15

77 5 0
                                    


Saida taga fitarsa sannan ta juya ta koma gida fuskarta cike da murmushi mai sanyi
Parlour tayi, nan taga Abban ta da Mama a zaune kowa yayi zugum, da sallama ta shiga
"Mama kad'ai ta amsa, amma Abba baice kanzil ba illa mik'ewa ma da yayi ya fice
Da Ido suka bishi daga ita har Maman, ajiyar zuciya Mama ta sauke a hankali ta goge hawayen fuskar ta batare da Saleema ta kula ba
Hannun kujerar da Mama ke zaune ta d'ofana mazaunanta, tace Mama lafiya naga Abba haka?ko laifi akayi masa? kasa magana tai saidata k'ara tambayarta
Huum babu komai, awaje ne aka b'ata masa ,shine yazo yana fushi, baisauke fushin akan kowa ba saimu
Dariya tai tace hooo Abba kenan, muda ko rataya ba'a bamu ba, ammq laifinmu yafi na wanda ya kashe zoman
Bara naje nayi Sallah, batajira cewar taba tayi sama, bayanta tabi da kallo tana tausayamata Idan taji zancen ko ya zatayi?, Allah masani
Sultan lokacin daya fita, baizarce ko'ina ba, sai office yasan Abban Deen baya gida yanzu, Allah ya taimakeshi yana nan, ansanshi so bawani iso da aka masa shiga kawai yayi
Akan kujera yaganshi idonsa na kallon k'ofa amma hankalinsa kwata kwata baya wajan
Saida yaje kusa dashi, yayi sallama sannan yaji, a hankali ya d'ago tareda murmushin k'arfin hali yace Sultan ne zauna mana ka tsaya haka
Zama yayi, saida suka gaisa yace masa Abba akwai damuwa ne?, naganka a haka shima Abban mu yaje gida yana wata magana wadda dagani har Mama kuka tasamu, bangane ba?
Ajiyar zuciya ya sauke, yace kabar komai da maganar harsai jibi dan nayiwa yayun ka magana akan haka since suna nan zuwa jibi, to kaga sai muhak'ura Allah ya kaimu
A'a Abba ai maganar Idan tayi tsawo takai gobe, amma bana barin nan face kagayan komai faru, nan ya zayyanemasa abinda yaji Abban su yana fad'a haryana gobe za'amaida kud'in zancen Deen yajanye bazai baku 'yar saba
Wai yamata miji nan da sati uku zuwa hud'u zaimata aure inda akasan daraja da mutunci da amana, amma ba irin kuba
Dariyar takaici yasaki, yace ikon Allah kaga bar maganar, komai yace mubishi yadda yake so, amma Idan ba haka ba, kowa ma saiyaji kanmu tunda bayin kansa bane
Aure kamar an d'aura Indai ina raye, amma duk abinsa Wallahi ko ba Deen Saleema zata aura ba, bazan barshi yabata wani Sagir ba
Yaro malalaci wanda baisan darajar kowa ba, mashayi d'an daba, b'arawo ai shi halinsa babu na zab'e, na zab'in d'aya dayake shi musulmi ne
Abba duk maganar da kake Wallahi ban fuskanci inda ta dosa ba, a baibai kake gayan maganar, kaina ya kulle kwata kwata
Sultan nace kabari jibi yayunka zasuzo zamu zauna, duk abinda zaiyi ku kyaleshi Idan kun biyemasa ku zakujawa kanku, Saleema ma Idan yamata maganar zan gayamata kada ta damu komai zaizo cikin sauqi
Ba yadda ya iya, dole tasa yayimasa sallama tarema suka fito, kowa ya tafi
Lokacin dayaje gida, motar Abban sa dayajima bai gani ba, ita yagani, amma amcanjamata paint, hakan yasa baikawo komai ba ya kutsa kansa cikin parlour d'in
Wani mutum da wani saurayi yagani a zaune, Abba Kuma yana tsakiyar su abinci suke ci, wanda a abincin saida sukasamu suka zuba masa magani agaban sa, wanda zai k'ara sawa zuciyarsa ta tsani duk wanda ya danganci Alhaji Raheem, da kuma wanda zai kamusu cikas cikin al'amransu
Zama yayi ya gaidasu, amsawa Alhaji Sani yayi, yace kaddai shine Sultan?
Eh shine, ah Lallai ai ya girma, nazata Yaro ne tabarkallah Allah ya raya Ameen yace
Yauwa Sultan haura sama zakaga briefcase d'ina, ba wadda nake fita da ita ba ka d'aukon tana kusa da mirror
Tashi yayi, yana mamakin ina Abba yasan wad'an nan Kuma ya akayi su sunshanshi amma shi baisansu ba?
D'akin ya shiga ya fito da Jakar a hannun sa, ya kamasa kusa da shi
Sultan da Sagir can ku gaisa, wankane shi zanbawa Saleema ya aura, yazone su gaisa to Kuma ta fita, gobe ya dawo munyanke hukunci sati ukun shine ba hud'u ba
Idansa ya juya ya kalleshu , hannu ya mik'amasa yace salamu alaikum
Ina! da sauri sultan ya mik'e yace Abba Waye wannan? Kuma wazakabawa shi, bakasan nema cikin nema haramun ne amusuluncin ba?, bare kai da ilimin ka da k'imarka kad'auki 'yarka mai daraja kabawa mashayi d'an giya Wallahi Indai ina raye Saleema batada miji sai Deen
K'anin tane ni, amma zan Iya bada aurenta, kada kamanta kabada Ita fa, yanzu kuma kace zaka bawa wani, ina katabajin anyi haka?
Abba da hankalin ka, idanka afarke, haba inaa!
Dama akansu d'azu kake haka, shine Sagir d'in hhhhhh lallai kanason kajawa kanka
Abba a fusace ya mik'e yabashi kyakyawan Mari guda biyu, yace kai nizaka tozarta ina magana kana cewa ban Iya ba, kaine uban ni d'an kenan?
Tsabar takaici Sultan ficewar sa yayi, ya barsu anan
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now