19

139 6 2
                                    


   Suna fita suka had'u da shi a compound yana waya, wajansa sukai a tsugunne sukace Abba muntafi Allah yabamu alkhairi Allah kusa yasa haka shine mafi alkhairi damu baki d'aya.
Kamar bazai amsaba. sai kawai yace Ameen Idan takai zuciya dan ni Yanzu kun maida wawa mara hankali komai naku sai Alhaji Raheem.
Hak'uri dai suka bashi, kowanne ya mik'e sika Shiga motar sukaja sai gidan su Deen.
Parking sukai, a nan sukaga su shehu kowanne da waya a kunnan sa sallama sukai musu suka shiga ciki, Zaid suka gani a kujera da sauri ya mik'e yace Yaya Abbas sannunku da zuwa da daddare kuke tafiya haka?, Wallahi kuwa bak'in turai ya garin saukar Yaushe?
D'azu na sauka, naso zuwa nagaida Abba ma, kuma sai gashi.
Huum aimu muna cikin tashin hankali, ni narasa da wanne zanji da maganar bawa wannan azzalumin dukiyar sa koda maganar auren Saleema wanda yake shirin yi nanda rana ita Yau.
Zaid tagumi yayi, yace tun tashina ban tab'a ganin koda harara Abban ku yayiwa Abban mu ba, amma yau nan ya labarta yadda abin yake, hawaye sukaita zubarwa dukkan su, tunda wannan masifa ce sabuwa.
A nan suka raba dare suna jajanta yadda abin yake, suna kuma kokawa kannen su, tunda suma shaidane akan k'aunar da suke wa junan su.

Deen tare da Abban sa ya kwana, Mom kuma a parlour ta zauna, addu'a take Allah yakawo mafita, amma wannan murd'addan al'amari dame yayi kama?.
Saleema tunda ta kwanta bata farka ba, saida akayi kiran Sallah daidai nan shima Sultan ya tashi, kallonsa yakai gareta, shi ya manta da wani abinda ya faru, sai daya ga yadda tai zuru zuru, ga idonta yayi ja, itama kusan haka ta manta da komai sai data tuna, nan fa tashin hankali yazo mata kuka tasaka mai k'arfin gaske tana birgima bakinta yakasa furta komai, Illa kuka datake yi a haka mama tazo ta same ta.
Mikar da ita tayi, tana lallashi da ban baki, da nunamata komai fa dan hak'uri ne, Idan batayi shiru ta kwantar da hankalin ta ba, ya za'ayi susan abinyi, lallab'ata tai, ta tashi tai alwala tace kiyi addu'a kikai kara wajan ubangiji yanajinki yana ganinki shine zai miki maganin komai.

Kuka k'unci babu abinda zasu sawakke akan abinda Allah ya tsara, sihiri gaskiya ne, wanda yace k'arya ne tabbas ya halaka, tunda ya kama Annabin Allah bare kuma mu yan Adam masu laifi da shirka.

Tabbas Abban ki, komai yayi bada saninsa bane, Idan bakiyi addu'a ba, ya za'ayi Allah ya dubemu ya yayemana halin da muke ciki, kanta take shafawa tana gayamata magana mai dad'i.
Uwa uwace, ko yaya dai Saleema taji sauqin wani abin, haka ta zauna akan dadduma tanakai kukanta wajan mai kowa mai komai.
Safiya nayi, Idan kaga Deen kace yayi cuta yanda yayi wani iri, yai laushi abinci kansa abaki Abban sa yabashi amma ko 3 spoons baiyi ba, yace bayaci, shima nasiha aka masa da nuna masa suma yaran gidan baso suke ba, kawai shine yake ki d'ansa, da haka suka shawo kansa shima yayi shiru.
Yayun Saleema da Abba ya gansu tambaya yayi yayah?, nan suka koramasa bayani akan yace ko kallon banza sukaiwa Sani bai yafeba, ajiyar zuciya ya sauke yace *Wato shi bakin iyaye define, ko da ba akan gaskiyar su, suke ba, Idan suka maka lallai saiya ka maka, saboda haka kubi umarnin sa, addu'a dai zamu cigaba da yi itace mafita*
To kowa ya shiga tsuu, Alhaji Sani dai duniya sabuwa, dan kuwa komai da Abban Saleema ya karb'a wajan Abban Deen yabawa Alhaji Sani ajiyar su, Kuma yace sufara shiri, lefe kuma shi ya d'auki nauyin yinsa, KATIN d'aurin Aure shima harsun tsara bugawa ya rage komai dai kud'i kawai yake bayarwa yace ayi abinda yakama ta.
Deen wanka kawai yayi, bayan amai da yayi, dan saida aka d'aura masa drip 2 leda sannan fa ya farfad'o har yake shirin zuwa wajan Saleema.
Sunyi waya sosai sukasha hira kamar ba abinda yake faruwa, saida suka tuno kuma sukaga lallai fa rabuwa zasuyi, nan akafa ambaliya da hawaye, dole ya zama Namiji yafara rarrashunta amma ina takasa den kuka.
Ba yadda yayimata saidaya furta cewa zaizo anjima wajan magreeb sannan tai shiru, tace tana jiran sa.
Abba ne ya shigo gidan fuskarsa d'aure yace ina Saleema?, sama ta nunamasa da hannu, bai saurari Sultan dayake masa magana ba, Illa hawa da yayi yace ke da sauri ta d'ago jikinta na rawa tace Abba.
Kallon tai yai, kana ya furzar da iska yace ki shirya da magreeb zakiyi bak'o, ki tabbata kinmasa abinci da abin sha, kiyi kwalliya wanda zai aure ki ne.
Baijira cewar taba, ya fice kifa kanta tai, tafara rera kuka tana yarfe hannu, abin tausayi
*To ya ,za'ayi kenan, ku saurari Autar Hajiya dai*
@ut@r h@jiy@ ce

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now