30

63 1 0
                                    


     Assalamu alaikum Yaya Saleema harkin shirya baki tsaya nazo nayi rubbing back naki ba na shirya ki, banson kina wahala bayan bakida lafiya?

  Murmushi tayi tace aikafita lokacin dana ka shirya ni, hancin ta yaja yace jiki kamar da gaske, nasan sauri ma kikayi kika shirya dan kada nazo na ganki?, nidai ba haka bane.

   To naji. Zama yayi kusa da Ita kan gadon yace wash nagaji zirga zirga da gaisawa da jama'a sun wahalar miki da miji. To ya za'ayi dole ne ai, dole koh? huum kinsan gajiyar danayi kuwa?, Allah da ace munyi events bansan colour na gajiyar da zanyi ba.

   Kinga tashi muyi Sallah mu godewa Jalla wa Azza da yabamu lkon mallakar junan mu cikin hanya mai sauqi. A hankali ta tashi hijab ta d'akko dadduma yasaka musu Sallah sukai raka'a biyu ba da addu'a ta nuna godiya ga sarki Allah.
   Sun jima kafin suka shafa addu'ar, kowanne kuma saiya kasa tashi daga kan sallayar, illa Idan ta d'ago ido taga yana kallon ta, yanzu ma kallon sa tayi suna ido hud'u ya bushe da dariya Yaya Saleema mene na kunyar mijin kine fa ki kallon ko da akwai maganar da zamuyi?, da hannu tace masa a'a. Ok taso mu kwanta dare yayi au namanta bakisha maganin ki ba, ke kuma kika k'i tunamin.
   Yatsine fuska tai, tace nifa naji sauqi dan Allah abar maganin nan, haba dai ai dole kisha, janyo wata Leda yayi maganin ya b'allo guda uku saina ruwa, tsam ya mik'e ya bud'e k'aramin  freigh d'in dake d'akin ya d'akko ruwa gora guda.
  Balle bakin yayi, yaje kusa da ita oya bud'e bakin, datse bakin tayi, ta juyar da fuskar ta, dariya yasaki mara sauti yace Yaya Saleema Allah rigimar ki yawa gareta, banda abinki ai maganin zaimiki amfani kuma jikin ki fa ba sauk'i kina daurewa ne kawai, saboda haka tunkafin muyi fad'a juyo ki amsa?

    Kwab'e fuska tai tace dama kaida sultan bakuda kirki, haka a Asibiti kuka sani dole saidana shanye magani kwalba d'aya, nadena kulasa ai.
   Inye kice Nima nakusa shiga layi, tsaya tsam ya rungumeta ya bud'e bakin ya zuba mata na ruwan da kokawa ta shanye, dariya tabashi sosai yadda yaga tanayi saikace wata Autar Hajiya mai kukan magani.
    D'ayan ya d'ebo bud'e kinga a hankali zan samiki bazai tab'a harshen kiba. Nidai nak'i ba yadda ta Iya haka ta bud'e bakin ruwa yafara zuba mata sannan ya saka maganin, tas ta shanye ba d'aci, dariya tai tace kaji ba d'aci?, eh ai sultan mugunta yamiki shiyasa
   Da haka suka tarkata saikan bed. Juyo da Ita yayi yace Yaya Saleema yanzu mune a unguwa d'aya gida d'aya d'aki d'aya akan gado d'aya, meyafi wanann dad'i?
  A hankali ta furta babu, Allah muna kara godiya a gareka, daka bamu damar mallakar junan mu, kuma abin dad'i k'ark'ashin inuwar aure, Sunnar ma'aiki SWA.

   Aure ni'ima ga wanda yakeda rabon yi, ada saidai mu kalli juna ba damar kusantar juna, amma yanzu abu uku zamu samu, nafarko zamuji dad'i, nabiyu duk abinda mukayi lada ne, na uku muncika addinin mu,   tabbas da mutane zasu gane wallahi babu abinda yakai aure ni'ima ku kasance lokacin da kuke so, kuma ga d'umbin lada da Allah zai baku, babban abu darajar ka da k'imarka zata k'aru wajan jama'a, Allah kasa muda ce.

   Kasan makoshi ta furta Ameen, saboda yadda yawani matseta ajikin sa, yana gugar k'afar ta Sai take jin wani iri. Fuskar ta ya tallafo a hankali yabata light kiss a baki, dariya yayi ganin yadda ta runtse idon ta.
   My choice " na'am, daban sameki ba bansan yadda zanyi ba, godiya ta wajan ubangiji mai yawa ce, zanyi ta godewa Allah har sai randa numfashi na ya d'auke.
   Yana gama fadar haka, yasaka bakinsa cikin nata, yanamata wani irin abu, a hankali yake sarrafa ta, yana mata wasu abubuwa, daga k'arshe dai rigar jikin ta ya fincike.
    Gaba d'aya jikin sa wani iri yake, Allah sarki Saleema Ita ba magana jikin lakwas yayi, takasa juya jikin tama saiyadda Yaro Deen yayi da Ita.

   Safiya nayi na had'a kayana sai gidan Saleema da Deen naga me akeyi duk da nasan komai yayi fine lokacin natafi celebrating murnar Haihuwar Deedoh.
    Gate nayi nocking a hankali mai gadi yazo ya bud'en, fuska ta a rufe nashiga gidan.
  "A zuciyata ina tafiya ina cewa Allah kasa da rabon zanga wani d'an hints wanda zanbawa makaranta labari ahaka na k'arasa cikin main parlour din"
   "Oga na gani zaune yayi crossing leg nasa da remote a hannun sa yana canja chenal
   " Rab'ewa nai dan kada ya jini nafara aikina wato d'aukowa masu karatu labari.
   Aljazeera yake kallo amma minti d'aya biyu zanga ya kalli k'ofar bedroom d'in su, jira yake yaga ta ina Yaya Saleema zata b'ullo amma shi har wajan 20 minutes hakan ne yasaka ya mike ya shige d'akin sa.
   Spare key ya d'akko, a hankali ya bud'e, cak ya tsaya yanq tasbihi ga ubangijin da yayi kayan k'awa da burgewa na sha'awa jikin Yaya Saleema.
   Towel ne babba ya rife jikin ta ruf amma Ikon Allah komai yake gani, shiru yayi tunda yaga bataji shigowar sa ba.
  "Ta jikin mirror yake kallon ta, yadda yaga kamar kara mata kyau akayi, shidai bashida bakin magana sai tasbihi ga Sarki mai kowa da komai
    Saleema tana tsaye tunani takeyi, ikon Allah Deen shine jiya ya maidata cikakkiyar budurwa, Yaro dashi amma ya birkitamata tunani.
   Yasata kukan akan wani abu can, shine zai wani lallab'ata.
  " lips d'anta ta shafa, dariya tai harda rife fuska tuno wani abu da tayi, d'aga idon da zatayi sai ganin sa tai jikin mirror ya zubamata ido.
   Suna had'a ido tai saurin kauda fuskarta, a hankali ya tako harta karaso kusa da ita.
   Hannayenta ya kama, Huum Yaya Saleema shine jiya kika dameni da kuka, nasan duk makota sunji abinda mukayi.
  "Wayyo Abba ashe dama Deen mugu ne, sultan abokinka zai kasheni, wayyo lips d'ina kayi hak'uri, dariya ya kwashe da ita yana lakutar hancin ta.
    Sai kwarwa kike mun kamar zan cire wani abu, jikinta yake tab'awa yana muga ina nacire ake mun kuka haka?
   Hannun sa ta doke, dariya takeyi itama, kwace jikin ta tai, takoma bayan k'ofa tana leqensa.
   Ta baya ya rungumota yana shinshinar k'amshin ta, bakinsa saitin kunannta magana yake mata a hankali.
  "Yaya Saleema shine kika k'i na shirya ki koh?, bayan ninayi aikin da yakamata ace nizan miki komai, amma shine kika sakan kuka kedai na fita koh?.
   Dariya tai kanta a sunkuye batace komai ba.
   Gashinta yafara shafawa a hankali, jin hannunsa zaikai wani waje daban yasaka ta rik'e hannun, juyo da ita yayi kallon ido sukai da sauri ta d'auke kanta.
   "Lips d'inta ya shafa yace Yaya Saleema I Love u, inason Komai naki, Allah yabamu yara nagari"
   Itama fuskarsa ta shafa tace me too my choice bansan adadin son danake maka ba.

Da gaske kike kina sona?, kai ta d'aga, alhamdulillah Yaya Saleema na sona.
   A tsayen da suke yafara mata wasu abubuwa, da sauri tace nidai kabari plx, a kasalance yace plx Yaya Saleema ones kawai, kinga ke mata tace kuma ke Allah ya hallatamun ki bari sau daya kawai.
    Shiru tai, jiyafa Ita tasan yadda taji a jikin ta, har yanzu wajan namata ciwo, ga breast nata suma ba sauqi ciwo.

   Kanta ya d'ago yace is OK one love a barshi kawai, zo muje kiyi break, Mom ta aikomana dashi?.
   Lafewa tai a jikin sa, hannun sa dake jikin ta, take shafawa bakinta ya kasa furta komai, a hankali ya janyeta daga jikin sa yace oya shirya kinji sweety na.
   A'a tace. Zama yayi bakin gado tace to mene na b'atan rai yammata?, ba Kaine ba, ni kuma to menayi?
  Shiru taqara illa lips nata datakai wani gun a ajikinsa. Abin nema yasamu ba shiri Deen ya ware yafara mayar mata da martanin abinda take masa, Daga nan Kuma Sai Oga aiki.
    Idona na rife, a haka suka gama kashe wa juna jiki, kana Kuma suka shiga toilet tare danyin wanka.
    Itace tafara fitowa sai shi daga baya, kan stool ta zauna hand dyer ta janyo, ko jonata bataiba yazo amsa yayi ya soka sannan yafara busar mata da gashi.
   Suna yi a hakan suna dariya, shi a dole shizai gyaramata kai, Ita Kuma zafi takeji Idan yana tab'awa, amma bata nuna ba.
   "Wayar sa ya janyo, selfei yafara kashe musu, sosai sukai kyau a hakan da suke haka suka d'auki kayan su.
    Material ya d'akko mata red sa silver ga d'in kin shima ya fita, sarka silver ta saka, zata d'aura d'ankwali yace tabari yanason ganin gashin ta a haka. haka suka shirya sannan yakama hannunta sai kan dining.
  Saleema yar gata duk ke d'aya, wannan abincin?

Kai ta kad'a, murmushi yayi yace to bismillah, da kansa yafara bata roman kaza ne sai hanta da tumatir dataji, ga tea maizafi da kayan k'amshi, haka sukaci sukai nak.
    Maganin ta ya ballo da qyar tasha, daga nan sai kan kujera, bacci zatayi yace ta tsaya tad'anyi mintu uku saita kwanta.
   Zamansu keda wuya, saime? Abba suka gani da Alhaji Sani a tsaye yayan cikin Saleema saida suka kad'a,
   Da sauri ta mik'e, Abba sannu da zuwa, wani kallo ya jefeta da shi, kana yace bazama nazo ba, d'akko mayafin ki, kizo mu tafi aure ne banso kuma dole ka saketa a yanzu ba sai anjima ba
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now