16

89 4 0
                                    


   Alhaji Sani ne ya mik'e yace haba Alhaji ba girman kabane, amma da takaici ace d'an cikinka shine mai gayamaka magana haka saikace sa'ansa
Tabbas Alhaji Raheem ya cuceka yarabaka da yaran ka, macen kwaya d'aya itama zairabaka da ita, wannan abin duba wane
Wallahi Hakane amma zan yiwa tufkar hanci, Shege kawai, aure kamar and'aura Sagir kafara shiri daga Yanzu ga Yaro mai hankali, amma shi kullum yana gida, ba kunyar cewa ni surukinsane magana yake saki, zanyi maganin Ku
Alhaji Raheem hak'uri zakayi, tabbas cuta dai ancuceka, yara dukiya duk an kwance
Kwafa yayi, kana ya janyo wannan jaka, bud'ewa yayi, takaddune yafito dasu ciki
Dubawa yayi, saigani nai ya d'akko wasu guda uku, ya mik'amasa yace, ungo wannan takardune na filayena a Rijiyar zaki, nabaka d'aya, d'aya Kuma Sagir ya d'auka saiyafara gini, duk da zanbashi gida wanda zasu zauna kafin nasan maiyakamata yafara yi, dayar Kuma saika ajiye mun
A banka na amsosu sauran na wajan sa, wata ya qara fitowa da ita, yace wannan kuma takardar Estate dana gina ce, a Shagari Qrts, nabaka ajiya ka adanamim su, amanarka na duba nabaka ajiyar
Ba komai Allah yatayamu rik'o, Allah kuma yasaka da alkhairi mungode sosai, haka yayita basu details akan dukiyar sa hatta account numbers nasa da pin d'insa saidaya gayawa Alhaji Sani
Aikin sihiri kenan, nan fa suka mik'e suna dariya tajin dad'i, suka fice harda tafawa
Duk abinda akayi akan Idon sultan ne, yana ganin sin fita da gudu yaje wajan Mama
Mama kina ina?, lokacin tana tare da Saleema suna tad'in su
A gigice ya shigo, Mama wai ina hankalin Abba yaje, yana wasu abubuwa kamar mara kai
Saleema ce ta mik'e Marinsa tai, tace Sultan Kaine bakada hankali, Yaushe kayi girman da zakagayawa Abba haka?
Mama laifin kine, shashasha kawai, tana gama fad'a ta fice tana tsaki
Wajan ya Shafa yace Mama Yaya Saleema batasan komai akan abinda Abba yake shirin aikatawa akan taba?, data sani dabatace haka ba
Mama takardun Abba na fili yabawa wani ajiya nan ya zayyanomata yadda akayi
Salati tafara, tace aure da wannan yaron dana gani, Lallai Wallahi bai isaba, takaddu kuwa fake ne
Bangane fake ba?, eh shekaran jiya naji yana magana akan zaikarb'i komai nasa a wajan Abban Deen yabawa shi wannan mutumin, da kuma takardunsa na gida
Banyi qasa a gwiwa ba, nayiwa Abban Deen magana bashiri yazo, takaddun kaf ya karb'a jiya yakamun su yace na ajiye masa wannan Idan sunan wata basusan wata ba
Kaga kuwa duk abinda yabayar da wanda zai bayar zasu zama not original, na wajan Alhaji Raheem d'in ma haka yace zaimusu kada yazo unexpected yace yabashi
Ikon Allah wannan mutum waye shi?
Wannan bak'in mugu kenan, nan ta labartamasa tin had'uwar su da yadda yaso Alhaji Raheem ya amince masa kawo Yanzu
Tab aiki Ja, Yanzu ya za'ayi kenan nibanason Saleema taji
Banko k'ofar akayi, Abba ne ya shigo kwalar rigar Sultana yakama
Mari ya ringa wanka masa yana nizaka wulak'anta?, ba'ahaifin d'an da zaimun haka ba
Nan yafara ball dashi, Mama ce tashiga tsakiya tace Wallahi bazaka dokarmun d'a ba, baka isaba
Nan yace matsa, bazan matsa ba, kadakeni nima, akan angayamaka gaskiya Kuma Wallahi bazaka aurawa yata wancen gantalallen yaron ba
Haihuwar tsakiyar rana, rainon wiwi da sholisho, tashin taba da 'yarmo, girman Whisky da wine
Eh Lallai da alama kinasha shiyasa kika sani ko d'an naki yana sha
To wayasani abu a duhu, amma Wallahi bazaka bawa 'yata wancen d'an daban ba
HAJIYA ni kike cewa haka?, to zan nuna miki true colour d'ina, zaki tantance waye keda iko akan Saleema ni ko ke?
Auren ma nadawo dashi sati d'aya ki nunan ikon naki, kinji kaikuma kanemi mai yimaka registration amma bani ba, y'a tawa ce
Shikuma wanccen uban Deen yau zankaimasa kud'in sa ba sai gobe ba, tunda naga shine ubanku yanzu
Daga yau na haramtawa *IMAM DEEN* zuwa gida na, aure kamar an d'aura
Allah yabaka ikon yi. Ameen Idan da gaske kike
Juyawar da zaiyi saiganin Saleema yai a bakin k'ofa idonta fal hawaye tasaka hannunta abaki tana gudun kada kukan ya fito
Hawaye shatata yake kamar anbud'e fanfo, kallon mahaifin ta take, Ido bud'3. Wajan ta yayi hannunta yakama, kwacewa tai tace Abba mainaji kana fad'a sokake kace zaka rabani da abinda zuciya ta ke muradi?
Deen rayuwa ta ne, Wallahi Idan babu shi nasan saura ce a rayuwa ta, laifin mai mukayi da harza'amana horan da mutawa ce kad'ai zata mana shi
Abba ai Deen ko yankata yayi, Indai da alkunya bakayi fad'a akaina ba, Indai har d'ane a gidan Abban babba
Tana magana tana rufe bakinta tana girgiza kanta, hannunsa takama tace Abba kasan SO kuwa?
Wallahi babu cutar datafi ta so had'ari.SO BABBAR CUTA ne, Idan har bakayi sa'a akansa ba
SO makahone bayaganin laifin masoyin sa, koda laifin yafi girman Dala da Goran Dutse bare Deen bashida aibun da za'ahanashi 'ya
Abba Indai kanason farin cikina kada karabani da Wanda zuciyata tafara SO
Kada kamun abinda zaiakawo naqasu a rayuwa ta, kada kamun abinda zakadawo kana danasanin, kada kamun abinda duniya zata zageka, kada kamun abinda rayuwa ta zata tagayyara
Rabani da Deen tamkar d'aukewar numfashi nane, Abba kayiwa tilon yarka mace adalci kayi mata abinda zaisakata farin ciki
Kuka take Wanda Idan mai sauraro yaji dole ya tausaya mata amma ina ko silin tausayi Abba baiji ba
Mamanta kuka take itama, fincike hannun sa yai, yace Idan nacanja ra'ayina kice yau ubana zai dawo duniya
Yana gama fad'a, yasakai ya fice
Daga wajan ko one minute bata k'araba ta sulale a k'asa sai jin k'arar faduwar ta Mama taji tunda Sultan yafita tun kafin shigowar Saleema
Ihu mama tasaka tace Saleema mene haka?, katashi Wallahi bazaki auri Sagir ba, Deen shine mijin ki
Shiru mak'atau, Saleema ba motsi ihu tafasa, Sultan da gudu ya shigo, shima layin yabi yana tab'ata ta tashi amma d'uf
Ruwa ya d'ebo, yafara zuba mata, saida ya kusan k'arar da gorar ruwan sannan sukaji tayi ajiyar zuciya idonta rife takasa bud'e shi
Hawaye ne yake fita a idaniyar ta, hannunta ma takasa d'agaashi, Sultan da Mama sune suka d'auketa suka azata a bed
@ut@r h@jiy@ ce

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now