28

66 2 0
                                    


    Saleema tana cikin gida itama da gudu da fito jin ana gud'a ana had'a sunan ta dana Deen matsayin Ango da amarya, hoo tamanta da jikin ta sai tsalle da murna itada Mamanta rungume juna sukai sunata murna hawayen dad'i ne idon Yaya Na'eem da matarsa lokacin dasukaga irin farin cikin da kanwarsa da Mahaifiyar sa suke ciki.
    Sultan acan kasa had'a ido yayi da Abban sa, saboda yasan tabbas dashi aka had'a yin komai.
   Abban Deen bakinsa har kunne lokacin dayaga yadda Alhaji Sani yake hauka yana kururuwa, shi dariya abin yabashi ma. Tafiya yai wajan Abban Saleema hannu ya mik'amasa, bashi yayi amma fuskar sa a cunkushe ba alamar annuri cikinta. Tabbas saiya rama abinda akayi masa, 'yarsa akama a d'aura mata aure da wani bayan ga wanda yace abawa, Huum Idan kunsan wata bakusan wata ba.
    Baice komai ba a wajan, saima k'ok'ari da yayi ya b'oye bacin ransa, kada agani, Alhaji Sani shida Sagir wanda abokai kewa dariya kasa zaman wajan sukai da b'acin rai suka tafi, da kuma burin d'aukan fansa.
    Walima aka tafi harda Abban Saleema wanda Yaya Abbas ya d'auka, saigani yayi anshiga Meena, jama'a kamar me, gashi nan komai birjik kama daga nakan ci harna sha, saiyanzu yayi tunanin yadda yaga kowa ya hak'ura ashe da tsiyar da sika shirya.
  Wajan yayi kyau Deen sai washe baki ake, sultan kam shida Shehu sai tsiya suke masa wai gawa tak'i rami shida Matar tasa.
    Anyi pictures da video coverage, komai yatafi cikin tsari har lokacin tashi yayi kowa yakama gaban sa.
   Suma iyayen mata sunacan ana shagali harda masu kid'an kwarya, gidan su Saleema kam Sa'adu Bori aka kira, harda Ita wajan rawa, ganomin Auta filin rawa sai cashewa suke abin su.
    Maman Deen kasa zama tai saida tazo wajan Maman Saleema nan ma hawayen dad'i suka zubar, ganin yadda kwanaki suke cikin bak'in ciki amma yau sai godiya.
    Haka akayi yini, wajan 6 akazo d'aukan amarya, ansha kuka Maman ta kamar bazasu rabu ba, D'akin Abban ta aka kaita, tana kuka take neman yafiyar sa da afuwar sa, yanajin tausayin yarsa, amma yakasa tausayamata a fili.
    Da kyar ya furta Allah yabada sa'a yanagama fad'a ya shiga d'akin sa.
   Haka aka d'auketa sai gidanta dake Tarauni inda gidan mijinta masoyinta Deen yake.

  Tare da rakiyar 'yan uwanta da k'awayenta da aminan ta, duk d'okin da take saitaji tadena lokacin da taga kowa nashirin tafiya, basu bari Ango yazo ba, jama'ar suka tafi Anker itada da STYLICH aka bari wajanta, suma dai nasiha da fad'a suke mata, akan zamantakewar aure. Kada taga ada yanamata abubuwa tazata haka ne zai d'ore akwai rayuwa Kuma hak'uri shine gaba, tunda d'an Adam ajizi ne, akwai mantuwa.
    Haka suka zauna saiwajan 8 sannan Ango ya shigo shida abokan sa, a parlour suka zauna, basuyi wani shashancin nan ba, abinda ya kasu shi sukai, sai addu'a da akayi ta d'orewar zaman lafiya.
    Sultan harda shi, lokacin da zasu tafi wajan ta yaje hannunta yakama nasiha yayi mata da kuma fad'an ta kula da kanta dakuma shan magani akan lokaci yana kuka tana kuka suka tafi.
  Su STYLICH saida suma suka tab'a kukan, saboda kowa yasan shaquwar su, gashi aure zai raba, haka ya musu rakiya ya dawo.
  @ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now