24

78 3 2
                                    


   Bayan fitar Maman Deen daga d'akin su Shehu abinci suka zubo masa da kunu mai zafi, a gabansa suka dire, ko kallon abincin baiyi ba ya tashi tsam ya haye gado ya juya musu baya.
    Abincin shehu ya d'auka ya hau gadon, kafadar sa ya  dafa yace Deen kada kayi fushi da abinci, kuma rashin lafiya zaka k'arawa kanka, then Idan baka ci abimci ba ya za'ayi ka sami karfin da zaka kwaci Saleema?
    Yanzu namaka alqawari Idan kaci zanyi wa sultan waya yabaka Saleema ku gaisa anjima kuma nakaika ka ganta koba haka ba?, da sauri ya tashi yana murmushi yace da gaske  zaka kaini wajan ta?, eh mana.
   Dariya yai yafara cin abincin, spoon uku kawai yakai bakin ya dire, a hankali ya waiga yace Shehu kamanta Abban ta yace kada naqara zuwa, kuma a yanzu wannan Sagir d'in ne a wajan ta?
    Deen kenan to ai jarumi zaka zama, kajure komai akan SO kana iya bada ranka ma da lafiyar ka, bare kuma ba duka ba yanka, kajure komai maza cinye  abincin ka shirya kai kwalliya muje.
    Hannu yasaka yafara ci, Shehu kuma yana masa hiran Saleema kafin me sai plate ya cinye, yana gamawa wanka ya shiga, yadi ne kufta brown anmasa aiki irin na hannun nan, yayi kyau tazarce ce, haka yasaka sannan ya d'akko hula da takalmi yasaka turare yafesa, wayar sa ya janyo suka tafi.
    Ko Mom basu gayawa zasu fita ba, haka suka kama hanya sai asibitin batare da fargabar komai ba, suka saka kansu cikin gate en, parking motar su, sukayi a ma'adanar ajiye motoci suka dab'a a k'afa duk da cewa jikin Deen baiyi kwari sosai ba
    Da sallama suka bud'e d'akin da take, sultan ne kusa da Ita, yanamata magana itakuma kuka takeyi dan ga alamar sheshekka nan atare da Ita.
    Jin k'amshin irin na Deen yasaka ta d'agowa, ido biyu sukai, wata sanyayyiyar ajiyar zuciya suka saki lokaci d'aya, a hankali ya k'arasa bakin gadon ya zauna.
  Sultan ne yace Yaya Deen kasan kazama Yaya, ya kake ya kuma karfin jikin ka?, hannu ya mik'a masa suka tafa yace shegen kaya anji wuya kaga yadda ka zabge kunban tausayi lovers hhhhh dariya suka saki shida Shehu.
   Saleema ce tace sultan bakada kirki haka ma zaka ce?, zamu rama. Hhhh saidai ku rame, kinga maganin kima lokaci yayi ungo ballo tablet yayi guda uku, yabata kauda fuska tai tace time baiyi ba, wallahi time yayi kuma saikin sha
   Deen ne ya kalleta yace maganin ne bazaki sha ba?, eh tace dariya yayi yace to da kika gayan tausayin ki zanji nace abarshi?, sultan bata, fuska a turb'une ta karb'a d'aci ne ya gauraye bakin ta haka taringa yatsina fuska har Allah ya isa tayiwa Sultan. Shi dariyar sa yake.
    Bararrajewa sukai suna hira Saleema ciwo saiya tafi, harsun manta a wani tashin hankali da suke ciki, kwatsam saiga Sagir ya shigo baiyi minti biyu da zuwa ba, Abban sa da Abban Saleema sukayi sallama.
   Ina wuta Alhaji Sani yasaka Deen, nan fa yafara masifa meyazo yi?, Abban Saleema kam waya yayiwa police ayi maza azo, ga wani zai kashe masa 'ya
    Deen kasa motsi yayi ma, Shehu ma haka, Sultan ne yace Abba mene haka, kiyayyar har takai haka?, Wallahi babu wanda zai tafi da Deen saidai a tafi dani, Mari Abban yakai masa, daga nan ne police guda biyu suka shigo.
    Deen ya nuna musu, abin tausayi tashi yayi fuskar sa sharkaf da hawaye yabisu a baya, Saleema ganin ya mike itama da sauri tace Deen katsaya dan Allah kada ka bisu zan mutu Idan katafi
Cak ya tsaya, amma yakasa juyowa, ransa Idan yayi dubu ya baci me yayi Abba da zafi haka zaimasa wannan cin mutunci, insha Allah sai Allah ya nunawa Alhaji Sani k'arshen sa.
    Bai juya ba, yayi gaba tareda Shehu da sultan da suka biyo bayan sa, Saleema kiransa amma ina ko waige yaci zuciya.
   Sultan da Shehu sune tun kafin suje station d'in, suka yiwa police din bayanin kosuwaye su da yadda komai yake wa kana, sauran kiris suma suyi kuka, tsayar da motar sukai suka ringa basu hak'uri tunda suma sunsan amintar dake tsakanin Iyalan biyu.
    Gida suka nifa, Sultan kam hak'uri yake basu, amma Deen ko kallon sa baiyi ba, badan yaji haushi ba, a'a tunanin ya halin da masoyiyar sa take ciki take.
   Direct Asibiti ya koma, tashin hankali Saleema aman jini ga idonta dayake rife amma hawaye kamar fanfo aka bud'e, hancin tama kansa zubar jini ya keyi, Abban ta kuka yakeyi yana wasu maganganu amma aikin asiri yasaka yakasa tuna komai Illa ma jin zuciyar sa yake tana tafarfasa akan yayi yayi yai auren nasu ya huta.
    D'akin thearter aka shigar da Ita, badan rai ba'a hannun ka yake ba, danace a Yau Saleema bazata kwana da rai ba
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now