4

238 11 2
                                    


Sultan yana fita gida yai, kansa ya d'auki charge yarasa yadda zaiyi, shima suna son saka shi cikin matsala tunda dukkan su jinin sane bazai Iya ganin d'aya yana cikin matsala ba ya zauna dole saiya shiga damuwa shima
  D'akin sa tafi shower ya sakarwa kansa ya dad'e yana tunanin mafita amma ina yakasa hangowa haryanzu baiga hasken hanyar warware matsalan ba
   Yaya Saleema ko zata mutu bazata iya furta cewa tanason Deen ba, Deen shima yaji yagani da idonsa kunya da nauyi da kuma ganin kamar Saleema tafi k'arfin sa shima bazai iya furta Kalmar SO gareta ba ya za'ayi kenan
   Haka ya fito tareda alwalar sa ya jima yana Addu'a, kafin yatashi yatafi d'akin Yaya Saleema
  Itada Mama yagansu ta d'ora kanta a cinyar Mama. Yauwa Sultan zo narasa gane kan Saleema kwana biyu tazama wata iri, yanzu magana nake mata akan meke damunta amma tak'i, nayi nayi da ita zo kai kozata gaya maka
   Tsugunawa yai, akan rug dake cikin d'akin, hannunta ya kamo yace Mama nima na tambayeta tak'i gayan, amma ni ina tunanin ko exam d'in da tayine taci CO shine take damuwa kada mugani dan naji ance tafito
   Da sauri ta tashi tana murgud'a baki tace Lallai yaro CO yayi hannun riga da Saleema, wuce nan fever ke damuna amma Idan naci CO aina banu
   Ko Mama ta Idan Autarki taci CO aiba kanta, kut wace yar Autar amma kin yanken ina zaune dan kin ganki jikin Mama shine zakici Auta
   Matsama ni tashi daga kanta, wallahi bazan tashi ba, kalle shi wani gardi dashi, kafin me ta ware sun fara hayaniya can kuma Sai hira Mama tashi tai ta barsu taiwa kowa asubah tagari
   Yana sane yace mata haka, danta ware gashi Allah yabashi sa'a damuwa ta tafi, shima mik'ewa yayi Yaya Saleema da alheri zan gudu inason yin karatu kinsan exam next week inajin campus zan koma ma, naga Idan ina nan bazaki barni nayi wani abin kirki ba
  Aikin ki ya ishan ma. Allah bazan saka ba, Plx Ka taimakan ka zauna rashinka wani gib'i ne arayuwa kaji
  Tom, amma Idan naganki cikin damuwa na tambaye ki baki gayan ba, saina tafi
  Naji na yadda, sallama sukai itakuma ta janyo bargo tashiga ciki tafara sana'ar wato tunanin Deen
   1:30 na dare Deen ya farka, wayar sa ya duba yaga time, lallai yayi bacci. Text din da aka turo, ya duba Sultan ne, da sauri ya karanta, baki ya washe yafara copying numbers d'in yana alhamdulillah
  Dialling number yafara, tunani yai to yace mata me?, kuma dare yai, anya zata kulashi kuwa
  "Hello" waye cikin dare haka?, maganarta ita tadawo dashi daga duniyar tunanin daya shiga
  Ajiyar zuciya ya sauke, cikin kasala da fargaba yace Yaya Saleema nine
  Kaiwa?
Deen mana nabugo na gaidaki bansan dare yayi ba, Sai danayi dialling number sannan naga time sorry for disturb
   A kwance take amma tanajin yace Deen, saita mik'e zaune fuskarta ta fad'a d'a da murmushi haryanajin sautin murmushin cikin ransa
  Ok Deen ya gari, kwana biyu lafiya dai? bata nuna komai ba, Illa basarwa data fara
  Wallahi banjin dad'i amma now I'm OK, ya kike Yaya Saleema ya karatu?
  "Karatu fyn, yanaka?"
Haka ake so, accounting kake karanta koh? Itace tamasa tambayar
  "Eh Yaya inason course d'in sosai tun ina Yaro nakeda burin karanta gashi Allah ya cikamun burina
   Koh nikam na tsani aikin bank ko d'aya bai burgeni, dan Yaya Na'eem bayadda zanyi kuma dan kafin nawani girma yayi karatun sa dabazan barshi ba
  Zuciyarsa ce yaji tanason kwacewa Yaya Saleema batason mai aikin Bank, Babbar magana
   Kanajina koh ni ko aure zanyi bazan auri Banker ba"
Tari ne Yakama shi dababu shiri, kenan Yaya Saleema bazata aureshiba koda yaga yamata
  Ina mafita?, babu wata zuciyar tace
  Deen sannu kana mura ne? A'a yazo ne tarin kawai
  Ni kuma Yaya Saleema banason lowyer saboda sharrin su, ga ha'inci da cin zali, ga k'arya ga rashin gaskiyar su, ni koda zanyi aure ban auran lowyer
  Eyee me kace?, lowyer bashida duk abinda ka fad'i yanzu nishinake karanta fa kuma kusan karashe ne yanzu
   Kai Yaya Saleema lowyer, da girman ki, lallai ni zan Iya canja course indai wadda nakeson aura bata so, kodan nafaranta mata
   Kinga bye ni nafara jin tsoran ki ma, yana magana yana dariya ciki ciki yaji dadin hira da Sweetyn sa, ga muryarta mai sanyi
   Deen tsaya kada kayi hanging nata, Kasan me?
  Nidai banji bye asubah tagari  a hankali ya furta I LOVE U.
"Hello Deen tsaya plx, nidai Yaya Saleema a'a kinsan lowyer da sharri, kuma koba halin kaba yanzu zasu koya maka
  Nidai nace wait koh, jin tayi magana seriously yace naji ya akayi?
  Kenan kai bazaka auri lowyer ba, mene aibun su?, haka kawai Yaya Saleema, ban sha'awar lowyer
   Huum, nima kuma natsani banker sosai, bye bacci yazo
Kafin yace wani abu ta datse layin
  Ihu yasaka jiyayi kamar ansakashi cikin aljannah Yaya Saleema nada kirki baizaci tanada sauk'in kai ba, amma wani hanzari ba gudu ba, kenan Idan har yazauna a haka bazata soshi ba
   Lallai mafita yakamata ya nema, yanason aikin Bank amma akan Saleema zai iya komai, zan iya jure komaine Indai har Saleema zatayi farin ciki
   Allah kabata ikon sona, to yazance mata ina sonta komai, kai ba haka ba, shirme yaringa yi har bacci yatafi dashi
  Itama tunanin ta yace bazai auri lowyer ba, to me yake so? batasani ba, tanason karatun ta amma Indai Deem bayaso zata canja, kai canjawa confirm, bara Safiya tayi tunda sunada Doctors da professors a hannu abin bazai zama da wuya ba
  Chancellor da vice nasa surukan sune,  'yayan su suna auran su Yaya Sameer, tsalle tai tace I find d solution, gobe ba jibi ba zanfara fighting akan haka
  Deen , I love u, itama bacci ne yatafi da ita
   Washe gari da Asubah Bayan an Idar da Sallah Deen yasamu Abban sa akan yanason canja course shi ya taimaka masa
  To Deen akan me? naga shi kake so, ko wani abu akayi ?
  Ko d'aya Abba, haka kawai naji hankali na a yanzu yafi karkata dana karanci business kodan na tallafamaka tunda naga suna Broth dukkan su kowa aikin sa yake
  Indai ka yadda ka amince inason ka taimakan acanjan course na koma nasu Sultan
   Babbar magana, tabbas kayi tunani kayi hankali wallahi naso kazama magajina amma kai sainaga kwata kwata bakada ra'ayi akan wani karatu Indai ba accounting ba
  So ni abinda kake so shina ke so, abinda kake muradi shinake muradi farincikinka nake so, a kullum amma alhamdulillah Addu'a ta tafad'a zanyi fighting akan hakan yau insha Allah Allah yayi maka albarka
   Wata matsanannciyar murna ta kama shi, baizaci Abba zai amince ba, Addu'a da fatan gamawa lafiya yafara jerowa uban
    Nayi Nasara sauran nasarar samun zuciyar Yaya Saleema itama Allah kaban sa'a
  Ko dayake yau su Yaya Fauzy zasu zo mayi magana akan subani tips na yadda zan Iya tunkarar Yaya Saleema da maganar so
   Baccin dayake komawa bayan ketowar alfijr anan yayi mafarki wai gashi da Saleema suna soyayya tanagayamasa tana son sa itama, kuma har anfara shirin aure amma kashi saiga duhu ya mamaye wajan daga can yajoyo muryar Abban ta yana cewa bazai bashi Saleema ba, tunda Abban sa maha'incine maci amana yaje can ya nemo mata amma ba Saleema ba
    Hannun su yana rik'e da juna suna kuka akan kada arabasu, dukkan su basa ganin juna duhun nan ya mamaye wajan
   Fit yaji an kwace hannunta daga hannun sa, kafin yayi wani yunk'urin komai ya farka agigece
  Salati yafara jikinsa sharkaf da gumi, ga hannun sa alamar shatin hannu
   Ido ya zare yafara duba hannun yes shatin hannu ne, amma ya haka, baikawo mugun nufi cikin mafarkin saba Addu'a yai ya mik'e
   Saleema cikin sharinta nazuwa school ta fito, tana rik'e da waya a hannunta tana karanta text na good morning da Deen ya turo murmushi tai kamar agabansa take sunba takaiwa wayar saitin inda yasaka ur lovely broth Deen
   Dukkan su yan gidan sun hallara ana zaune ana hira, wajan Abba tai tace Abba dama inason gayamaka magana amma dan Allah kataimakan kuma kada katambayen dalili duk da nasan ba'ayin abu batare da Dalili ba, kuma kamun kyakyawan fahimta
   Saleema kome kike so insha Allah zan miki fad'i naji, Yauwa Abba inaso Ka taimakan kasaka baki acanja course dan Allah Kasan yadda nake son wannan karatun nawa amma ikon Allah wallahi jiya da shekaran jiya bana gane komai akai, hasalima bacci da kasala itane take kamani canjawar shizaifimun alkhairi
   Saleema naji na gamsu, kuma nasan Indai bada wani abu ba bazaki canja ba, naso tambayar dalili amma tunda kince nayi hak'uri da tambayar nayi shiru Allah yayi miki Albarka tashi dama fita zanyi yanzu muje makaran tar
  Murna tafara, itama Sultan kallon tai yayi yace Yaya Saleema yanzu kin tashi a barrister komai zaki koma kuma oho
   Zab'armun broth, Huum kefa zakiyi karatun ki ni banda zab'i, amma kinga Deen shi yafison matar sa ta karanci English kawai
  Amma Idan kinada ra'ayi a kansa kiyi shi, good shi zanyi tnz peck tamasa a kumatu taje taiwa Mama suka kama hanya
   Yana zaune yana tunani yajiyo wayar sa, Deen akan layi
"hello guy y kake ya jiki jiki kuma?
Fyn aboki nafa canja course yanzu haka muna school ana fighting akan inason course naku
  Kai Deen itama yaya Saleema yanzu suka tafi da abba anan yagayamasa yanda sukayi
  Wow Yaya Saleema taci gari, yanzu zata zama big lady, nima nacanja
   To kai in tambaya ka mana, ya haka kaika canja Ita tacanja kunyi waya ne jiya?
  Eh nan yaga yamasa yadda sukayi, hhhhhh Allah ya kyauta Idan tayi wari maji amma kun burgeni
  Bangane ba, eh bazaka gane ba, ma had'u anjima
  Bye guy Manya, Kaga banson gulma, sai mun had'u
    Alhamdulillah angama komai, kuma yasamu abinka da hanya, itama haka lallai abin Manya, basu had'u ba
   Yau za'aje majalisa, murna d'oki zasuga juna, tunda Deen baije gidan su ba
   Yan gidan su Deen mata sunzo, sai rawar kai yake akan yabasu labari yadda za'ayi
   Suna zama a parlour ya biyosu, nan ya zauna yafara fada musu komai harakawo yanzu
   Yaya Ummi ce takece da Dariya harda riqe ciki, tana kallon sa tace kabari Shehu yazo yabaka ko Halifan malam kasan jiya da daddare suka sauka kuma sunce zasu zo
  Ihu yasa kai Lallai maza sun dawo, munyi missing juna, kai kace banda matsala bara namusu waya akan suzo muje can tare
   Yaya Fatee ce tace, amma Deen kana ganin zata yadda ba amatsayin k'ani kuma d'an uwa ta d'auke kaba?
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now