tafara tace haka akayi, Wallahi bansani ba, nashiga uku, kuka tafara kanta kuwa yace salamu alaikum ciwo, dama yanayi amma akan maganar data mata zuwan bazata saitaji komai ma ya tsaya mata.
Addu'a tafara azuciyar ta, Allah cikin Ikon sa, Kuma saitaji dama dama, a daddafe itada Sultan suka gama ayyukan, sannan taje sit room ta gyara ta jera su duka ta hausama tai wanka ko powder batasaka ba, haka ta fito ta zauna a parlour.
Bata jima da zama ba, Abba ya shigo yace Saleema saiki tashi ga Sagir can yazo maza wuce kije, cikin sanyin jiki ta tashi, shima bayanta Abban yabi sai dayaga ta shiga parlour'n sannan ya juya.
Da sallama tashiga itama dan tasan martabarta ne, kallo d'aya taimasa ta kauda kanta, a kujera dake can nesa da shi, ta zauna.
D'agowa yayi, yana duban fuskarta akayi sa'a itama ta d'ago, ya ilah ai wannan yarinyar daya had'u da itane a green park, yaso yamata magana saiyaga ina tafi k'arfin sa baran dayaji ance takusan graduation akan low, gata da motar da tafi tasa shiyasa amma yana sonta.
Tashi yayi tsam yaje kusa da ita yace Saleema Sannu koh?, kinshigo ba magana bakisan nizaki aura ba?,Abban ki ya bani ke,saboda haka kamar matata kike a yanzu.
Yana magana ita hancinta ta toshe badan komai ba, saidon warin da d'oyi da bakinsa ya keyi, hannunsa ya mik'a ya rikemata hannu wanda saboda shaye shaye ya fadar, a hankali yakai hannun bakinsa yabashi sumba guda.
Da sauri ta fizge hannun ta, ta mike tsaye tace kai shashasha mara tunani da ilimin addini, ance maka ni shashace dazakawani riken hannu, Kallon k'asa da sama take masa k'arshe yawu ta zubar saboda kyakyami.
Zuciyarsa ce ta baci, aikam mari yabata yace ke dallah sadakar yalla mai bakin jini, tambayi uban ki kyauta yaban ke, badan inaso ba. Stupid kawai.
Aure kuma nan da kwana 5 kinzama tawa, saiki had'i yi zuciya ki mutu ko.
Duk maganar nan da yake yab'amata kaf cikin kunnan Deen wanda zuwan sa kenan yajiyo maganar daga sama, a fusace ya shiga yace kai Waye?, da zaka gayawa Yaya Saleema wannan maganar, aure Kuma Wallahi bazaka aureta ba.
Shashasha yana magana idonsa kan fuskar Sagir, dariya ya saki, yace Deen masoyinta ai magana a k'are, Wallahi ko a yau naso auran Saleema Abban ta saiya bani, kuma kai baka isa komai ba.
Get out from here, Sagir ne fad'a, yana wani muzurai, hannun sa yakai ya rik'o hannun Saleema, ahaf baikarasa kama hannun ba, Deen yabashi mari nan ya fad'a ya kaure, kowa na k'ok'arin nuna shi wani ne afagen fad'an.
Abban Saleema ne ya shigo dayaji hayaniya, tsawa ya musu, waih idansa na haduwa dana Deen nan ya kankance yafara zuba ruwan masifa, yanayi kamar bazai dena ba.
Sagir kam cewa yayi, dama Abba kasan tanada wani kace nazo mu sasanta?, da rawar murya yace k'arya ne ko da akwai ni kai nake so, katin bikin ku ma anbugo, saboda kai Wallahi nakara ganin k'afarka a gidan nan saina wulakanta ka, shege masu asirin tsiya nan yayita masa masifa abin tausayi Ita Saleema kuka tasaka.
Hak'uri tafara bawa Abban ta, akan yadena zagin Deen, shi mutumin kirki ne. Harara ya watsamata yace ke fita idona na rufe zataqara wata magana, hannu ya d'aga zai wanka mata mari, da sauri Deen ya tare Marin ya sauka a fuskar sa, guda uku kwarara masu zafi
Lokacin dayaga ba Saleema yamara ba. Deen ne aisaya saki jiki yafara marinsa mai dalili harda buga kansa da bango, Kuka Saleema keyi tana neman ceton sa amma ina saidaya fasa masa kai, Deen duk abinda Abban yake masa baiji zai iya guduwa ba, illama qara gyara tsayawa da yayi.
Ganin jini nazuba akan Deen da gudu taje ta rungumeshi a jikinta abinda bata tab'a yi ba, amma yau wuya tasaka ta sab'a dokar ubangiji, kuka take bakinta magana d'aya ya kasa furtawa, amma Deen yana jikinta Abban ya had'a su duka yana jibga, Sagir harda taya Abba wajan dukan Deen.
Zafin dukane ko zafin radadin dukan masoyin tane yasaka Saleema zibewa a qasa batare da numfashi a jikin taba
@ut@r h@jiy@ ce

SHI NAKE SOHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin